Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Isra'ila ta amince da Somaliland a matsayin ƙasa mai ƴanci?
- Marubuci, Wedaeli Chibelushi
- Marubuci, Ameyu Etana
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afaan Oromoo
- Marubuci, Farah Lamane
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Somali
- Lokacin karatu: Minti 4
Isra'ila ta sanar da amincewa da Somaliland a matsayin ƙasa mai ƴanci, lamarin da ya haifar da suka da taƙaddama daga wasu ƙasashen.
Isra'ila ce ƙasa ta farko a duniya da ta sanar da ɗaukar wannan matakin, kimanin shekara 30 bayan ta sanar da samun ƴanci daga Somalia.
Shugaban Somaliland ya kira amincewar ta Isra'ila da "nasara babba," amma Somalia ta yi watsi da lamarin, wanda ta ayyana a matakin karan-tsaye da take ƴancinta.
Haka kuma ƙasashe irin su Turkiyya da Saudiyya da tarayyar Afirka da wasu ƙungiyoyi na duniya sun soki matakin.
Haka kuma China ma ta sa baki a lamarin, inda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin ƙasashen wajenta Lin Jian ya bayyana wa manema labarai cewa, "bai kamata wata ƙasa ta goyi bayan wani yanki da ke neman warewa ko ɓallewa a cikin wata ƙasa ba saboda buƙatarta."
Ita kuma Amurka goyan bayan matakin Isra'ila ta yi a taron gaggawa na Majalisar Ɗinkin Duniya kan batun.
"A farkon wannan shekarar, ƙasashe da dama, cikin har da mambobin wannan kwamitin sun amince da ƴancin Falasɗinu, amma ba a kira taron gaggawa irin wannan ba," in ji mataimakin ambasadan Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya Tammy Bruce.
Shi ma mataimakin ambasadan Isra'ila a Majalisar Ɗinkin Duniya Jonathan Miller ya bayyana wa kwamitin cewa Isra'ila ba ta ɗauki matakin domin take ƴancin Somalia ba, "kuma ba mu rufe ƙofar tattaunawa a tsakanin ƙasashen ba."
Me ya sa Somaliland ke son ƴanci?
A shekarar 1991 yankin Somaliland ta sanar da samun ƴanci bayan an hamɓarar da mulkin gwamnatin soja ta Siad Barre.
Duk da cewa ba ta samu amincewar ƙasashen duniya ba, Somaliland ta cigaba da tsara mulkinta da jami'an tsaronta da ma kuɗinta.
Tarihinta ya faro ne tun a ƙarni na 19 a lokacin mulkin mallaka, inda ta kasance ƙarƙashin mulkin Birtaniya kafin ta haɗe da Somaliland da ke ƙarƙashin Italiya a shekarar 1960, inda aka samar da Jamhuriyar Somalia.
Waɗanda suke son ƴantacciyar Somaliland sun bayyana cewa yanki ya kasance mai cike da ƙabilar Isaaq ne suka fi yawa, waɗanda suke da bambanci da sauran ƴan ƙasar Somalia.
Sannan akwai kusan mutum miliyan shida a Somaliland, kuma sun daɗe suna morar zaman lafiya.
Amma Somalia tana ganin Somaliland a matsayin yankinta, inda gwamnatin Somalia ta daɗe tana cewa duk wani yunƙurin amincewa da Somaliland a matsayin ƙasa zai yi karan-tsaye ga ƴancin Somalia.
Me ya sa Isra'ila ta amince da Somaliland?
Da suke magana ta wayar tarho, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyhu ya faɗa wa Shugaban Somaliland Abdirahman Mohamed Abdullahi cewa sun amince da burin da ƙasar ke da shi na zama da ƙafarta.
Isra'il ta yi alwashin ba Somaliland goyon baya wajen inganta harkokin noma da kiwon lafiya da kimiyya da fasaha a tattalin arziki.
Sai dai masana suna ganin akwai wata buƙatar daban da ta sa Isra'ila ta sanar da amincewa da ƙasar.
"Isra'ila na buƙatar ƙasar da za ta zama ƙawarta a yankin Red Sea saboda wasu dalilai, ciki har da shirin fuskantar ƴan Houthi," in ji cibiyar masana ta nazarin tsaro a Isra'ila.
"Somaliland ce ƙasar da za ta fi taimakonta wajen samun wannan nasarar."
Isra'ila ta kai hare-hare kan ƴan Houthi a Yemen bayan da aka fara yaƙin Gaza na watan Oktoban 2023 bayan ƴan Houthin sun kai hari a Isra'ila, harin da suka bayyana na goyon bayan Falasɗinawa a zirin Gaza.
Da take martani kan amincewa da ƙasar Somaliland da Isra'ila ta yi, Houthi ta ce kasancewar Isra'ila a Somaliland, "babbar barazana" ce ga dakarunta.
A watannin baya ne wasu kafofin watsa labarai suka ruwaito cewa Isra'ila ta tuntuɓi Somaliland kan yiwuwar kai mata Falasɗinawa da aka kwaso daga Gaza.
Isra'ila ba ta ce komai ba kan batun, amma Somaliland ta ce batun amincewa da ƴancita da aka ba shi da alaƙa da batun Falasɗinu.
A nasa jawabin, mai sharhi kan harkokin yau da kullum na Afirka mazaunin Amurka, Cameron Hudson ya shaida wa BBC cewa Isra'ila ta amince da Somaliland ne saboda daƙilewa ko rage ƙarfin Iran a yankin tekun Red Sea.
Me ya sa ake sukar matakin Isra'ila?
Ƙasashen da suka soki matakin Isra'ila sun haɗa da Masar da Turkiyya da Saudiyya da tarayyar turai da Yemen da Sudan da Najeriya da Libya da Iran da Iraqi da Qatar.
Dukkansu sun yi Allah-wadai da amincewar, sannan suka bayyana amincewar a matayin "karan-tsaye ga ƴancin Somalia."
Za ta sake samun amincewar wasu ƙasashen?
Ƙasashen da ake gani a matsayin ƙawayen Somalia ko suke sonta ko ma suke ƙarfafa mata gwiwa duk sun yi tsit.
Misali, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da take a sansanin soji a yankin ba su ce komai ba har yanzu.
Mr Hudson ya shaida wa BBC cewa UAE "na tare da Isra'ila a game da batun Somaliland."
Mr Abdurahman ya ce Turkiyya ce ta shiga tsakani domin samar da maslaha tsakanin Somalia da Habasha bayan Somaliland ta bayar da hayan wani yankinta ga Habasha.
"Don haka duk da cewa Isra'ila ta sanar da amincewa da ƴancin Somaliland, kuma duk da cewa Habasha za ta ya maraba da lamarin a sirrance, dole za ta bi sannu a hankali," in ji masanin.
Mutanen Somalilan sun yi tunanin Amurka za ta amince da yankin a matsayin ƙasa mai ƴanci bayan Donald Trump ya yi nuni da hakan bayan ɗarewarsa karagar mulki.
Amma bayan Isra'ila ta sanar da matakin da ta ɗauka, Trump ya bayyana wa kafar New York Post cewa ba zai matakin gaggawa ba irin na Netanyahu.