Hatsarin yin garkuwa da matasa 'yan hidimar ƙasa a Najeriya

    • Marubuci, Frey Lindsay
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

“Mun ji ƙarar harbin bindiga, shi ne direbanmu ya tsaya. Sai kawai masu harbin suka ce kowa ya sauko, sai suka raba mu suka ce mu kwanta a ƙasa mu yi rubdaciki sannan mu sanya kanmu a ƙasa, daga wannan sai suka kai mu cikin daji”.

Patience, wadda aka sakaya sunanta domin kare ta, tana magana ne a daren shekara ta 2023 da wasu masu garkuwa da mutane suka sace ta tare da wasu mutane goma yayin da suke tafiya a cikin wata motar bas ta hanyar karkarar jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.

Patience na kan hanyarta ta zuwa sansanin horar da ƴan hidimar ƙasa ne a farkon shirinta na yi wa kasa hidima na shekara guda, wato NYSC, wanda ya zama tilas ga waɗanda suka kammala karatun digiri a jami’o’in Najeriya da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha.

Masu yi wa ƙasa hidima waɗanda aka fi sani da "corpers," ana tura su zuwa yankunan karkara masu nisa don yin ayyukan hidimar jama'a, inda ake biyan su alawus-alawus duk ƙarshen wata.

Da shiga cikin daji, masu garkuwar suka buƙaci Patience da sauran waɗanda aka sace da su miƙa kayayyakinsu.

Bugu da kari, ɗaya daga cikin masu garkuwa da mutanen ya umurci Patience da ta kira mahaifinta ta ce masa ya biya kuɗin fansa har Naira miliyan 20 kimanin dalar Amurka 15,000 tare da yi mata barazanar za su kashe ta idan har bai biya kuɗin fansar ba.

"Na ce masa, idan ina da miliyan 20, ba za ka sami 'yata har ka sace ta ba," in ji mahaifin Patience yayin da yake tattaunawarsa da masu garkuwar.

"Da jirgi za ta bi zuwa garin kuma jami’an tsaro ne za su yi mata rakiya, ba ni da irin wannan kuɗin."

Lamarin dai ya nuna yadda ake fama da matsalar garkuwa da mutane a Najeriya, musamman a yankunan karkara, da kuma irin illar da waɗanda abin ya shafa da iyalansu ke fuskanta.

Suna da sauƙin kai wa hari

Yayin da al’amuran yin garkuwa da mutane ke ci gaba da ƙaruwa a faɗin Najeriya, matasan da suka kammala karatu kuma ke shirin yi wa kasa hidima (NYSC) sun nuna fargabar cewa za su zamo abin hari ga masu garkuwa da mutane.

A cewar gidauniyar binciken aikin jarida ta Najeriya, a cikin shekaru goma da suka gabata, an sace sama da masu yi wa ƙasa hidima 80.

Kodayake wannan adadin ya bayyana kaɗan idan aka kwatanta da mutane 4,427 da aka yi garkuwa da su a cikin 2023 kaɗai, masu yi wa ƙasa hidima na fuskantar lahani na musamman.

A matsayinsu na waɗanda suka kammala jami'a a ƙasar da wasu tsirarun matasa ne kawai ke shiga manyan makarantun gaba da sakandare, galibinsu sun fito ne daga iyalai masu arziki, wanda hakan ya sa masu garkuwa da mutane ke samun riba.

Bugu da ƙari, hauhawar farashin kayayyaki ya tilasta wa masu hannu da shuni su zaɓi hanyar sufuri mai rahusa da rashin tsaro zuwa yankuna masu nisa inda aka kai su yi wa ƙasa hidima.

"Masu garkuwa da mutane na ganin NYSC a matsayin harkar yin garkuwa da mutane saboda irin mutanen da hukumar ke turawa yi wa ƙasa hidima" a cewar wani manazarci kan harkokin tsaro Ikemesit Effiong na kamfanin SBM Intelligence.

Ga waɗanda suka kammala karatun digiri, janyewa daga yin NYSC ba wani zaɓi ba ne, saboda yawanci ana buƙatar takardar shaidar kammala NYSC wajen neman ayyukan yi a kamfanoni da masana'antu.

Mma Amara Ekeruche daga cibiyar nazarin tattalin arzikin Afirka ta bayyana ƙalubalen da ɗaliban da suka kammala karatunsu ke fuskanta wajen neman aikin yi musamman ma ga mata..

Damuwa game da lafiyar masu yi wa ƙasa hidima, wanda aka yi niyya don haɓaka haɗin kan ƙasa da hidimar jama'a sai ƙara ƙaruwa yake wanda ke nuni da buƙatar gaggawa na haɓaka matakan kare masu yi wa ƙasa hidima.

Rashin samun kariya

Matasan Najeriya da dama na amfani da shafukan sada zumunta na zamani wajen bayyana damuwarsu dangane da matsin lambar da suka fuskanta dangane da kammala yi wa ƙasa hidima (NYSC) da kuma takaicin yadda hukumomi suka kasa tabbatar da tsaron lafiyarsu.

A cikin shekarar 2021, wani hoto da aka yaɗa a kan shafin X ya bayyana wani shafi daga littafin NYSC wanda ke ba da shawara ga masu yi wa ƙasa hidima da ke tafiya kan takamaiman hanyoyi su shirya kuɗin fansa ko da za a sace su.

A cewar Ebenezar Wikina daga wata ƙungiya mai rajin ra'ayin matasa ta Policy Shapers, tattaunawa a shafukan sada zumunta galibi sun shafi fushi ne da kuma yadda hukumomi suka yi watsi da su, ta yadda za su ci gaba da kare kansu.

Yawancin waɗanda suka kammala karatun digiri sun bayyana aniyarsu na kin yi wa ƙasa hidima a wasu jihohi saboda tsoron kare lafiyarsu.

Duk da yunƙurin shawo kan lamarin, gami da umarni daga babban daraktan NYSC Yusha’u Ahmed da ya buƙaci masu yi wa kasa hidima da su ba da fifiko kan harkokin tsaro da kuma bin ƙa’idojin tsaro, amma har yanzu akwai damuwa.

BBC ta tuntuɓi hukumar NYSC da ma'aikatar harkokin cikin gida ta Najeriya domin jin ta bakinsu amma ba ta samu amsa ba.

Ita kuwa Patience wadda aka yi garkuwa da ita a farkon shirinta na NYSC, ‘yan uwanta ne suka sa baki wajen ganin an sako ta.

An dai shafe kwanaki tara ana tattaunawa tsakanin mahaifinta da masu garkuwa da mutanen, inda aka ci zarafin wasu da aka yi garkuwa da su.

Patience ta tuna da yanayi na baƙin ciki da ta jure, musamman a lokacin da aka yi ruwan sama mai tsanani a darenta na ƙarshe wajen masu garkuwa da mutane.

A ƙarshe dai, mahaifin Patience ya yi nasarar yin shawarwari game da kuɗin fansa zuwa adadin da zai iya tarawa daga dangi da abokai, don tabbatar da an sake ta.

Duk da cewa kuɗin bai kai Naira miliyan 20 da aka nema a farko ba, amma ya isa a sako ta.