Yadda ƙasashe 11 da suka taɓa lashe Afcon za su fafata a zagaye na biyu a Morocco

Asalin hoton, Getty Images
A gasar Afcon guda uku da aka buga a baya, manyan kasashe sun kasance suna shan wahala, inda kananan tawagogi suka yi ta bayar da mamaki kan rawar da suka taka wajen fitar da manya daga wasannin.
Sai dai batun ba haka yake ba a gasar da Morocco ke shiryawa ba, inda manyan tawagogi suka yi tafiyar ruwa da kanana tun kan a kai ga zagayen ziri ɗaya ƙwalle.
Ranar Laraba aka kammala zagayen farko na rukuni, inda ƙasa ɗaya wato Zambia wadda ta taɓa lashe Afcon da ba ta kai bante ba, amma 11 daga ciki da suka taɓa ɗaukar kofin sun kai matakin ƴan 16 da za su ci gaba da karawar.
Mozambique daTanzania ne ba su taɓa kaiwa zagaye na biyu ba daga fitatu uku da aka yi wa alfarma, yayin da Sudan za ta buga zagayen ƴan 16 karo na biyu tun bayan da ta lashe kofin a 1970.
Kafin nan tawaga 12 ta kai zagayen gaba kai tsaye daga cikin rukuni har da bakwai da za su buga gasar cin kofin duniya a bana a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Yayin da ake sa ran buga wasa mai zafi a zagaye na biyu ranar Asabar tsakanin Senegal da Sudan a Tangier.
Senegal ta ja ragamar rukuninta da tazarar rarar kwallaye tsakaninta da Jamhuriyar Congo, kuma za ta yi wasan ba tare da ƙyaftin ɗinta ba, Kalidou Koulibaly wanda aka bai wa jan kati a karawar da suka doke Benin 3-0.
Amma suna da kwarin gwiwa a cikin tawagarsu, kamar yadda sauran manyan kasashen da ke fafatawa ma suke da shi, sun kuma samu damar hutar da muhimman ƴan wasansu gabanin karawa ta uku a rukuni, domin tuni sun tabbatar da gurbin zuwa zagaye ƴan 16.
Mai masaukin baƙi, Morocco na buga wasa ɗari-ɗari

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mai masaukin baƙi, Morocco ta kai zagaye na biyu da kwarin gwiwa da doke Zambia 3-0, hakan ya sa ta ja ragamar rukunin farko, bayan da ake sukarta da cewar tana buga wasan cikin ɗai-ɗari duk da cewar ita ce mai shira wasannin.
Har yanzu ana da ƙyaƙƙyawan fata ga mai masaukin baƙin, wadda ita c e kan gaba a mataki na ɗaya a taka leda a duniya a jadawalin Fifa, wadda ta kai daf da karshe a gasar kofin duniya a Qatar a 2022, shekara uku da ta gabata.
''Daga yanzu kowane wasa tamkar karawar karshe ce,'' in ji kociyan Morocco, Walid Regragui a shirin da yake na fuskantar Tanzaniya a katawar zagaye na biyu ranar Lahadi a Rabat.
Kawo yanzu Aljeriya da Najeriya ce suka lashe dukkan wasansu na cikin rukuni a gasar ta Afcon ta bana, ana kuma hasashen Super Eagles ce za ta kai zagayen gaba ranar Litinin a wasan da za ta yi da Mozambique.
Sai dai kuma fafatawar da Aljeriya za ta kece rainin da Jamhuriyar Congo a Rabart ranar Talata ita ce ta fi jan hankalin masu bibiyar tamaula, ganin kwazon da tawagogin suka yi a rukuni da kuma fitattun ƴan wasan da suka kai Morocco da gogewar kowanne.
"Zai zama babban wasa, domin su babbar tawaga ce, haka mu ma," in ji mai tsaron bayan Algeria, Mehdi Dorval, bayan nasarar Algeria a kan Equatorial Guinea ranar Laraba.
Kididdigar zagayen farko a gasar Afcon a Morocco

Asalin hoton, BBC Sport
Tawaga 24 ce ta barje gumi cikin rukuni shida dauke da hurhudi kowanne da ta kai yanzu saura 16 suka rage da za su ci gaba da neman lashe kofin Afcon na bana.
Tun farko kasashe biyu ne a kowanne rukuni su ka bante daga baya aka tsinto hudun da suka kare a mataki na uku a teburi, amma da sakamako mai kyau da ya hada da Mozambique da Benin da Sudan da kuma Tanzania.
An kuma zazzaga kwallo 87 a gasar, inda yan wasa uku ne kan gaba a wannan kwazon masu uku-uku a raga
da ya hada da kyaftin din Algeriya, Riyad Mahrez da guda biyu daga Morocco mai masaukin baki da ya hada da Brahim Díaz da kuma Ayoub El Kaabi.
An kuma bayar da jan kati bakwai da kuma katin gargadi mai ruwan dorawa guda 10.
Jadawalin wasannin zagaye na biyu
Wasannin da za a buga ranar Asabar 3 ga watan Janairu

Asalin hoton, BBC Sport
Wasannin da za a kara ranar Lahadi 3 ga watan Janairu

Asalin hoton, BBC Sport
Karawar ranar Litinin 4 ga watan Janairun

Asalin hoton, BBC Sport
Fatatawar ranar Talata 5 ga watan Janairu

Asalin hoton, BBC Sport














