Isra’ila ta sanar da ranar kai farmaki ta ƙasa a birnin Rafah

A karon farko, Isra’ila ta sanar da lokacin da zata ƙaddamar da hari ta ƙasa a birnin Rafah da ke kudancin Gaza.

Wani ɗan majalisar yaƙin Isra’ila, Benny Gantz ya yi gargaɗin cewa za su afkawa Rafah, nan da makwanni uku, idan Hamas ba ta sako mutanen da ta yi garkuwa da su ba.

Da ya ke magana a ranar Lahadi, Mr Gantz, wanda tsohon ministan tsaro ne ya ce wajibi ne duniya ta sani, kuma shugabannin Hamas su sani cewa idan har aka shiga azumin watan Ramadan ba a sako mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su ba, za a ci gaba da gwabza yaƙi a ko’ina, har a cikin Rafah.

Ana sa ran fara azumin Ramadan ne a ranar 10 ga watan Maris.

Mr Gantz ya ƙara da cewa Isra’ila za ta yi tsari mai kyau na kwashe fararen hula daga yankin, da haɗin gwiwar Amurka da Masar.

Majalisar yaƙin Isra’ila ta ƙumshi manyan jami’an tsaron ƙasar.

An kafa ta ne kwanaki bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba da mayaƙan Hamas suka kai Isra’ila, wanda ya kashe mutane aƙalla 1,220, tare da yin garkuwa da wasu 253.

Har yanzu Isra’ila na ganin cewa akwai sauran mutane 130 da Hamas ke tsare da su a Gaza.

Yayin da ya rage makwanni uku a fara azumin Ramadan, rahotanni daga Rafah sun ce akwai tsirarun mutane da ke tserewa daga garin, inda suke tafiya ba tare da tabbacin wajen da za su je ba.

Duk da matsin-lamba daga kasashen duniya, Firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya sha alwashin afkawa Rafah ta ƙasa, domin aiwatar da abin da ya kira ‘‘kawar da mayaƙan Hamas’’ daga yankin.

Kawo yanzu dai hukumomi a Isra’ilan ba su fayyace yadda suke fatan aiwatar da harin ba.

Ana dai ci gaba da nuna adawa da shirin Isra’ila na ƙaddamar da hari ta ƙasa a Rafah daga sassan duniya. Yanzu haka Falasɗinawa aƙalla miliyan ɗaya da rabi ke zaman neman mafaka a garin.

Tun da farko, Majalisar Dinkin Duniya ta ce aiki ya tsaya cak a babban asibitin Gaza, bayan harin da Isra’ila ta kai.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce an hana ta damar shiga asibitin Nasser da ke Khan Yunis a Arewacin Rafah, domin ganin halin da ake ciki.

A ranar Alhamis dakarun Isra’ila suka shiga asibitin, inda suka ce bayanan sirri sun tabbatar masu cewa a ciki Hamas ta ɓoye mutanen da ta yi garkuwa da su.