Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
APC ba za ta ci zaben shugaban kasa ba saboda 'yan takara Musulmai - Babachir
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya kuma jigo a APC, mai mulki Mista Babachir Lawan ya ce, jam’iyyar ba za ta ci zaben shugaban kasa da za a yi a 2023 ba saboda zaben mataimaki Musulmi da dan takarar shugaban kasar Bola Tinubu ya yi.
A tattaunawarsa da BBC Mista Babachir ya ce, sun yi bakin kokarinsu don ganin Tinubu wanda shi ma Musulmi ne, ya samu takara, amma daga baya sai suka fahimci ya yi musu rufa-rufa game da abokin takara ko mataimakinsa, lamarin da ya sa suka juya masa baya.
Tsohon sakataren ya ce APC ba za ta kai labari ba a zaben shugaban kasar, kuma zai iya faden jihohin da Bola Tinubu zai iya cin zabe da kuma wadanda ba zai ci ba.
Ya ce, '‘Ni dai kam ba na Bola Tinubu yanzu. Ni ba na Muslim-Muslim ticket.’’
‘’Shi Bolan ne bai zabe mu ba ya zabi inda yake so ya je, mun kuma gaya masa can daman ba za mu zabe shi ba in ya yi Muslim-Muslim ticket.’’ In ji shi.
Babachir ya kara da cewa PDP sun zo sun tattauna da su, kuma sun yarda za su yi musu abin da suke soi dan suka hada kai saboda haka sun yarda za su yi musu.
Ita ma jam’iyyar Labour ya ce kusan ma kwana suke yi a wajensu domin su tafi tare da su.
Ya ce Tinubu ba shi ya yi wa rufa-rufa ba ganin cewa sun tsaya kai da fata ya samu takara, ya ce dukkanin Kirista ya yi wa.
Ya kara da cewa matsalar babba ce irin wariyar da ya ce ana nuna wa su Kirista a Arewa, ‘’Ka ga problema din na ‘yan Arewan nan a ce kai Kirista ne samun aiki na mana wuya.’’
‘’Ka ga universities (jami’o’i) 27 a arewar nan biyu ne kawai Kirista na VC (shugaba). Polytechniques 27 guda biyu ne kawai Kirista na Rectotr (shugaba), nan ederal ke nan fa banda states’’ in ji shi.
Ya yi korafi da cewa wariyar da ake nuna wa Kiristoci a Arewa ta yi musu yawa,’’ Har ya zama kuma yanzu ka ce za ka yi Muslim-Muslim ticket to ka buga mana kusa a kaik e nan banda wanda aka buga mana a kafa.’’
Da aka yi masa, magana kan ko sun yi kokarin janyo Bola Tinubun domin dinke barakar, sai ya ce, ‘’A’a shi zai neme mu yanzu ba ni zan neme shi ba ai. Mu ai muna da inda za mu nufa inda za mu kafe. Amma bai neme mu ba.’’
‘’Shi ya ga zai ci zabe to za mu ga cin zaben da zai yi,’’ in ji Babachir.
Ya nanata cewa shi har yanzu yana nan a APC amma a shugaban kasa ba zai yi ba kuma mutanensa ba a su yi APC saboda zaben abin da Tinubun ya yi kasancewar shi Musulmi kuma ya zabi mataimakinsa Musulmi.
Ya ce akwai mutanensa masu neman gwamna da sanata da majalisar wakilai da majalisun jihohi a APC.
Game da cewa za a yi masa zargin y iwa jam’iyyar ta APC kafar-ungulu sai ya ce hakan bai dame shi ba a zage shi mana, ‘’su su gyara mana.’’ In ji shi.
Ya kara da cewa shi ba zai fita daga APC ba amma idan Buhari ya tafi shi ma zai tafi.
Idan Buhari ya bar siyasa shi ma zai bari domin saboda Buhari ya shiga siyasa.