Yadda Zirin Gaza zai kasance bayan kammala yaƙi

Yadda hayaƙi ya turnuƙe bayan wani hari da Isra'ila ta kai a Zirin Gaza a ranar 26 ga watan Disamba 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda hayaƙi ya turnuƙe bayan wani hari da Isra'ila ta kai a Zirin Gaza a ranar 26 ga watan Disamba 2023

Isra'ila na shan matsi daga ƙawayenta kan cewa ya kamata ta fitar da tsarin yadda Zirin Gaza zai kasance da zarar aka kammala yaƙin da ake yi da Hamas.

Yanzu haka ministan tsaro na Isra'ila, Yoav Gallant ya zayyana matsayar da ƙasarsa ta cimma kan yadda za a tafiyar da lamurran yankin bayan yaƙi - wanda ta yi wa take "kwana guda bayan kammala yaƙi."

Mene ne wannan shiri ya ƙunsa? Mene ne martanin ƙasashen Larabawa da kuma na al'ummar Isra'ila? Kuma wane ƙalubale za a iya cin karo da shi wajen aiwatar da shirin?

Mene ne tsarin da zai fara aiki a Gaza da zarar an kammala yaƙi?

Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya fayyace tsarin da za a yi aiki da shi a Gaza bayan kammala yaƙi

Isra'ila ta bayar da shawarwari guda huɗu da za a yi aiki da su a Gaza bayan kammala yaƙi:

  • Ƙwace ikon Gaza daga hannun Hamas - Isra'ila ce za ta ja ragamar ɗaukacin harkokin tsaro a Gaza, ciki har da tantance duk wasu kaya da za a shigar ko fitar daga yankin, sai dai fararen hula ƴan Isra'ila ba za su zauna a yankin ba.
  • Dakarun ƙasa da ƙasa, bisa jagorancin Amurka, waɗanda suka haɗa da wasu daga ƙasashen yankin da kuma na Turai za su ja ragamar sake gina yankin na Gaza.
  • Ƙasar Masar mai maƙwaftaka, wadda ta cikinta ne ake da mashiga ɗaya tilo daga yankin za ta taka muhimmiyar rawa bayan kammala yaƙin, sai dai ba a fayyace irin rawar da za ta taka ba.
  • Za a taƙaita ikon da Falasɗinawa ke da shi a yankin, "bisa sharaɗin cewa babu wata barazana ga ƙasar Isra'ila."

Lokacin da take sharhi kan sabon tsarin da za a aiwatar a Gaza, babbar wakiliyar BBC, Lyse Doucet ta ce "babu alamar cewa hukumar mulkin Falasɗinawa da ke Ramallah a Gaɓar Yamma ko kuma Hamas za su taka wata rawa a Zirin Gaza bayan yaƙin.

Tsarin da Isra'ilar ta fitar ya kuma zayyana yadda sojojin ƙasar za su aiwatar da mataki na gaba na yaƙin da suke yi a Gaza.

Ministan tsaron ƙasar ya ce dakarun Isra'ila za su mayar da hankali wurin kai hare-hare a wurare na musamman a arewacin Zirin Gaza, inda lamarin zai haɗa da kai samame, da rushe hanyoyin ƙarƙashin ƙasa, da kuma kai hare-hare ta sama da ta ƙasa.

A kudancin Gaza kuma dakaruin Isra'ila za su ci gaba da nemowa da kama shugabannin Hamas da kuma ceto ƴan Isra'ila da ake garkuwa da su, kamar yadda ministan ya faɗa.

Martanin al'ummar Isra'ila kan tsarin?

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Har yanzu firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu bai ce uffan ba game da tsarin wanda Mista Gallant ya bayyana
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tsarin wanda Mista Gallant ya zayyana ba a riga an amince da shi ba a hukumance kuma ba a riga an miƙa shi ga sauran ministocin gwamnatin Isra'ila ba.

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu bai ce uffan ba tukuna game da tsarin.

A baya ya bayyana cewa ana buƙatar sojojin Isra'ila su kawar da Hamas tukuna kafin fara duk wasu shirye-shirye na yadda Gaza za ta kasance bayan kammala yaƙi.

Ba a tattauna sosai kan tsarin ba a zaman majalisar zartarwar Isra'ila da ya gabata ba, inda aka bayyana cewa tsaron ya tashi baram-baram, bayan da wasu ministoci suka nuna adawa da wasu sunaye da aka gabatar waɗanda aka ce za a bincike su game da harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.

Wasu masu ra'ayin riƙau na gwamnatin Netanyahu sun ce ya kamata a buƙaci Falasɗinawa su yi ƙaura daga yankin Gaza, sannan a sake gina matsugunan Falasɗinawa a yankin - shawarar da wasu ƙasashen yankin da kuma wasu ƙawayen Isra'ila suka yi watsi da ita tare da cewa ta yi tsanani kuma ba za a iya aiwatar da ita ba.

Ƙarin labaran da za ku so ku karanta:

Wane martani hukumar mulkin Falasɗinawa ta mayar?

Firaministan mulkin yankin Falasɗinawa, Mohammad Shtayyeh

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Firaministan hukumar mulkin yankin Falasɗinawa Mohammad Shtayyeh na neman a samu mafita ta siyasa ga dukkanin Falsdinawa

A wata tattaunawa da jaridar Financial Times, Firaministan mulkin yankin Falasɗinawa Mohammad Shtayyeh ya ce duk wata yarjejeniya da za a cimma dole ne ta ƙunshi "mafita ta siyasa ga dukkan Falasɗinawa", ba Gaza kawai ba.

Shtayyeh ya ce "(Isra'ila) na son ta ware Gaza daga Gaɓar Yamma a siyasance."

"Ba na tunanin cewa Isra'ila za ta fice daga Gaza da wuri. Ina tunanin cewa Isra'ila za ta kafa tata hukumar mulkin (a Gaza) wadda za ta yi aiki ƙarƙashin sojojin mamaye na Isra'ila. Saboda haka babu cikakken bayani kan shirin tafiyar da Gaza bayan kammala yaƙi."

Masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a ƙasar Jordan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a ƙasar Jordan

Masar, wadda aka ambace ta a cikin shirin ita ma har yanzu ba ta ce komai ba kan lamarin.

A ƙasar Jordan mai maƙwaftaka, dubban masu zanga-zanga sun hau kan tituna domin bayyana goyon baya ga al'ummar Gaza.

Jagoran jam'iyyar Labour, mai adawa a Birtaniya, Sir Keir Starmer ya ce bai kamata Isra'ila ta zama wadda za ta tantance makomar Gaza ba, sannan ya yi kira da a martaba batun kafa ƙasashe biyu a yankin.

Ya shaida wa BBC cewa: "Ba za mu yarda da mamayen Isra'ila ba, ba za mu amince da tarwatsa mutane waɗanda ba za su iya komawa gida ba, domin a cikin wata huɗu da suka gabata an tarwatsa mutum miliyan biyu, wannan abu ne da ba za a amince da shi ba,: ya ƙara da cewa: "Ba na tunanin Isra'ila ce ya kamata ta tantance abin da zai faru da yankin Gaza bayan yaƙi. Ya kamata a samu matsaya tsakanin ƙasashen duniya kan lamarin, in ba haka ba, abin ba zai yi nasara ba."

Ya bayar da shawara cewa ya kamata a tuntuɓi shugabannin Jirdan da Qatar da sauran ƙasashen Larabawa wajen neman mafita game da Gaza bayan kammala yaƙi.

Amurka ta sha nuna sha'awar samar da ƙasashe biyu a yankin, inda ta bayar da shawara a samar da wata sabuwar hukumar Falasɗinawa da za ta tafiyar da lamurran yankin.

Yanzu za a sanya ido domin ganin martanin da Amurka za ta mayar, yayin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ke kai ziyara a Isra'ila, inda ake sa ran za a tattauna makomar Gaza bayan yaƙi.

Waɗanne ƙalubale za a fuskanta?

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken

Da wuya ƙasashen Larabawa su yi na'am da shirin na Isra'ila.

A ranar Juma'a shugaban ƙungiyar Hezbollah ta mabiya Shi'a a Lebanon, Hassan Nasrallah ya yi gargaɗin cewa: "Idan Isra'ila ta kammala da Gaza, yaƙi na gaba zai ɓarke ne a kudancin Lebanon."

To sai dai hatta samun daidaiton ra'ayi tsakanin Isra'ila da babbar ƙawarta Amurka kan wannan shiri zai zama mai wahala.

Wakiliyar BBC a Gabas ta tsakiya, Yolande Knell ta ce rashin kasancewar fararen hula ƴan Isra'ila a yankin Gaza zai zamo abu mai muhimmanci, lamari ne wanda zai janyo ce-ce-ku-ce a cikin gwamnatin Isra'ila, "domin Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi a gwamnatin Isra'ila na ta kira wajen ganin an samar da matsugunan Falasɗinawa a Gaza."

Wani ƙalubalen kuma, in ji Knell shi ne "ra'ayin babbar ƙawar Isra'ila, domin kuwa Amurka na so ne wata sabuwar hukumar tafiyar da yankin Falasɗinawa ta jagorancin yankin na Gaza."

To amma duk kafin a fara ƙaddamar da shirin tafiyar da Gaza bayan kammala yaƙi, ya zama tilas a kawo ƙarshen yaƙin wanda ya kashe Falasɗinawa sama da 22,000 da kuma ƴan Isra'ila 1,100 a ranar 7 ga watan Okotoba.