Mutum ya yanke ƴaƴan marenansa cikin barci

Wuka da jini

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutumin yana mafarki ne yana zaune yana yanka nama

Wani manomi a Ghana yana can kwance a asibiti cikin wani mawuyacin hali bayan da ya yanke marenansa (golaye ko kwalatai) a lokacin da yake barci.

Mutumin mai suna Kofi Atta, wanda a gadon asibitin da yake ya gaya wa BBC yadda lamarin ya faru, yana can ana ƙoƙarin duba yadda za a yi masa aiki.

Ya ce a yanzu dai ana sa masa ƙarin ruwa ne tare da wasu allurai da ake ta yi masa, amma dai sai an yi masa tiyata.

Sai dai ya ƙara da cewa a yanzu ba shi da ko kudin da zai biya motar asibitin da za ta dauke shi zuwa babban asibitin koyarwa na Komfo Anokye, da ke Kumasi a kasar ta Ghana inda a can ne za a iya yi masa tiyata. 

Mutumin ya ce, yana barci ne na ƙailula wato da rana a kan wata kujera sai ya yi mafarki cewa yana yanka nama da ke ajiye a gabansa, wanda zai dafa abinci da shi, inda a cikin barcin ya janyo wuka ya yanke marenan nasa.

Mista Atta ya ce abin ya ba shi mamaki ƙwarai domin har lokacin da wasu maƙwabtansa biyu suka kawo masa agaji bai san me ya faru ba, sai da ya tashi daga kan kujerar ya riƙa jin wani zafi a gabansa ga kuma jini na zuba.

'Na yanke kwalataina ina barci'

Wuka da jini

Asalin hoton, Getty Images

Mutumin ya ce, har lokacin da aka kawo masa daukin ba shi tabbacin kan abin da ya faru, ji yake kamar yana mafarki ne.

Ya ce shi kansa bai san yadda aka yi ya dauko wuƙar ba ma, ''abin ya ɗaure min kai, '' in ji shi.

Manomin mai shekara 47 wanda ke garin Assim Akomfode a yankin tsakiyar kasar (Central Region), har bayan da ya yanke marenan nasa yana cikin barci har ya yi kururuwar neman taimako bai farka ba yana cikin mafarki ne domin shi duk bai san abin da ya faru ba a lokacin.

Ya ce duk da cewa maƙwabtansa sun kawo masa dauki inda ya riƙa jin zafi a gabansa ga kuma jini yana zuba, bai fahimci abin da ya faru ba, sai daga baya a gadon asibiti hankalinsa ya dawo ya san abin da ya faru.

Wasu labaran da za ku so ku karanta

Larurar da ke sa mutum ya yi wani abu cikin barci

A fagen ilimin kula da lafiya, akwai wata larura wadda ake kira Parasomnia a harshen Ingilishi, inda mutum kan aikata wasu abubuwa saɓanin na hankali a lokacin da yake barci.

Wannan larura takan sa mutum ya rika tafiya ko maganganu ko fitsarin kwance ko mugun mafarki ko ƙiƙƙifta ido da dai sauran abubuwa na daban a lokacin da yake barcin.

A lokacin da mutum yake cikin wannan hali wasu da ke tare da shi ko kusa da shi za su ga kamar ba barci yake ba yana farke ne, to amma yana cikin yanayi ne na barci bai san abin da yake yi ba.

Mutanen da ke cikin wannan yanayi ba ma sa iya tuna abin da ya faru da su ko abin da suka aikata a lokacin da suke cikin halin.

Bayanai sun nuna cewa abin da mutum kan yi a wannan lokacin kamar yana aikata abin da mafarkinsa ya kunsa ne a zahiri.