Ana fama da bala'in rashin magunguna a Gaza, in ji likita

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Adnan El-Bursh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
- Aiko rahoto daga, Rafah, Gaza
"Halin da ake ciki a Zirin Gaza da kuma musamman a Rafah yana haddasa mace-mace."
Dr Marwan al-Hams shi ne daraktan Asibitin Shahidi Mohammed Yusuf al-Najjar da ke Rafah, mai gadon kwanciya 63 amma yana kula da majinyata 145.
Hakan na iya kasancewa fiye da ninki biyu na abin da asibitin zai iya ɗauka, to amma fa birnin Rafah wanda ke kan iyaka da Masar a yanzu ya zama mazauni ga Falasɗinawa miliyan ɗaya da yaƙi ya raba da gidajensu, ƙari a kan al'ummar da ke rayuwa a can su 300,000 tun kafin fara yaƙi.
"Rashin magani ya zama bala'i kuma ga shi babu masaka tsinke a asibitoci saboda yawan marasa lafiya," kamar yadda Dr al-Hams ya faɗa wa BBC, wanda kuma ya ci gaba da zayyana cutukan da ke bazuwa a wuraren da mutane ke fakewa da makarantu da gidajen da ke cike da mutane.
Dr al-Hams ya ce asibitoci a faɗin Zirin Gaza na karɓar marasa lafiya da ke fama da matsananciyar gudawa da galabaita da kuma zazzaɓi.
Waɗannan duka larurori ne da ke yaɗuwa ta hanyar ruwan sha da abinci da kuma hulɗa da sauran mutane.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce aƙalla ba akasara ba, gidan wanka ɗaya ne mutum 700 ke amfani da shi, yayin da mutum 150 ke amfani da banɗaki ɗaya a Gaza, bayan shafe wata biyu ana yaƙi.

Asibiti ɗaya ne kawai yake aiki ne a arewacin, yayin da goma ke ci gaba da aiki a kudu, cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mutane na ƙoƙarin kuɓuta daga luguden bama-baman Isra'ila, kusan abu ne da ba zai yiwu ba ka iya samun sabulu da garin sabulu.
"Cutukan fata kuma suna bazuwa. Yawan mutanen da ke zuwa asibitoci da cibiyoyin lafiya da cutar ƙarambau sun kai 4,593 - wannan ƙididdiga an samo ta ne kimanin kwana biyar a baya," a cewar Dr al-Hams.
Ƙyanda ma ta ɓulla inda aka samu mutum biyar sun kamu da cutar zuwa yanzu.
Dr al-Hams ya ce ƙyanda wata babbar cuta ce da ta ɓulla kuma sun samu mutum 115 da suka kamu a faɗin Zirin Gaza.
Sun kuma samu ɗumbin mutanen da ke fama da cutukan fata da ƙuraje. Ya ce jimillar mutum 35,305 da ke fama da irin waɗannan larurori aka gabatar a asibitocin da ke faɗin Gaza ranar 8 ga watan Disamba.
"Mun kuma samu mutum 17,511 da suka zo asibitoci da sha-ka-tafi da ƙwayoyin cutuka irinsu kwarkwata," a cewarsa. "Ba ma iya samun magungunan da za mu ba su."
Bugu da ƙari, mutum 19,350 sun kamu da cutuka masu alaƙa da ƙarzuwa, waɗanda kan bazu daga wannan mutum zuwa wancan a wuraren da ake da cunkoson jama'a.
Hukumomin lafiya a Gaza sun samu rahoton mutum 350 da suka kamu da cutar amai da gudawa, wadda kan shafi 'ya'yan hanji ta hanyar haraswa da bayan gida mai haɗe da jini da majina, da ciwon ciki. Cuta ce mai saurin bazuwa.
"Wannan duka ƙari ne a kan ruɗewar ciki," a cewar Dr al-Hams. "Saboda ƙarancin abinci, mutane sun koma cin busassshiyar gurasa. Sai su wanke ta, su ɗumama ta a kan wuta kafin su ci."

Asalin hoton, Reuters
Haka kuma mutane na kamuwa da cutar shawara, a lokacin da fatar jiki da ƙwayar idon mutum ta kaɗa ta koma ruɗan ɗorawa, abin da ake alaƙantawa da ciwon hanta da kumburin hanta.
Dr al-Hams ya ce an samu rahoton mutum 4,146 da ke da larurorin ciwon hanta.
Yana kira a buɗe dukkan rijiyoyin ƙarƙashin ƙasa ta yadda mutanen da yaƙi ya ɗaiɗaita za su iya samun tsaftataccen ruwa.
"Sannan a rufe ruwan tafki da na fadamu masu yaɗa cuta ta hanyar ciwon sauro da sauran ƙwari," Dakta al-Hams ya ƙra da cewa.
Ya ce yana tabbacin cewa duk kayayyakin asibitin da aka shigar Zirin Gaza, an yi amfani da su gaba ɗaya.











