Kotun ƙoli ta ce dole Nnamdi Kanu ya fuskanci shari'a

Asalin hoton, Getty Images
Kotun ƙoli ta Najeriya ta yi watsi da hukuncin wata kotun ɗaukaka ƙara ta ƙasar wadda ta ce madugun ƴan awaren Ipob, Nnamdi Kanu ba zai fuskanci shari'a ba kasancewar an kama shi ne ba bisa ƙa'ida ba.
Saboda haka nan alƙalan kotun suka ce za a ci gaba da yi wa Kanu shar'ia.
A yau ne kotun ta yanke wannan matsaya kan Nnamdi Kanu, wanda ke da mabiya a ciki da wajen Najeriya.
Shari'ar Nnamdi Kanu ta baya-bayan nan ta faro ne tun daga shekarar 2021, daga Babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Wannan dai shi ne kat, game da batun ko za a saki Nnamdi Kanu ko a'a, kasancewar ba za a iya ɗaukaka ƙara ba.
Yadda aka yanke hukunci

Mai shari'a Emmanuel Agim ne ya karanta hukuncin kotun, wanda Mai shari'a Garba Mohammed ya haɗa.
Hukuncin ya ce gwamnati ba ta kyauta ba a lokacin da ta kai samame gidan Nnamdi Kanu lokacin da kotu ta bayar da belin shi.
Haka nan gwamnatin ba ta bi ƙa'ida ba a lokacin da suka tafi farautar sa suka sato shi tare da mayar da shi Najeriya domin fuskantar shari'a.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar kotun ba a bi doka ba wajen yin hakan.
Sai dai kotun ta ce duk da ba a bi doka ba wajen kamo Nnamdi Kanu, hakan ba ya nufin cewa ba zai fuskanci shari'a ba.
Kotun ta ƙara da cewa kotun ɗaukaka ƙara ta yi daidai a hukuncin da ta yanke kan cewa bai kamata Kanu ya fuskanci shari'a ba saboda ba a bi ƙa'ida wajen kamo shi ba, ya yi daidai, sai dai wannan batu ne na dokar ƙasa da ƙasa.
Kotun ƙoli ta ƙara da cewa alƙalan kotun ɗaukaka ƙara sun gaza ambato wata doka ta Najeriya da ta goyi bayan hukuncin da suka yanke.
Alƙalan na kotun ƙoli sun ce babu irin wancan tanadi a dokar Najeriya, saboda haka ba za a iya yin watsi da ƙara ba saboda kawai an kamo wanda ake zargi da aikata laifi ba bisa ƙa'ida ba.
"Idan ƴan sanda sun lalata gidan wanda ake zargi a ƙoƙarinsu na nemo hujjoji, hakan na nufin za mu yi watsi da laifin da ake yi masa ke nan?
Mun yanke shawarar ƙin goyon bayan kotun ɗaukaka ƙara. Duk da cewa mun yi tir da take haƙƙoƙinsa."
Sai dai alƙalan sun ƙara da cewa: "Dole ne Najeriya ta dawo da martabarta a idon duniya kuma ta bi doka."
Hukuncin ya ƙara da cewa babu wata doka a Najeriya da ta ƙwace wa kotun ƴancin sauraron ƙara, duk da cewa gwamnatin tarayya ta aikata ba daidai ba.
"Wajibi ne doka ta yi aikinta"
"Saboda haka mun amince da ɗaukaka ƙaran da aka yi kuma mun kori koken (wanda ake zargi) ya yi." In ji Mai shari'a Agim.
A shekarar 2015 ne aka kama Mr Kanu amma ya tsere daga Najeriya a 2017 bayan an bayar da shi beli.
Ya kasance a tsare tun 2021 lokacin da aka tasa ƙeyarsa daga Kenya domin fuskantar tuhume-tuhumen ta'addanci.
A watan Oktobar bara ne, wata kotun ɗaukaka ƙara ta bayar da umarnin a saki Mista Kanu inda ta ce akwai kura-kurai a shari'ar.
Sai dai gwamnati ta sake shigar da ƙara inda ta ce Kanu barazana ce ga tsaron Najeriya.
Wasu shugabannin yankin kudu maso gabashin Najeriya sun nemi a saki Kanu.
Zaman kotun na baya
A zaman da ta yi na ƙarshe, ranar 5 ga watan Oktoba, 2023, kotun ƙolin ta ajiye ranar 15 ga watan Disamba a matsayin ranar da za ta yanke hukunci.
A lokacin zaman kotun na ƙarshe, lauyan gwamnati, Tijani Gazali ya buƙaci kotun ta yi watsi da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara wadda ta bayar da umarnin sakin Nnamdi Kanu.
Ya ce "Ina roƙon alƙalan wannan kotu kuma su yi watsi da ƙorafin da ɓangaren Kanu suka kawo mata saboda rashin cancanta."
A nashi ɓangaren, tsohon lauyan da ke jagorantar tawagar lauyoyin da ke kare Kanu, Mike Ozekhome ya buƙaci kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke.











