Iran ta kunyata Amurka - Ayatollah

Lokacin karatu: Minti 3

Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya gabatar da jawabinsa na farko ga al'ummar ƙasar tun bayan harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar ƙasar a wani ɓangare na yaƙin da ya ɓarke tsakanin Isra'ila da Iran.

Kafar talabijin ta gwamnati Iran ce ta sanya jawabin na Ayatollah da yammacin ranar Alhamis, agogon Tehran.

Cikin jawabin nasa, Khamenie ya ce "babu wata illa" da ta faru da cibiyoyin nukiliyar Iran bayan harin da Amurka ta kai a farkon wannan mako.

Sai dai wannan bayani nasa ya ci karo da iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump wanda ya ce an "lalata" shirin nukiliyar Iran.

Khamenei ya ce: "Ina taya ku murna kan nasarar da aka samu a kan gwamnatin Yahudawa mai cike da kuskure".

Ya ce Amurka ta shiga yaƙin kai tsaye ne saboda ta fahimci cewa idan ba ta shiga ba, to gwamnatin Yahudawa za ta rushe gaba ɗaya.

Ayatollah Khamenei ya ƙara da cewa Amurka ba ta samu wata riba daga yaƙin ba, amma Iran ta fito da nasara kuma ya ce "Iran ta kunyata Amurka".

Ya ƙara da cewa "al'umma kusan miliyan 90 sun tsaya tsayin daka kuma da murya ɗaya wajen goyon bayan rundunonin tsaro."

Al'ummar Iran, a cewarsa, sun nuna halin jarumta kuma "a lokacin da bukata ta taso, murya guda ce ke fitowa daga gare su."

'Ba saboda makamin nukiliya ne Amurka ta kai mana hari ba'

A cikin jawabin nasa, jagoran addini na Iran ya nuna cewa Amurka ta kai wa Iran hari ba domin barazanar makamin nukiliya ba.

Ya ce ba saboda haɓɓaka makamashin nukiliya ba ne - sai dai domin neman "miƙa wuya".

"Wata rana su ce kare hakkin ɗan'adam, wani lokacin su ce kare hakkin mata, kuma sun ce batun nukiliya, daga baya kuma makami mai linzami," in ji Ayatollah.

Ya ce manufar Amurka kawai ita ce ta sanya Iran ta miƙa wuya.

Trump ya kira ga Iran ta "miƙa wuya", to amma wannan bai kamaci shugaban Amurka.

"Ga babbar ƙasa kamar Iran, buƙatar cewa ta miƙa wuya cin fuska ne," in ji Khamenei.

A ranar Lahadi ne Amurka ta ƙaddamar da hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, wato Fordo, Natanz da kuma Isfahan.

Amurka ta ce ta yi amfani da gagarumin makaminta na GBU-57, wanda shi ne kaɗai aka yi amannar zai iya yin illa ga cibiyoyin inganta makaman nukiliyar.

Sai dai daga baya batun tasirin da harin da ya yi ya haifar da gagarumar muhawara.

Yayin da shugaban Amurka Donald Trump ya ce "an lalata" shirin nukiliyar Iran, wasu bayanai na sirri da aka fitar sun nuna akasin haka.

An shafe sama da mako ɗaya ba tare da ganin jagoran na Iran ba a bainar jama'a tun bayan jawabin da ya yi wa ƙasar daga wani wuri da ba a bayyana ba a ranar 18 ga watan Yuni.