Wasu manyan makusantan Shekarau da suka ki binsa PDP

Asalin hoton, Facebook/Shekarau New Media Team
Wasu jiga-jigan 'yan siyasa a Kano da ke arewacin Najeriua kuma makusantan tsohon gwamnan Jihar, Malam Ibrahim Shekarau, sun yi masa turjiya a yayin da ya fice daga jam'iyyar NNPP inda ya koma jam'iyyar PDP.
A farkon makon nan ne dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar ya karbi Sanatan da ke wakiltar Kano ta Tsakiya a majalisar dattawan kasar a wani kwarya-kwaryar biki da aka gudanar a birnin na Kano.
Shekarau ya ɗauki matakin komawa PDP ne sakamakon abin da ya kira "rashin adalci" da jagoran jam'iyyar NNPP kuma ɗan takarar shugaban ƙasarta a zaben 2023, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya yi musu wajen rabon kujerun da za a yi takara a kansu da wasu batutuwan.
Wannan ne karo na biyu da Sanata Shekarau ya sauya jam'iyya a cikin shekarar 2022 -- ya bar APC zuwa NNPP a watan Mayu, sai kuma ya bar NNPP zuwa PDP a Agusta.
Wannan lamari ya matuƙar jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ƴan Najeriya, musamman ma al'ummar jihar Kano.
Wasu na ganin tsohon gwamnan na Kano ba shi da alkiba inda yake sauya sheka a-kai-a-kai, yayin da wasu ke ganin matakin ya yi daidai saboda akidar Sanata Shekarau ta ganin cewa an tsare "gaskiya".
Kazakila batun ya raba kawunan magoya bayansa da kuma makusantansa a bangaren siyasa, musamman wadanda tare da su ya shiga jam'iyyar NNPP kuma tuni aka ba su takarar manyan kujeru.
'Ba za mu bi shi ba'
A cikin wadannan 'yan siyasa har da dan majalisar wakilan Najeriya Kabiru Alhassan Rurum, wanda ya ce ba su ji dadin fitar Sanata Shekarau daga NNPP zuwa PDP.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A hirarsa da BBC, ya ce matakin tamkar wata kaddara ce da Hausawa kan ce ta riga fata.
''Ba mu ji dadin abin da ya faru ba, mu ire-irenmu wadanda muka dawo jam'iyyar NNPP tare da Malam Ibrahim Shekarau mun kai hamsin da biyar, wasu na da mukamai wasu 'yan takara ne a mukamai daban-daban, kuma muna nan a jam'iyyarmu ta NNPP."
Kabiru Rurum, wanda ke takarar majalisar tarayya a zaben 2023, ya ce sun amince da tsare-tsare da kuma "manufofin da aka kafa jam'iyyar NNPP kuma ba za mu fita daga cikinta ba."
Shi ma Abdulrahaman Kawu Sumaila, wanda ya dade yana gwagwarmaya tare da Sanata Ibrahim Shekarau, yana cikin jam'iyyar NNPP, inda yake takarar majalisar dattawa mai wakiltar Kano ta Kudu.
Sanata Ibrahim Shekarau ya koma jam'iyyar NNPP a watan Mayun da ya gabata daga APC mai mulkin Kano bayan rikici tsakaninsa da Gwamna Ganduje, wanda ya kai ga zaɓar shugabannin jam'iyyar biyu.
Dama dai wani jigo a jam'iyyar ta NNPP, Injiniya Buba Galadima,ya shaida wa BBC ya ce ya tabbatar "kashi 90 cikin dari na magoya bayan Sanata Shekarau ba za su bi shi zuwa jam'iyyar PDP ba", inda ya ce za su ci gaba da zama a jam'iyya NNPP.











