Sojojin Faransa sun azabtar da al'ummar Kamaru - Macron

    • Marubuci, Paul Njie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News in Yaoundé
  • Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron ya amince da irin uƙubar da dakarun ƙasarsa suka yi wa al'ummar ƙasar Kamaru a lokacin gwagwarmayar ƴancin kai da bayan nan.

Wannan dai ya biyo bayan wani rahoton hadin gwiwa tsakanin masana tarihin ƙasar ta Kamaru da na Faransar da suka yi waiwaye dangane da zaluncin Faransa a kan masu gwagwarmayar neman ƴanci a tsakanin shekarun 1945 zuwa 1971.

A wata wasiƙa zuwa ga shugaban Kamaru, Paul Biya da aka bayyana ga ƴan ƙasar ranar Talata, Macron ya ce rahoton ya fayyace cewa "yaƙi ya faru a Kamaru lokacin gwamnatin turawan mulkin mallaka sannan kuma sojojin Faransa sun aikata zalunci daban-daban a yankuna da dama na ƙasar."

"Yanzu ya rage a gare ni na ɗauki alhakin rawar da Faransa ta taka a lokutan," in ji Macron.

To sai dai Macron bai fito fili ya nemi afuwa ba dangane da zaluncin da dakarun sojin ƙasar tasa suka aikata kan tsohuwar ƙasar da suka yi wa reno wadda ta samu ƴancin kai a 1960.

Shugaban na Faransa ya kuma lissafa wasu jiga-jigan mutane guda huɗu da suka yi fafutukar neman ƴancin kai waɗanda kuma sojojin na Faransa suka kashe: Mutanen sun haɗa da Ruben Um Nyobe mai zazzafan ra'ayi da ke jagorancin jam'iyyar UPC mai adawa da turawan mulkin mallaka.

Faransa dai ta kulle dubban ƴan Kamaru a sansanonin azabtar da waɗanda ake ɗauka a matsayin maƙiya sannan kuma ta goyi bayan azzaluman masu ɗauke da makamai wajen daƙile yunƙurin neman ƴancin kai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito rahotan na faɗi.

Dubban ɗaruwawan mutane ne aka kashe tsakanin 1956 da 1961, in ji rahoton na masana tarihi.

Dalilin yin wannan bincike da kuma wallafa shi dangane da rawar da Faransa ta taka a gwagwarmayar samun ƴancin kan ƙasar Kamaru, ya samo asali ne a 2022 lokacin da Macron ya ziyarci Yawunde, bayan matsin lamba daga ƙasar na dole ne Faransa ta amince da rawar da ta taka.

BBC ta nemi gwamnatin Kamaru ta tofa albarkacin bakinta dangane da amincewar da shugaban Faransar ya yi na muguntar da dakarun ƙasarsa suka yi wa al'ummar Kamarun.

Duk da cewa Macro bai yi magana ba dangane da batun biyan diyya, amma akwai yiwuwar hakan ne zai zama batun da za a yi ta tattaunawa a Kamarun.

A ƙarƙashin mulkin Macron dai, Faransa ta yi yunƙurin yin fito na fito da tsoffin ƙasashen da ta mulka.

A bara, Faransa ta yarda a karon farko cewa sojojinta sun ƙaddamar da "kisan kiyashi" a ƙasar Senegal inda aka kashe sojojin Afirka ta yamma a 1944.

A baya ma Macro ya amince da rawar da Faransa ta taka a kisan ƙare dangi na Rwanda a inda aka kashe ƴan ƙabilar Tutsi da Hutus, sannan kuma ya nemi afuwa.