Yara na cikin mutum 12 da suka mutu a kwale-kwalen da ya kife a mashigin Birtaniya

Asalin hoton, AFP
Wata mata mai juna biyu da yara da dama na cikin mutane 12 da suka mutu bayan da wani kwale-kwalen da ke dauke da bakin haure da dama ya kife a mashigin Birtaniya.
Galibin wadanda suka mutu mata ne da kuma yara da dama, in ji ministan harkokin cikin gida Faransa Gérald Darmanin, ya kuma kara da cewa wasu mutane biyu sun bace.
Jami'an tsaron gabar ruwan Faransa sun ce an ceto mutane fiye da 50 a gabar kogin Gris-Nez da ke kusa da garin Boulogne-sur-Mer. An ce biyun na cikin mawuyacin hali.
Mista Darmanin ya ce jirgin ya yi lodi fiye da kima, kuma mutane kasa da takwas ne ke dauke da rigar da ke bayar kariyar nutsewa a cikin tekun.
Wannan Iftila'ai dai shi ne aka fi samun asarar rayuka mafi muni a mashigin a bana
Magajin garin Boulogne-sur-Mer, Frédéric Cuvillier, ya shaida wa BBC cewa wata mace juna biyu ta mutu.
Wata majiya ta ce mai yiwuwa akwai hannun wani mai safarar mutane daga kasar Syria
Mai gabatar da kara na birnin, Guirec Le Bras, ya ce wadanda suka mutu ‘yan asalin Eritrea ne, amma jami’ai “ba su da cikakkun bayanai da za su ba mu damar bayyana ainihin yan kasashen”.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kafin faruwar alamarin na ranar Talata, mutane 30 sun mutu yayin da suke tsallaka mashigin a cikin 2024 - adadi mafi girma a kowace shekara tun 2021, lokacin da aka sami rahoton mutuwar mutane 45, a cewar Hukumar Kula da kaura ta Majalisar Dinkin Duniya.
Mista Darmanin ya ce hukumomin Faransa sun hana kashi 60 cikin 100 na kananan jiragen ruwa tashi. Sai dai masu fasa-kwaurin mutane na cushe mutane kusan 70 a cikin jirgin ruwa guda wanda a da ke daukar mutane 30 zuwa 40 - abin da ya kai ga kifewar jirgin.
Ya yi kira ga Birtaniya da EU da su amince da "yarjejeniya kan ƙaura" don hana ƙananan jiragen ruwa.
Sakatariyar harkokin cikin gida ta Burtaniya Yvette Cooper ta bayyana lamarin a matsayin "mai ban tsoro da kuma ban tausayi."
Adadin mutanen da ke tsallakawa ta mashigin cikin kananan jiragen ruwa ya karu, inda sama da mutane 135,000 suka shigo Burtaniya ta wannan hanyar tun daga shekarar 2018.
Sama da mutane 21,000 ne suka tsallaka mashigin a bana
Tuni dai jam'iyyar Labour da gwamnatin da ta gabata suka sha alwashin shawo kan matsalar.
Firayim Ministan Burtaniya Keir Starmer ya soke shirin gwamnatin Jam'iyyar Conservative na tura wasu masu neman mafaka zuwa Rwanda, wanda aka fara sanar da shi a shekara ta 2022 amma bai fara aiki ba.
Sir Keir ya lashi takobin daukar tsauraran matakai don " tarwatsa " kungiyoyin masu safarar mutane .
Sai dai masu suka sun ce kamata ya yi gwamnati ta kara yin kokarin samar da hanyoyi masu aminci ga masu neman mafaka.













