Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Paris St-Germain ta dauko dan wasan Uruguay Manuel Ugarte
Paris St-Germain ta kulla yarjejeniya da dan kwallon Sporting Lisbon Manuel Ugarte a kan fan Euro miliyan 60.
Dan wasan Uruguay mai shekaru 22, ya sanya hannu a yarjejeniyar shekaru biyar domin taka leda a Parc des Princes har zuwa shekara ta 2028.
Chelsea da Tottenham da kuma Liverpool duk sun yi zawarcin dan wasan.
"Na yi matukar jin dadin daukar wannan babban matakin. Zan zage damtse a PSG," in ji Ugarte.
Ugarte ya buga wa Uruguay a wasa takwas kuma shi ne dan wasa na uku da sabon kocin PSG, Luis Enrique tun da ya maye gurbin Christophe Galtier a ranar 5 ga watan Yuli.
PSG ta dauko Marco Asensio daga Real Madrid da kuma Milan Skriniar daga Inter Milan.