Me ya sa ake zanga-zangar a saki Nnamdi Kanu a Abuja?

Asalin hoton, Getty Images
An girke jami'an tsaro a wasu manyan hanyoyi da muhimman wurare a Abuja, babban birnin Najeriya saboda zanga-zangar neman a saki Nnamdi Kanu.
Jagoran masu zanga-zangar dan gwagwarmayan kare hakkin dan'adam, Omoyole Sowore yana matsa lambar a saki shugaban kungiyar Ipob mai rajin ballewa daga Najeriya tare da neman kafa kasar Biafra.
Masu zanga-zangar sun ce niyyarsu ita ce su yi tattaki zuwa fadar Shugaba Tinubu da sauran muhimman cibiyoyin mulki.
Rahotanni sun ce 'yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye tun misalin karfe 7 na safe a kan wasu mutane da suka taru a titin shiga Abuja daga Nyanya.
Jami'an tsaro ciki har da 'yan sanda da sojoji da sauransu ne suka kafa shingayen bincike a kan tituna musamman wadanda suka nufi fadar Aso Rock.
Masu zanga-zangar sun ci alwashin ci gaba da shirinsu duk da gargaɗin da hukumomi suka yi bayan umarnin wata babbar kotun tarayya da ke takaita musu yin zanga-zangar a wasu sassan babban birnin Najeriya.
Sun tsara gudanar da zanga-zangar tasu ne a ranar Litinin 20 ga watan Oktoban 2025, don neman gwamnati ta sako jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, wanda ake tsare da shi tun a 2021, lokacin da jami'an tsaro suka kama shi a Kenya kuma suka mayar da shi Najeriya inda yake fuskantar tuhuma a kan ayyukan ta'addanci.
Injiniya Temple na cikin jagororin ƴan gwagwarmayar da suka shirya zanga-zangar, kuma ya shaida wa BBC cewa gangamin nasu na neman ƴanci ne.
Ya ce ''Za mu taru a Abuja, za mu je mu faɗa wa Tinubu cewa kawai ya ba da umarni a saki Nnamdi Kanu yau.
''Ba mu da damuwa da ƴansanda, ƴansanda ma za su raka mu, in shaa Allahu.''
Tun da farko, rundunar ƴansandan Najeriya ta gargaɗi masu zanga-zangar da su yi biyayya ga umarnin kotu da ya haramta masu yin gangami a wasu wurare na birnin Abuja ciki har da Aso Rock da majalisar dokokin tarayya da hedikwatar ƴansanda da dandalin Eagle Sqaure da kuma kan titin Shehu Shagari.
Sanarwar da kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin ya fitar ta yi gargaɗin cewa rundunar za ta ɗauki matakin doka a kan duk wanda ya nemi tayar da zaune tsaye.
"Kotu ta hana ko dai wannan ƙungiya ko kuma wata ta daban gudanar da zanga-zanga a Aso Rock da kewaye ,'' In ji sanarwar.
Masu zanga-zangar sun yi watsi da gargaɗin ƴansandan, tare da shan alwashin fitowa domin gangamin nasu kamar yadda suka tsara tun da farko.
A gefe guda kuma akwai wasu ƙungiyoyin na daban masu kira ga ƴan Najeriya, musamman matasa sun ƙauracewa zanga-zangar ta ranar Litinin.
Ƙungiyar matasan Najeriya wato National Youth Council of Nigeria (NYCN) na cikin masu adawa da zanga-zangar, kuma shugaban kwamitin riƙo ƙwarya na ƙungiyar, Buhari Ibrahim Shehu ya shiadawa BBC cewa sun ɗauki wannan matsaya ne don gudun abin da zai iya biyo bayan zanga-zangar.
''Abu ne wanda idan an fara shi kamar wasa ba ka san inda zai tsaya ba. Zanga-zanga ce a kan Nnamdi Kanu wanda maganar shi tana gaban kotu, be kamata a ce mun shiga an yi karan tsaye ga abin da ke gaban kotu ba,'' In ji Buhari Shehu.
Masu shirya wannan zanga-zanga a ƙarƙashin jagorancin ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowere, sun sha alwashin ci gaba da fafutuka har sai an saki Nnamdi Kanu.
Shari'ar Nnamdi Kanu
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shari'ar Nnamdi Kanu idan za ku iya tunawa tana gaban Mai shari'a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya, kuma har ta ba shi beli a kan dalilai na rashin lafiya a shekara ta 2017, sai dai Kanu ya tsere inda ya fitar ya bar Najeriya bayan sojoji sun gudanar da wani samame a gidansa da ke Umuahia cikin jihar Abia, kudu maso gabas.
A watan Yunin 2021 ne kuma jami'an tsaro a Kenya suka cafke Nnamdi Kanu, sannan ala tilas aka dawo da shi Najeriya don ya fuskanci shari'a.
Tuhume-tuhumen da aka yi wa jagoran kafa kasar Biafra sun kai 15, amma daga bisani aka rage su zuwa guda bakwai.
Duk da yake daga baya Kotun Daukaka kara ta rushe duk tuhume-tuhumen kuma ta sallame shi, sai dai Kotun Kolin Najeriya ta sake mayar da tuhume-tuhumen, kuma ta ce jagoran na Ipob akwai tambayoyi a kansa.
Nnamdi Kanu dai yana fuskantar tuhume-tuhume ne masu alaka da cin amanar kasa da ayyukan ta'addanci kafin daga bisani a mayar da shari'arsa zuwa gaban Mai shari'a James Omotosho.
A watan Satumba ne kuma, Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci a kan furucin wadanda ake kara na babu bukatar ci gaba da shari'a kan jagoran na Ipob saboda rashin gabatar da gamsassun hujjoji daga masu shigar da kara.
Mai shari'ah James Omotosho ya yanke hukuncin cewa gwamnati ta tabbatar da hujjoji kan karfin tuhume-tuhumen da take yi wa Nnamdi Kanu kuma bisa don adalci, akwai bukatar wanda ake kara ya shigar da bayanan kare kansa.
Haka zalika, kotun ta umarci kungiyar likitoci ta Najeriya ta gudanar da bincike a kan matsayin lafiyar Nnamdi Kanu don tabbatar da ko zai iya fuskantar shari'a da kuma ko akwai bukatar a mayar da shi zuwa Babban Asibitin Kasa daga cibiyar da ake tsare da shi ta hukumar tsaron farin kaya ta DSS.
Bayan kwanaki kalilan Kotun ta Abuja ta ki amincewa da bukatar a mayar da Nnamdi Kanu zuwa Babban Asibiti na Kasa.
Mai shari'a James Omotosho ya ba da hukunci ne bisa rahoton kungiyar likitoci ta Najeriya wanda ya ce Nnamdi Kanu yana da lafiyar da zai iya fuskantar shari'a.
A cewar rahoton, kungiyar likitocin ta ce bin diddigin da ta yi ya nuna cewa halin lafiyar da Nnamdi Kanu yake ciki ba mai barazana ga rayuwa ba ne kuma cibiyar lafiyan da ke harabar hukumar tsaron farin kaya ta DSS na da isassun kayan aikin da za a iya duba lafiyarsa a can.











