Halin da matasa masu son zuwa Turai ke faɗawa a tsibirin Lampedusa

..

Dubban ƴan ci-rani ne suka isa gaɓar tsibirin Lampedusa a makon da ya gabata, inda ake tsare ƴan ci-ranin a ƙasar Italiya.

BBC ta ziyarci inda ake tsare da 'yan ci-ranin, wanda aka fi sani da 'Hotspot'.

Sansanin na Lampedusa cike yake da jama'a a kowace rana.

A ƴan watannin baya-baya nan, mutanen da ake tsarewa a cibiyar sun zarta adadin da ya kamata a tsare a cibiyar.

Ƙungiyar agaji ta Red Cross a Italiya ta ƙiyasta cewa mutum 10,000 ne suka isa cibiyar a makon da ya gabata, da yawa daga cikinsu sun isa tsibirin ne cikin ƙananan jiragen ruwa daga Tunisiya.

Mazauna tsibirin na bai wa ƴan ci-ranin tallafin abinci da ruwan sha da tufafi, yayin da suke fama da ƙarancin wurin kwana a cibiyar da aka gina don daukar mutum 400.

Yayin da tawagar BBC ta nufi cibiyar ta ci karo ga gungun matasa na raye-raye yayin da suke sauraron waƙoƙin yammacin Afirka da na Larabci.

BBC ta yi yunƙurin tattaunawa da ƴan ci-ranin, amma a kowane lokaci sai ƙungiyar Agaji ta Red Cross ta kange mu daga yin hakan, tana mai cewa sai mun samu izinin yin hakan daga gwamnati ko hukumomi.

Mata huɗu kawai muka iya gani suna hutawa, a kofar shiga cibiyar, amma da dama daga cikin mutanen da muka gani matasa ne masu ƙannan shekaru.

Mun samu nasarar tattaunawa da Ahmed, wani matashi mai shekara 20 daga Masar ta hanyar mai gadin cibiyar.

Ya ce ya yi tafiyar kwana uku a jirgin ruwa daga Libiya kafin ya zo nan. yayin da muke tsaka da tattaunawa wasu sojoji biyu sun katse mana hira, nan da nan sai Ahmed ya ce musu yana faɗa mana ne yadda yake samun komai a nan.

Ya ce da yawa daga cikin 'yan ci-ranin na tsoron yin magana da 'yan jarida.

...
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Da yawa daga cikin 'yan ci-ranin a yanzu an sauya musu matsuguni zuwa wasu cibiyoyi cikin Italiya.

A makon da ya gabata firaministar Italiya, Giorgia Meloni ta ziyarci ɗaya daga cikin cibiyoyin tare da shugabar gudanarwar tarayyar Turai, Ursula von de Leyen.

Cikin wani jawabi da ta yi mai cike da balagar harshe amma ba tare da yin cikakken bayani ba, Misis Meloni ta kira ƙaruwar ƴan ci-rani a ƙasar da 'mamaya' ko 'yaƙi'.

To sai dai magajin garin tsibirin, Filippo Mannino ya faɗi saɓanin hakan.

"Tsibirin ya shafe fiye da shekara 30 a haka, amma ga mutanen da ke wajen tsibirin sai su dauka tamkar wani tashin hankali ne, sai su dauka tamkar yaƙi ko rigima tsibirin ke fuskanta, amma mu mun san cewa wanan ba wani abin damuwa ba ne", in ji shi.

Tarayar Turai na shirin aika wa Tunisiya yuro biliyan ɗaya (dala miliyan 872) don bunkasa tattalin arzikinta domin hana 'yan ƙasar yunkurin tafiya ci-rani zuwa ƙasashen Turai.

Sai dai akwai saɓani tsakanin ƙasashen Turai dangane da 'yan ci-ranin.

Gwamnatin Faransa ta ce ba za ta amince da shigowar 'yan ci-rani daga tsibirin Lampedusa ba.

...

Yanayin Lampedusa zai yi wahalar magancewa ba tare da haɗin kan gwamnatocin ƙasa da ƙasa ba.

Tsibirin bai yi kama da yankin da yake fuskantar tashin hankali ba, mazauna wurin ba sa amfani da salon da ƴan siyasar Italiya suke amfani da shi wajen kwatancen Lampedusa.

Amma sun shirya ɗaukar matakin kariya ga waɗanda suke taimaka wa masu shigowa tsibirin domin su daina fuskantar tsangwama.

Mista Mannino ya ƙara da cewar "Ba ni da ikon samar da mafita, aikina shi ne kulawa da gari.''

"Tilas mu zaɓi yadda za mu tallafi mutane tsakanin ƴan Ukraine da suke tsere wa yaƙi da ƴan Afirika da suke tsere wa yaƙi da hukunci. Shin za mu ɗauke su abu ɗaya ne ko za mu bambanta su gwargwadon launin fatarsu?''