Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yaƙin Gaza zai iya ɗaukar ƙarin watanni ana gwabzawa'
- Marubuci, Daga Henri Astier
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Yaƙin Isra'ila da mayaƙan Hamas, zai ci gaba har tsawon watanni, a cewar shugaban rundunar sojojin Isra'ila.
"Babu mafita ta nan take," kamar yadda Herzi Halevi ya faɗa wa manema labarai.
A ranar Litinin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi gargaɗin cewa yaƙin ba zai ƙare a nan kusa ba.
Isra'ila ta ce ta kai hari kan cibiyoyin Hamas sama da 100 a ranar Talata. Ta kuma ce tana ƙara faɗaɗa farmaki ta ƙasa a tsakiyar Gaza.
Ma'aikatar lafiyar Gaza da ke ƙarƙashin ikon Hamas ta ce an kashe Falasɗinawa 20, 915 a cikin makonni sama da 11 da aka shafe ana gwabza faɗa.
An fara yaƙin ne tun ranar 7 ga watan Oktoba bayan wani ƙazamin shiryayyen hari da Hamas ta kai kan garuruwan Isra'ila.
An ɗaiɗaita mutane kusan miliyan 1.9 tun bayan da Isra'ila ta fara luguden wuta, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Juliette Touma, wata mai magana da yawun hukumar kula da Flasɗinawa ƴan gudun hijira ta MDD (Unwra) ta faɗa wa BBC cewa: "Muna ganin tashin hankali na yunwa da ƙarancin abinci a wasu wurare, yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa, ana kuma ci gaba da ɗaiɗaita mutane sannan sansanoni sun cika makil."
A makon jiya, sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya yi kira ga Isra'ila ta sassauta hare-haren da take kai wa, don rage barazana da fararen hula ke ciki.
A ranar Talata, shugaban sojojin Isra'ila Herzi Halevi, ya faɗa wani taron manema labarai cewa yaƙin zai "ci gaba da gudana har na tsawon watanni" don tabbatar da cewa "mun yi tattalin nasarorin mu na tsawon lokaci".
"Babu gaggawa idan aka zo batun tarwasa ƙungiyar ƴan ta'adda, sai dai idan ta nuna turjiya da kuma jajircewa a faɗa," in ji shi.
Dakarun tsaron Isra'ila sun ce sun kai hare-hare ta sama kan wurare 100 a birnin Jabaliya da ke arewacin Gaza zuwa Khan Yunis da kuma Rafah a kudanci.
Akwai rahotanni da ke cewa sun kaddamar da farmaki ta ƙasa a sansanonin ƴan gudun hijira da ke tsakiyar Gaza bayan umartar mazauna wurin su fice.
An sake yanke layukan waya da na intanet a faɗin Zirin Gaza.
An kashe wasu mutum 1,200, yawanci fararen hula a hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba. An kuma yi garkuwa da kusan 240 zuwa cikin Gaza. Isra'ila ta ce har yanzu ana ci gaba da rike da 132.
A ranar Litinin mista Netanyahu ya faɗa majalisar ƙasar cewa: "Ba za mu iya sakin dukkan waɗanda ake garkuwa da su ba ba tare da amfani da sojoji ba....ba za mu dakatar da faɗa ba."
Kafofin yaɗa labarun Isra'ila da na Larabawa sun ce Masar ta gabatar da buƙatar tsagaita wuta.
A cewar rahotanni, shirin tsagaita wutar zai ba da damar sakin ƴan Isra'ila da ake garkuwa da su da kuma sakin fusunoni Falasɗinawa da ake rike da su a gidajen yarin Isra'ila, da kuma dakatar da farmakin Isra'ila gaba-ɗaya.
Tsagaita wuta da aka cimma a baya wanda Qatar ta shiga tsakani ya kai ga sakin gomman Isra'ilawa daga Gaza da kuma sakin fursunoni Falasɗinawa.
Zuwa yanzu, Isra'ila da Hamas sun bijirewa kiraye-kirayen tsagaita wuta.
A gefe guda, Ministan tsare-tsaren ayyukan sojin Isra'ila Ron Dermer na birnin Washington don tattaunawa da mista Blinken da kuma Babban Mashawarci Kan Harkar Tsaro Jake Sullivan.
Tattaunawar za ta mayar da hankali kan "batutuwa da suka shafi yaƙin Gaza da kuma sakin waɗanda Hamas ke garkuwa da su", a cewar mai magana da yawun Kwamitin Tsaro na Ƙasa Adrienne Watson.