Jerin ayyukan Nnamdi Kanu da takun sakarsa da gwamnatin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Yusuf Akinpelu, Data Journalist
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa DIgital Team
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja babban birnin Najeriya ta yi watsi da bukatar bayar da belin shugaban haramtacciyar kungiyar 'yan a-ware ta Biyafara, (IPOB), Nnamdi Kanu.
A lokacin da take yanke hukuncin a ranar Talata 28 ga watan Yunin 2022, Mai shari'a Binta Nyako, ta ce bukatar aba ce da ke zaman cin zarafi ga shari'a, kuma yunkuri ne na ci gaba da magana a kan abin da aka riga aka yanke hukunci a kai.
Sai dai ta shawarci wanda ke neman belin da ya nufi kotun ɗaukaka ƙara a kan batun, idan bai gamsu da hukuncinta ba.
Babbar Kotun Tarayya a Abuja na tuhumar Mista Kanu, ɗan Najeriya wanda kuma yake da shaidar zama ɗan ƙasa ta Birtaniya ne da laifin cin amanar ƙasa da sauran tuhume-tuhume.
A bara ne aka dawo da sauraron shari'arsa bayan da Najeriya ta dawo da shi ƙasar daga Kenya bayan tserewar da ya yi da aka bayar da belinsa.
Tun bayan da ya ƙirƙiri ƙungiyar Ipob, ya yi ta sakin maganganu na jawo tashin hankali a kan gwamnatin Najeriya.
Ƙungiyar tasa na son ballewa ne daga Najeriya tare da kafa ƙasar Biyafara a kudu maso gabashin ƙasar, wato yankin ƙabilar Ibo.
Ga dai jerin yadda al'amura suka dinga gudana na ayyukan Ipob da kuma takun-saƙar da aka dinga yi tsakanin gwamnatin Najeriya da Nnamdi Kanu.















