Mene ne amfanin daddawa ga lafiyar jikin ɗan'adam?

Lokacin karatu: Minti 3

Daddawa sinadari ce da ake amfani da ita a abinci sannan kuma tana bayar da kamshi mai daɗi.

To amma da yawa mutane ba su san cewa sinadari ce mai kyau da kuma amfani ga lafiyar ɗan'adam ba baya ga sanyata cikin abinci.

Daddawa na bayar da ɗandano mai daɗi fiye da sauran sinadarai da ake haɗawa don sanya wa abinci kamar su kori da sauransu.

Bata kyau a ido saboda kalarta, baƙa ce wuluk to amma a baki kuwa akwai ɗanɗano mai daɗi.

Wani abu kuma shi ne da yawan mutane ba sa son daddawa saboda warinta, to amma ƙamshinta shi ke ɗaukar hankalin masu amfani da ita.

Tana da sunaye daban-daban, ya danganta daga wanne ɓangare ka fito ko ƙabilarka ko kuma harshenka a Najeriya.

A ɓangaren Inyamirai ana kiranta da suna Ogiri, su kuwa Yarabawa Iru suke ce mata, yayin da Hausawa kuma ke kiranta da suna daddawa.

Ana samun daddawa ne daga (kalwa), wato ƙwallon bishiyar ɗorawa.

Ta yaya daddawa ke taimaka wa lafiyar jiki?

Daddawa na da sinadaran da dama da ke ƙara wa mutum lafiya a cewar wata ƙwararriya a fannin abinci, Vivian Onyenora Ujunwa.

Wasu daga cikin abubuwan da daddawa ke ƙarawa lafiyar ɗan'adam sun haɗa da:

  • Inganta lafiyar zuciya
  • Tana taimakawa wajen narkar da abincin da mutum ya ci.
  • Tana sa jini ya riƙa yawo a jikin ɗan'adam yadda ya kamata.
  • Tana inganta garkuwar jiki.
  • Tana ƙara ƙwarin kashi da na haƙori.
  • Tana sanya fatar mutum ta yi kyau da lafiya.
  • Tana ƙara ƙwari ido.
  • Tana taikawa wajen rage ƙiba.
  • Ta na kuma ɗauke da sinadarin Karbohidiret da Furotin da dai sauransu.

Amfani da daddawa na da illa?

Vivian Onyenora Ujunwa, ta ce daddawa na da matuƙar amfani fa lafiyar ɗan'adam, to amma shanta akai-akai ko kuma amfani da ita da yawa na da hadari.

Masu sarrafa daddawa kansa ta yi wari kafin a sayar da ita, to idan aka yi rashin sa'a aka samu wanda baya jure wa wari to hakan kan iya janyo masa ko mata matsala.

Wani lokaci za ka ji idan ya yi amfani da daddawa musamman a abinci to za ka ji idan ya shiga cikin mutane za a rinka jin warinta har ka ji wasu na tsokanarka suna cewa hala ka ci daddawa.

Sannan kuma a wajen haɗata, dole sai masu sarrafata sun kula sosai saboda gudun kada wata ƙwayar cuta ta shiga ciki a lokacin da ake haɗata.

A don haka domin ka kare kanka ko kanki daga kamuwa da wata cuta sakamakon amfani da daddawa, ya kamata a rage amfani da ita a abinci sosai sai dai jefi-jefi.

A waɗanne abubuwa ake amfani da daddawa?

Ana amfani daddawa a abubuwa da dama kamar:

*Ana sanya daddawa a miyar kaɗi, kamar miyar kuka da kuɓewa da karkashi da da makamantansu.

*Ana amfani da daddawa a dafadukan shinkafa ko taliya ko kuma fate-fate.

*Ana amfani da daddawa wajen yin farfesu ko na nama ko kaji ko kifi da dai sauransu.

*Ana amfani da daddawa a kwadon abinci ko kwadon gari ko na tuwo.

*Ana amfani da daddawa wajen hada yaji.

Ya ya ake haɗa daddawa?

Ana samun kalwa wanda ake samu daga 'ya'yan ɗorawa sai a gyara a zuba a tukunya a zuba ruwa sannan a ɗora a wuta a bar ta ta dahu idan ta dahu sai a sauke a wanke ta tas sannan a sake mayar da ita kan wuta.

Daga nan za a zuba abin da ake kira namijin kalwa wanda ake haɗawa da 'ya'yan zobo a haɗa da kanwa kadan a dake sai a zuba a cikin kalwar a barta ta sulala.

Sannan sai a sauke a zuba a turmi a kirɓa sai a zuba a ƙwarya ko buhu a rufe a barta ta kwana biyu.

Idan aka lura ta kusa fara wari to sai a ɗauko ta shanya daga nan sai a kara kirɓata bayan nan sai kuma a curata sannan a bar ta ta bushe kafin a yi amfani da ita.