Chelsea na bukatar maki uku ta kai zagayen gaba a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Chelsea ta ziyarci Red Bull Salzburg, domin buga wasa na biyar a cikin rukuni na biyar a Champions League da za su kara ranar Talata.
Wannan shi ne wasa na biyu da za su yi a gasar Zakarun Turai a tsakaninsu, bayan da suka tashi 1-1 ranar 14 ga watan Satumba a Stamford Bridge.
Daya wasan za a buga ne tsakanin Dinamo Zagreb da AC Milan a rukuni na biyar ranar Talata.
Chelsea ce ta daya a rukunin da maki bakwai, Salzsburg ce ta biyu mai shida, sai AC Milan da Dinamo da kowacce take da hur-hudu.
Kungiyar Stamford Bridge za ta kai zagaye na biyu idan ta yi nasara a wasan Talata, ko kuma ta yi canjaras, sannan AC Milan ta ci wasanta.
Chelsea za ta ja ragamar rukunin idan ta ci wasanta, sannan aka doke Dinamo Zagreb.
Salzburg za ta kai zagayen kungiyoyi 16 da zarar ta ci Chelsea, sannan Dinamo ta doke Milan.
Milan ba za ta kai zagaye na biyu ba, idan har aka zura mata kwallaye daga uku zuwa sama, za ta koma ta hudun teburi kenan, idan Chelsea ta kasa cin wasanta.
Haka kuma kungiyar Italiya ba za ta kai zagaye na biyu ba da zarar aka doke ta a Zagreb, sannan Salzburg ta ci Chelsea.
Ita kanta Dinamo ba za ta je zagayen kungiyoyi 16 ba, idan ta kasa cin wasa, sannan Chelsea ta hana Salzburg yin nasara a kanta.
Saboda haka za ta koma ta karshen teburi idan Salzburg da Chelsea suka tashi canjaras.
Ranar 2 ga watan Nuwamba za a buga wasa na shida a cikin rukuni, inda Chelsea za ta karbi bakuncin Dinamo Zagreb, sannan Salzburg ta ziyarci AC Milan.










