Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 15/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 15/03/2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Hotunan ɓarnar hare-haren Isra'ila a Iran

    An samu fitowar sabbin hotunan ɓarnar hare-haren Isra'ila a Iran.

    Iraniyawa na share ɓaraguzan gidajen da suka lalace a Tehran, babban birnin ƙasar.

    Tun da farko Isra'ila ta ce ta ƙaddamat da ''manyan hare-hare a yammacin Iran, sai dai har yanzu babu labarin ɓarnar da suka haifar.

  2. Isra'ilawa fiye da 100 aka kai asibiti cikin sa'a 24 - Ma'aikatar lafiyar ƙasar

    Ma'aikatar lafiyar Isra'ila ta ce mutum 108 ne aka kai asibiti sakamakon raunukan da suka samu a cikin sa'o'i 24.

    Ta ce daga cikin wannan adadi, 96 sun samu ƙananan raunuka, biyu na cikin matsakaicin yanyi, yayain da tara ke buƙatar gwaje-gwaje.

    Tun bayan fara musayar hare-hare tsakanin Isra'ila da Iran, ma'aikatar lafiyar Isra'ila ta ce mutum 3,195 ne aka kai asibiti domin yi musu maganin raunukan da suka samu, sakamakon hare-haren makamai masu linzami da Iran ke kai wa ƙasar.

    Ma'aikatar lafiyar Isra'ilar ba ta bayar da rahoton adadin mutanen da suka mutu.

  3. Ɓarnar da hare-haren cikin dare suka yi a Holon na Isra'ila

    An samu sabbin hotunan da ke nuna ɓarnar da hare-haren cikin dare suka yi a birnin holon da ke kudancin Tel Aviv, a Isra'ila.

    An ga yadda wata mota ta kife, yayin da ɓaraguzai suka warwatsu, sai kuma wani ƙaton rami da hari ya haifar a kusa da wani gina.

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar (MDA) ta ce ta yi wa wasu mutum biyu da suka jikkata a hare-haren maganin ƙananan raunukan da suka samu.

    Wani tsoho mai shekara 80 ya samu raunukan tsagewar gilashi, yayin da wata tsohuwa mai shekara 80 ta samu matsalar numfashi saboda shkara hayaƙi.

    An kuma kwantar wa mutane da dama hankali da suka firgita a lokacin harin, a cewar hukumar ta MDA.

  4. Iran ta sha alwashin 'farautar' Netanyahu domin 'kashe' shi

    Sojojin Iran sun sha alwashinkashe firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Iran suka ruwaito.

    Kamfanin dillancin labarai na Mehr ya ce dakarun juyin juya halin ƙasar za su ''ci gaba da farautar Netanyahu domin kashe shi da ƙarfin tsiya''

    Rundunar ta IRGC ta yi ikirarin cewa ta kai hare-hare cikin Isra'ila da sansanonin sojin Amurka uku a yanzkin Gabas ta Tsakiya a karo na 52 na hare-haren da ta ƙaddamar.

  5. Mojtaba Khamenei 'na cikin ƙoshin lafiya' - Araghchi

    Ministan harkkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce sabon jagoran addinin ƙasar, Mojtaba Khamenei na cikin ƙoshin lafiya.

    Cikin wata hira da kafar yaɗa labarai ta Alaraby Aljadeed ya ce sabon jagoran addinin na ''cikin yanayin cikakken iko da ƙasar''.

    • Sabon jagoran dai, bai bayyana a bainar jama'a ba tun bayan naɗa shi a matsayin ranar 8 ga watan Maris. Sai dai a ranar 12 ga watan Maris an yaɗa jawabinsa ta kafofin yaɗa labaran ƙasar.

    Ya ce Iran na maraba da ''yunƙarin ƙasashen Gabas ta Tsakiya na kawo ƙarshen yaƙin''.

    Abbas Araghchi ya ce Iran za ta buɗe mashigar Hormuz amma ban da jiragen ruwan Amurka da ƙawayenta.

    Sai dai Araghchi ya ce ''zuwa yanzu babu wani yunƙuri na kawo ƙarshen yaƙin''.

  6. Labarai da dumi-dumi, Iran ta sake harba makamai masu linzami zuwa Isra'ila

    Rundunar sojin Isra'ila (IDF) ta fitar da sabon gargaɗi ga ƴan ƙasar, tana mai cewa ta hango makamai masu linzami da OIran ta harba cikin ƙasar.

    Hare-haren su ne na biyar da Iran ta ƙaddamar cikin Isra'ila a cikin sa'o'i tara.

    Sojojin Isra'ilar sun buƙaci ƴanƙasar da ke zaune a wuraren da makaman suka hara su nemi mafaka.

  7. 'An kai hari sansanonin sojin Amurka a Iraƙi'

    Jami'an tsaro a Iraƙi sun ce an kai harin jiragen sama marassa matuƙa kan wani sansanin sojin Amurka da ke kusa da filin jirgin sama na Bagadaza, babban birnin ƙasar.

    Rahotanni sun ce wuta ta tashi ganga-ganga a sansanin, amma ba a ji komai ba game da ko harin ya jikkata ko halaka wasu.

    An kai harin ne ƴan sa'o'i bayan da ofishin jakadancin Amurka a Bagadazan ya yi kira ga dukkanin Amurkawa da har yanzu ke ƙasar Iraƙi su fice nan take.

    A ranar Juma'ar da ta gabata ma an kai hari da jiragen sama marassa matuƙa kan ofishin jakadancin na Amurka da ke Bagadazan.

    Ofishin ya ce ƙungiyoyin ƴanbindiga da ke goyon bayan Iran, suna kai wa wuraren da ke da alaka da Amurka hari na makaman roka da jirage marasa matuka a Iraƙi.

  8. Iran ta yi barazanar faɗaɗa yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya

    Iran ta yi barazanar ta faɗaɗa yaƙin da take yi zuwa maƙwabtan ƙasashe, inda ta yi kira ga Hadaddiyar Daular Larabawa ta fara kwashe ƴan ƙasarta daga yankunan da ke kusa da tashoshin jiragen ruwa a Abu Dhabi da Dubai da kuma Fujairah.

    Yayin da rikicin ya shiga mako na uku, Iran ta ci gaba da harba muggan makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan kayayyaki da cibiyoyi na ƙasashe makwabtanta da kuma Isra'ila.

    Duk da ruwan bama-bamai ba ƙaƙƙautawa tsawon mako biyu na sojojin Amurka da suka fi ƙarfi ainun, Iran ta ci gaba da ƙaddamar da hare-hare.

    Wani mai bayar da shawara na diflomasiyya ga shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, ya mayar da martani da cewa ƙasarsa tana da ƴancin kare kanta, amma ta zaɓi ta ci gaba da amfani da hankali da tunani.

    An ji fashewar bama-bamai a Manama, babban birnin ƙasar Bahrain.

  9. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun karshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku ci gaba da tafka muhara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.