Bayern Munich ta kammala ɗaukar Palhinha daga Fulham

Bayern Munich ta kammala ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Fulham Joao Palhinha kan kudi fan miliyan 42.3, kan kwantaragin shekara huɗu zuwa watan Yunin 2028.

Dan kasar Portugal ɗin mai shekara 28 ya koma ƙungiyar Bundesliga shekara ɗaya bayan yarjejeniyar da suka cimma shekara ɗaya baya ta ruguje.

"Wannan na daya daga cikin rana mafi farinciki a a rayuwata," kamar yadda ɗan wasan ya faɗa a shafin ƙungiyar.

"Yanzu zan bugawa ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin duniya kwallo. Wani fatan da nake da shi ne tun da daɗewa, ina Alfahari da hakan."

Palhinha ya koma Fulham ne daga Sporting Lisbon a 2022 kan kuɗi fan miliyan 17.

Ya lashe kyautar ɗan wasan ƙungiyar da ya fi ƙoƙari a kakarsa ta farko a Fulham.

Dan wasan ya buga wasa 79 a cikin kaka biyu da ya yi a kungiyar ta yammacin Landan, tare da cin kwallo takwas.

Palhinha ya bi bayan Michael Olise tsohon ɗan wasan Crystal Palace na gefe.

Dan wasan Ingila Eric Dier shi ma ya koma ƙungiyar a matsayin ɗan wasanta bayan wasan da ya buga mata a matsayin aro daga Tottenham a bara.

Bayer Levekusen ta kawo ƙarshen shekara 11 da Bayern Munich ta kwashe tana lashe gasar Bundesliga.