Rasha za ta janye fice daga shirin tashar sararin samaniya

Rasha za ta janye daga haɗakar tashar ƙasa da ƙasa da ke sararin samaniya ISS bayan shekarar 2024 ta gina tata tashar.

Sabon shugaban hukumar sararin samaniyar Rasha Yuri Borisov, ya ce kafin wannan lokacin hukumar ta Roskosmos za ta kammala dukkan abubuwan da suka kamata a yi.

A shekarar 1998 ne, Amurka da Rasha da wasu ƙasashen abokan hulɗa suka yi nasarar kammala aikin ƙaddamar da tashar ISS.

Amma tun bayan da Rasha ta kutsa Ukraine dangantaka ta yi tsami, kuma a baya Rasha ta sha yin barazanar janyewa daga shirin saboda takunkuman da ƙasashen yammacin duniya suka ƙaƙaba mata.

Tashar ISS – wacce tasha ce ta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin sararin samaniya na ƙasashe biyar – tana zagaye duniya daga sararin samaniya tun 1998, kuma ta gudanar da dubban bincike da gwaje-gwaje na kimiyya.

An amince da fara aikinta har zuwa 2024, amma Amurka ta so ta tsawaita hakan da wata shida bisa amincewar dukkan abokan hulɗar.

A wani taro da shugaban Rasha Vladimir Putin ya halarta, Mr Borisov ya ce an ɗauki matakin ficewa daga yarjejeniyar ne bayan shekarar 2024.

“Ina ga zuwa yanzu za mu fara ƙoƙarin samar da tashar sararin samaniya mai zagaye duniya ta Rasha,” kamar yadda Mr Borisov ya faɗa, yana mai cewa sabuwar tashar da Rasha za ta samar ɗin a yanzu shi ne abu mafi muhimmanci a wurinsa.

Mista Putin ya amsa masa da cewa “hakan ya yi kyau.”

Har yanzu babu tabbas kan ko me matakin yake nufi ga tashar ISS ta yanzu, inda wani babban jami’in hukumar sararin samaniyar Amurka ya shaida wa Reuters cewa ba a sanar da Nasa shirin na Rasha ba a hukumance.

Da gaske Rasha take?

Rashawa sun daɗe suna magana kan janyewar ƙasar amma babu tabbas kan ko da gasken-gaske suke yi.

Sun yi magana a kan gina tasu tashar ta Russian Orbital Service Station, wato Tashar da ke zagaye sararin samaniya ta Rasha – amma hakan na buƙatar kuɗaɗe da dama irin waɗanda gwamnatin Rashar ba ta taɓa zubawa ba a harkar da ta shafi tashar ISS ta yanzu.

Kazalika, kayayyakin da Rasha ke amfani da su a tashar ISS duk sun tsufa, amma injiniyoyin na ganin za su iya ci gaba da aiki har zuwa shekarar 2030.

Idan Rasha ta janye, babu haufi za a samu matsala.

An tsara tashar ISS ce ta yadda dukkan ƙasashen da ke da mallakinta za su dinga dogara da juna.

Ɓangaren Amurka na tashar ISS shi ke samar da wuta; Rasha ke lura da injinan da ke hana tashar faɗowa duniyar Earth daga sama.

Idan har Rasha ta janye wannan ɓangare na injinan, ya zama dole Amurka da Japan da Kanada da Turai su nemi wasu hanyoyin na ƙarfafa tashar don gujewa faɗowa.

Wannan wani abu ne da wasu jiragen Amurka marasa matuƙa da za su iya yi.

Ba a samu wata ɓaraka ba ta haɗin kai kan tashar ISS tsakanin Rasha da Amurka sakamakon yaƙin Ukraine, inda ƙasashen biyu suka sanya hannu kan wata yarjejeniya a farkon watan nan da za ta bai wa ƴan sama jannatin Rasha damar tafiya zuwa tashar a cikin rokar Amurka.

Kamar yadda ita ma Rashan ta yarda a dawo da ƴan sama jannatin Amurka da rokar Rasha wata biyu da suka gabata.

Yarjejeniyar za ta indaganta ci gaban haɗin kan a bisa tsarin shirin tashar ISS,” a cewar hukumar Roskosmos.

Sai dai kuma, yaƙin ya shafi wasu fannonin na haɗin kai tsakanin Rasha da ƙasashen Yamma.

Hukumar Sararin Samaniya ta Turai ESA ta kawo ƙarshen haɗin gwiwar tsakaninta da Roskosmos don aika wata roka zuwa duniyar Mars.

Sannan Rasha ta dakatar da aika jirgin sama jannatinta na Soyuz daga wajen da hukumar ESA ke harba su a ƙasar French Guiana.

Tarayyar Sabiyet da Rasha sun daɗe suna harkokin da suka shafi bincike a sararin samaniya, kuma sun cimma nasarori da suka haɗa da aika mutum na farko zuwa sararin samaniya a 1961, wanda ya zama wani abin tunƙaho ga ƙasar.

A ganawar da ya yi da Putin, shugaban Roskosmos, Mr Borisov ya ce sabuwar tashar samaniyar ta Rasha za ta samar wa da Rashar abubuwan da ake buƙata na zamani a sararin samaniyar.