Saƙon gwarazan Gasar Hikayata ta BBC Hausa, 2023
Saƙon gwarazan Gasar Hikayata ta BBC Hausa, 2023
A ranar Alhamis ɗin nan BBC Hausa za ta sanar da gwarzuwar gasar ƙagaggun rubutattun labaru ta Hikayata, 2023.
Mata kusan 500 ne dai suka shiga wannan gasa, inda a matakin farko aka tantance labaran zuwa 400, kafin daga bisani a mataki na biyu na tantancewa wasu alkalai da ba ma'aikatan BBC ba ne suka zabi guda 30.
Wata tawagar alƙalan a mataki na karshe, bisa jagorancin ma'aikacin BBC sun zaɓi labaran 15 daga cikin 30 sannan kuma sun zabi gwarazan da labarinsu ya yi nasarar yin na ɗaya da na biyu da na uku.
Ga jerin labaran uku da suka yi fice:
Bakin Kishi - Aisha Abdullahi Yabo
Tuwon Kasa - Aisha Sani Abdullahi
Rina A Kaba - Aisha Adam Hussaini



