Hikayata 2024: Hajara Ahmad Hussain ce ta lashe gasar rubutu ta BBC Hausa

Hikayata 2024
Bayanan hoto, Hajara (ta uku daga hagu) 'yar jihar Jigawa ce a arewacin Najeriya
Lokacin karatu: Minti 4

Hajara Ahmed Hussain ce gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024.

Matar wadda uwar 'ya'ya biyar ce, ta yi nasara ne da labarinta mai suna Amon Ƴanci, wanda labari ne kan wata matashiya mai suna Aminatu da ke fafutuka.

Hajara, ta samu lambar yabo da kuma kyautar naira kuɗi 1,000,000.

An haifi Hajara Ahmed Hussain a unguwar Kuburu da ke Hadejiya a Jihar Jigawa da ke Najeriya. Ta yi karatun arabiya da boko har zuwa matakin difloma a fannin lissafi, yanzu haka Hajara na da aure da yara.

Amon Yanci: Labari ne a kan wata matashiya 'yar makaranta mai suna Aminatu, da take fadi tashi domin sama wa jama'arta 'yanci a kan matsalolin rayuwar da suka musu rubdugu, cikin rashin sa'a kuma sai ta tsinci talatarta a laraba inda ta kare a gidan yari.

Hajara ta kasance ma'abociyar karance-karance tun lokacin da take sakandire har zuwa lokacin da ta yi aure.

Takan yi rubutu a takarda da biro amma ba ta samu damar buga su ba har aka fara yi a yanar gizo a shekarar 2015 wanda ita ma ta fara yi a yanar gizo domin isar da sakonni masu yawa ga mutane.

Ya zuwa yanzu Hajara ta rubuta litattafai kusan 20 baya ga wasu gajerun labarai.

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama don kallon yadda aka karrama Hajara Ahmad Hussain

Amra Awwal ce ta zo ta biyu

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amra Awwal Mashi ce ta zo mataki na biyu a gasar Hikayata ta 2024.

Ta shiga gasar da labarinta mai suna Kura a Rumbu, wanda aka gina kan wata mace da ke yawan hira da maza a shafukan sada zumunta.

Amra ta samu kyautar kuɗi naira 750,000 da kuma lambar yabo.

Rayuwar Amrah:

An haifi Amrah a karamar hukumar Mashi ta jihar Katsina. Ta yi karatun addini da na boko duka a garin Katsina, har zuwa matakin digiri na farko. Amra na da aure da yara biyu. tana sha'awar karance-karance wanda ke ba ta kwarin guiwar yin rubutu. Ta fara rubutu a shekarar 2014. Amrah na sha'awar labaran ban tausayi masu saka kuka.

Labarin KURA A RUMBU: Labari ne a kan wata matar aure wadda ta kasance mai mu'amala da mazan banza da wayarta ta hannu a yanar gizo, a rashin saninta, za ta zama mabudin warwarar matsalar da ta addabi al'ummarta. Gambo Kidinafa ya yi amfani da ita domin cikashe manufarsa, kamar yadda mijinta Habu ɗansanda ma ya yi amfani da ita, Gambo ya shiga hannun hukuma. Da yake ba a fafe gora ranar tafiya, ta yi nadamar da ba ta da amfani a lokacin da rayuwa ta yi mata juyin waina a kasko.

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon yadda aka karrama Amra Awwal

Zainab Chubado ta zo ta uku

Zainab Muhammad CHubado ce ta zo ta uku a gasar Hikayata ta bana.

Zainab ta shiga gasar ce da labarinta mai suna Tsalle Ɗaya, wanda ta gina shi a kan wata mace mai suna Binta.

Ta samu kyautar naira 500,000 da kuma lambar yabo.

An haifi Zainab Muhammad Chibado a garin Kafancan na jihar Kaduna.

Zainab ta yi karatun firamare ne a birnin Kano, sannan ta yi karatun sakandare a garin kafancan.

Daga nan kuma ta tafi ta yi N.C.E Fedral collage of Education Kano, sannan ta juya B.Ed inda take karantar Education Social Studies. Yanzu haka tana shekarar karshe a jami'ar Ahmadu Bello.

Labarin Tsalle daya: Labari ne wanda aka gina a kan rayuwar wata baiwar Allah mai suna Binta, wadda tsautsayi da kaddara suka yi sanadin fadawar ta hannun yan garkuwa da mutane, ta sha matukar wahala a hannun su har hakan yai sanadiyar da ta rasa abu mafi mahimmanci a rauwarta, wanda hakan ya zame mata ciwo mafi wahalarwa a cikin tsokar zuciyarta.

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon yadda aka karrama Zainab Muhammad Chubado

Wannan ne karo na tara da BBC Hausa ke gudanar da irin wannan biki na karrama waɗanda suka yi nasara a gasar.

Hikayata gasa ce ta ƙagaggun gajerun labarai da ke samar da dama ga mata marubuta, ƙwararru da waɗanda ba su ƙware ba.

Gasar na ba su damar nuna fasaharsu da kuma bayar da damar karanta labaran nasu a harshen Hausa ga masu bibiyar kafofin watsa labarai na BBC.

Da farko dai BBC Hausa ta samu labarai kimanin 450 da marubuta daban-daban suka aiko, inda bayan tankaɗe da rairaiya aka miƙa labarai 400 ga alƙalai na sahun farko waɗanda duka malaman jami'a ne masana harshen Hausa inda suka tantance suka zaɓi guda 30.

Daga cikin 30 ɗin ne kuma alƙalan na ƙarshe suka zaɓi guda 15, inda 12 suka cancanci yabo sannan kuma uku suka zama zakaru.

Hoton marubutan da labaransu suka cancanci yabo

Za a karanta labarai uku na farko da kuma labarai 12 da alƙalan suka ce sun cancanci yabo tashar a tashar rediyo ta BBC da babban shafinta intanet da kuma kafafenta sada zumunta.

Waɗanda suka lashe gasar a shekara uku da suka gabata su ne:

  • Aisha Adam Hussaini - 2023.
  • Amira Souley - 2022.
  • Aisha Mohammed Dalil - 2021.