Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da Trump ya ce kan sasanci da Iran
Shugaba Trump ya shaida wa wata kafar talabijin ta Amurka cewa, Iran ta nuna tana son sasanci amma a cewarsa bai gamsu da sharuddanta ba.
A wata hira da ya yi da kafar NBC ta wayar tarho a ranar Assabar, Donald Trump ya ce Iran tana son ƙulla yarjejeniya amma shi ne a yanzu ba ya so saboda bai gamsu da sharuɗɗanta ba.
Kodayake ya ki bayyana sharuɗɗan da yake nufi. Mista Trump ya ce bukatar Iran na yin watsi da duk wani buri na mallakar nukiliya dole ne ya kasance wani bangare na yarjejeniyar da za a cimma.
Ya ce harin da Amurka ta kai ranar Juma'a ya tarwatsa tsibirin Kharg - wata muhimmiyar cibiyar da Iran ke fitar da mai.
A nata bangaren kuma Iran ta kaddamar da hare-hare a sassan Gabas Ta Tsakiya inda Amurka ta yi kira ga yan kasarta su gaggauta ficewa kasashen.
A hirar, Mr Trump ya yi ikirarin cewa kasashe da dama sun amince su tura jiragen ruwa na yaki zuwa mashigin Hormuz, amma ya ki bayyana sunayen kasashen.
Masu sharhi sun ce kalaman Mr Trump sun ci karo da na baya da ya yi inda ya ce Amurka ta kai hari ne kawai kan sansanonin soji a tsibirin Kharg.
A safiyar Lahadi, Iran ta yi luguden makamai masu linzami a Isra'ila wadanda rundunar sojin Isra'la ta ce ta kakkaɓo.
Haka ma Iran ta kai hare-hare sassan Gabas ta tsakiya, yayin da Amurka ta fitar da wani gargaɗi ga ƴan ƙasarta su gaggauta ficewa ƙasashen.
Saudiyya ta ce ta harbo jirage marar matuka bakwai a Riyad da kuma yankin gabashin ƙasar,
Haka ma hukumomi a Dubai da Qatar sun ce sun yi nasarar daƙile wasu hare-hare na makamai masu linzame da jirage marar matuka daga Iran.