Yadda ƙwayar cuta ta farko da muke gamuwa da ita ke inganta lafiyarmu

Hoton yaro.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, James Gallagher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Correspondente de saúde e ciência
  • Lokacin karatu: Minti 3

Ƙwayar cuta ta farko da jikinmu ke gamuwa da ita - sa'o'i kaɗan bayan haihuwa - za ta iya kare mu daga cutuka masu haɗari, a cewar masana daga Birtaniya.

Sun bayyana cewa a karon farko, waɗannan ƙwayoyin cuta za su iya rage rabin barazanar da yara ke ciki na kwanciya rashin lafiya sakamakon kamuwa da ciwon huhu.

Masu bincike sun ce wannan wani "sabo ne kuma babban bincike" - kuma wanda zai saka a gano ƙwayoyin cuta masu alfanu cikin yara.

An yi imanin cewa ƙwayar cuta ta farko da muke gamuwa da ita, na da muhimmanci wajen cigaban garkwuwar jiki.

Kowane lungu da sako na jikin ɗan'adam wuri na rayuwar ƙwayoyin bacteria.

Masu bincike daga jami'ar College University a Landan da kuma cibiyar Sanger a Birtaniya sun yi bincke na yadda tsarin jikinmu yake a lokacin haihuwa da yadda ƙwayoyin cuta na bacteria da fungi da sauransu ke kasancewa.

An ɗauki bahayar da za a yi gwaji daga jarirai sabbin haihuwa 1,082 a makon farko na rayuwarsu. Daga nan, tawagar ta gudanar binciken ƙwayoyin halitta na DNA daga gwajin domin gano waɗanne irin na'u na ƙwayoyi ke ciki, kuma ya yawansu a cikin kowane jariri.

Sai kuma, suka bibiyi abin da ya faru da waɗannan jarirai, ta hanyar amfani da alkaluman asibiti a tsawon shekara biyu da suka biyo.

Hoton jaririya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An ɗauki bahayar jarirari sama da dubu ɗaya a matsayin wani ɓangare na gwaji don gano ƙwayoyin cuta da ke ciki

Ɗaya daga cikin abin da ke fara zama a cikin jikin ɗan'adam shi ne wata ƙwayar cuta da ke wajen jijiyar da ta haɗa ciki zuwa maƙogoro, ta bayyana cewa tana da kariya.

Kashi huɗu na jarirai da ke da wannan na'uin za su shafe dare a asibiti da ciwon huhu a shekaru biyu masu zuwa. Yaran da ke da ƙwayoyin cuta na farko daban-daban sun fi sau biyu zuwa uku na buƙatar kulawa.

Waɗannan su ne alkaluma na farko da ke nuna cewa samuwar ƙwayoyin cuta na shafar haɗarin kamuwa da cuta.

Nigel Field, farfesa a jami'ar UCL, ya shaida wa BBC cewa "Ina tsammanin abin mamaki ne da gaske. Yana da ban mamaki a iya nuna wannan.

Ta yaya waɗannan ƙwayoyin cuta ke yin haka?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Abin da ya fi haddasa buƙatar kai yara asibiti shi ne ƙwayar cuta da ke shafar numfashi (RSV) - amma menene ya danganta wannan cutar da wadda ke taimakawa wajen narkar da abinci?

Wannan ita ce "tambayar da aka fi yi," a cewar Field.

Mun san cewa B. longum na farawa ne ta hanyar narkar da madarar nono, wadda ke ɗauke da abincin jarirai kuma yana motsa kwayoyin cuta masu kyau.

Ba a kai ga gano ainihin cikakkun bayanai ba tukuna, amma ƙwayoyin cuta da kansu, ko abubuwan da suke samarwa yayin narkewar abinci, suna hulɗa tare da garkuwar jiki "kuma suna tasiri kan yadda garkuwar jiki ke girma kuma yana iya bambanta abubuwa," in ji Field.

Ana samun ƙwayoyin cuta masu kariya ne kawai a cikin jariran da aka haifa, ba waɗanda aka yi wa uwanyensu aiki kafin haihuwarsu ba.

Masu bincike sun ce sakamakon aikinsu ba hujja ba ce ta yin abin da ake kira a turance 'vaginal seeding', inda ake amfani da wani soso don yaɗo sinadaran da ke cikin al'aurar mace ana shafawa a jikin jaririn da aka ciro shi daga ciki ta hanyar tiyata, da nufin samun tagomashin ƙwayoyin halittun da jariran da aka haifa ta hanyar naƙuda ke samu, domin bunƙasa garkuwar jiki da raguwar shiga hatsarin kamuwa da cutukan hanyoyin numfashi.

Ƙwayar cuta mai amfani na zuwa ne daga ɓangaren ƴaƴan hanji.

"Aikin tiyata lokacin haihuwa tsari ne na ceton rai, kuma zai iya zama hanya mafi dacewa ga uwa da jaririnta," kamar yadda likitar mata Louise Kenny na Jami'ar Liverpool da ke Birtaniya ta bayyana.

Ta ce yayin da aka ga alfanun a wurin yaran da aka haifa ba tare da tiyata ba, ba a ga haka ba wajen dukkan jarirai da aka haifa - don haka, "ana buƙatar yin ƙarin bincike don gano sauran abubuwan da ba a sani ba."