Ibrahimovich zai bar AC Milan a karshen kakar bana

Zlatan Ibrahimovich

Asalin hoton, Getty Images

Zlatan Ibrahimovic zai bar AC Milan da zarar kungiyar ta kammala wasan karshe a Serie A na bana da za ta kara da Hellas Verona ranar Lahadi.

Milan za ta dan dakar da wasan domin karrama dan wasan mai shekara 41 da taya shi murna kan taka leda da ya yi a kungiyar.

Ibrahimovic ya koma Milan a 2019 kuma ya taimaka wa kungiyar ta lashe Serie A a kakar da ta wuce.

Wasa hudu aka fara karawa da shi a bana da cin kwallo daya, bayan da ya sha fama da jinya, hakan ya sa kungiyar tace ba za ta tsawaita zamansa ba idan kwantiraginsa ya kare a karshen watan Yuni.

Tsohon dan wasan Malmo da Ajax da Inter da Barcelona da Paris St-Germain da LA Galaxy da kuma Manchester United, ya lashe Serie A tare da AC Milan a karon farko da ya buga mata tamaula a 2011.