Arsenal da Man Utd na son Guehi, Barcelona na harin Williams

Arsenal da Manchester United za su fafata a zawarcin Marc Guehi, ganin cewa ɗan bayan ya shirya yin watsi da sabon tayin kwantiragin da Crystal Palace za ta yi masa. (Sun)

Ana sa ran Manchester United ta cimma farashin da aka gindaya na sayen Joshua Zirkzee fam miliyan 34, kafin a raba ɗan gaban na Netherlands mai shekara 23, da Bologna. (Mail)

United na tunanin ko ta biya wannan farashin na cikin yarjejeniyar ɗan wasan ko kuma ta yi cinikinsa a kan farashin da ya fi haka domin ta samu damar biyan kuɗin kashi-kashi a hankali. (Guardian)

Arsenal na fatan kammala cinikin Riccardo Calafiori a makon nan bayan ta tattaunawa da Bologna a kan ɗan bayan na Italiya mai shekara 22. (Guardian)

Shugaban Barcelona Joan Laporta ya ce ƙungiyar za ta iya sayen matashin ɗan wasan gaba na gefe na Sifaniya Nico Williams, mai shekara 21 wanda yake da yarjejeniyar sayar da shi a kan fam miliyan 49 a kwantiraginsa da Athletic Bilbao. (Catalunya Radio, daga ESPN)

Ipswich na da ƙwarin gwiwar sayen yan wasa biyu na Hull City, 'ayn Ingila - ɗan gaba Jaden Philogene, mai shekara 22, da ɗan baya Jacob Greaves, mai shekara 23, a kan kusan fam miliyan 35. (Talksport)

Idan kuma ba haka ba ita ma Everton tana da ƙwarin gwiwar doke Crystal Palace wajen sayen Philogene bayan wata yarjejeniya da suka yi da Hull. (Teamtalk)

Tottenham na duba yuwuwar musayar ɗan wasa tare da kuɗin, ita da Aston Villa kan ɗan wasan tsakiya na Villa ɗin Jacob Ramsey, mai shekara 23, da kuma na Spurs ɗin Giovani lo Celso, na Argentina mai shekara 28. (Sky Sports)

Stuttgart na shirin gabatar da sabon tayi a kan ɗan gaban Brighton Deniz Undav, na Jamus (Bild)

Tsohon kyaftin ɗin Wolves Danny Batth, ya koma ƙungiyar inda yake atisaye da tawagar ƴan wasanta na ƙasa da shekara 21 bayan da ya bar Norwich. (Express & Star)

Tottenham Hotspur na da ƙawin gwiwar riƙe matashin ɗan wasanta na gaba na gefe Mikey Moore, ɗan Ingila mai shekara 16 duk da sha'awarsa da Paris St-Germain da Real Madrid ke yi. (HITC)

Luton na cikin ƙungiyoyin da ke son matashin ɗan wasan tsakiya na Mechelen Ngal'ayel Mukau, mai shekara 19, wanda zai iya taka wa Belgium ko Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo leda. (HLN)

Chelsea ta cimma yarjejeniya da Atlanta United ta sayi ɗan bayan Amurka Caleb Wiley, mai shekara 19,a kan fam miliyan 8.5 - amma kuma ana sa ran za ta bayar da aronsa ga Strasbourg. (Athletic)

Ana sa ran Leeds United ta sayar da ɗan gaba na gefe na Holland Crysencio Summerville, dan ɗan gaba Georginio Rutter, na Faransa, da ɗan gaba Wilfried Gnonto, na Italiya a bazarar bana. (Football Insider)

Bayern Munich ba buƙatar ta sayar da wasu ƴan wasa kafin ta sayi wani - inda ake sa ran daga cikin waɗanda za ta sayar akwai Kingsley Coman, ɗan Faransa da ɗan bayan Netherlands Matthijs de Ligt, da ƴan wasan tsakiya na Jamus Leon Goretzka, da Joshua Kimmich, da Serge Gnabry, da kuma ɗan bayan Kanada Alphonso Davies. (Kicker)

Ɗan bayan Nice da Faransa Jean-Clair Todibo, yana son tafiya Juventus bayan maganar komawarsa Manchester United ta wargaje. (Gazzetta)

Sevilla na sha'awar sayen ɗan tsakiya na Sifaniya Saul Niguez, daga Atletico Madrid. (SER)