Ferguson ya lashe kyautar gwarzon mai taka leda daga tsakiya a Serie A

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan tawagar Scotland, Lewis Ferguson ya lashe kyautar Bulgarelli a matakin ɗan wasan tsakiya da ba kamarsa a Serie A ta bana.
Kyaftin din Bologna na taka rawar gani a kokarin da kungiyar ke yi na neman gurbin Champions League a badi, daga baya ya ji rauni a cikin watan Afirilu.
Kafin ya ci karo da koma bayan, Ferguson ya ci kwallo shida ya bayar da hudu aka zura a raga a wasa 31 a bana a babbar gasar tamaula ta Italiya.
Wadanda suk lashe kyautar a baya sun hada da Daniele De Rossi da Nicolo Barella da kuma Sandro Tonali.
Mai shekara 24, ba zai buga wa kasarsa gasar cin kofin nahiyar Turai ba da za a yi a Jamus Euro 2024 daga Yuni zuwa Yuli, bayan da aka yi masa tiyata.







