Ake ya yi watsi da tayin West Ham, Camavinga ba ya son barin Madrid

Nathan Ake

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Ɗanwasan baya na Manchester City mai shekara 30 Nathan Ake ya yi watsi da tayin West Ham. City na son sayar da ɗanwasan na Netherlands international, wanda ƙungiyoyin Premier ke ribibinsa. (Talksport)

Manchester United na fuskantar barazanar hamayya daga Bayern Munich da Paris St-Germain kan ɗanwasan gaba mai shekara 19 na Ivory Coast Yan Diomande, wanda farashinsa ya kai fam miliyan 52 zuwa miliyan 61 a RB Leipzig. (Sky Sports)

Ɗanwasan Tottenham da Wales Brennan Johnson, mai shekara 24, ana sa ran diba ƙoshin lafiyarsa a Crystal Palace nan da sa'a 24 bayan amincewa da yarjejeniyarsa kan kuɗi fam miliyan 35. (Telegraph)

Bournemouth na cikin ƙungiyoyin Premier da suka nuna sha'awar ɗanwasan tsakiya na Arsenal da Ingila Ethan Nwaneri. (Mail - subscription required)

Borussia Dortmund za ta gwada taya ɗanwasan gaba na Norway Oscar Bobb, mai shekara a matsayin aro daga Manchester City idan har ta rasa ɗanwasan tsakiya na Amurka Cole Campbell, mai shekara 19, ko kuma ɗanwasan gaba na Belgium Julien Duranville, mai shekara 19 a Janairu. (Sky Sports Germany)

West Ham na dab da kammala cinikin Pablo ɗanwasan gaba na Gil Vicente, yayin da ake sa ran ɗanwasan na Portugal zai tafi diba lafiyarsa a London. (Guardian)

Brighton na sa ido kan ɗanwasan tsakiya na Nordsjaelland da Ghana Caleb Yirenkyi, bayan ta ɗauko ɗanwasan gaba na Ivory Coast Simon Adingra, mai shekara 23, da kuma ɗanwasan gaba na Ghana Ibrahim Osman, mai shekara 21. (Sky Sports)

Manchester United na son ɗanwasan Crystal Palace Jean-Philippe Mateta, wanda har yanzu ya ƙi tsawaita kwangilar shi da za ta kawo ƙarshe a 2027. (Football Insider)

Galatasaray na son karɓo aron ɗanwasan tsakiya na Manchester United da Uruguay Manuel Ugarte. (CaughtOffside)

Ɗanwasan tsakiya na Faransa Eduardo Camavinga, mai shekara 23, na son ci gaba da taka leda a Real Madrid duk da Liverpool ta nuna tana so. (Teamtalk)

West Ham na shirin taya ɗanwasan gaba na Spain da Fulham Adama Traore. (Football Insider)