Rayuwa a Gaza: 'Babu wurin fakewa a ruwan makamai masu linzami'

"Duk harin da aka kai, sai ka ji kamar girgizar ƙasa ce ta ke faɗawa gine-gine - Ina jin tsoro ya cika zuciyata jikina duka na ɓari," in ji Nadiya, wata wadda aka sakaya sunanta.
Ƙarar rushewar ƙofofi da tagogi ce ta tashe ta daga barci a safiyar ranar Litinin.
"An fara harba makamai ne da misalin ƙarfe 8 na safe kuma haka aka ci gaba har tsakiyar dare, ba a ƙaƙƙauta ba ko na daƙiƙa ɗaya."
Matar mai ƴaƴa biyu maza, na farko ɗan shekara biyar ne na biyun kuma shekararsa uku, tana zaune ne a wani gida da suka saye wanda suka gyara ba da jimawa ba.
Tana zaune ne a gidan tare da yaran, yayin da mijinta da ke aiki da ƙungiyoyin lafiya na duniya yake aikin taimaka wa waɗanda suka jikkata.
"Mene ne ke faruwa? Yaushe zai tsaya?" Tambayar da babban yaronta ya riƙa yi mata ke nan.
Ta ce hanya ɗaya da take kwantar masa da hankali ita ce faɗa masa cewa ƙarar duk wani abin fashewa na zuwa ne bayan abin ya fashe da mintuna" - shi ne kawai abin da yake ba shi natsuwa.
Wani ilimi ne na rayuwa da ɗan shekara biyar bai kamata ya sani ba- amma a wajen mahaifiyarsa babu yadda ta iya dole ta shaida masa amma ta wata hanyar ta daban.
Hare-haren sun firgita yaronta ɗan shekara uku abin da ya kai ga hana shi cin abinci.

Ta ƙi yarda ta fita daga gidanta na tsawon kwanaki, "inda duk wani saƙo da lungu ke ciki da abubuwan tunawa".
Amma a ranar Litinin da daddare tana zaune sai ta ji makwaftanta na sakkowa daga bene suna ihun a taimaka a kwashe su.
Matar dai ta ƙi motsawa amma ƙwaƙwalwarta ta kasa zama lafiya. Kawai sai ta ji ta fashe da kuka na rashin mai taimako.
Nan da nan ta fice daga ginin cikin sauri tare da yaran nata, ba ma ta iya gane ginin makwaftan nata ba saboda an yi kaca-kaca da gidansu.
Yanzu hankalinta ya koma kan cewa ta tafi gidan iyayenta amma sai ta tambayi kanta "ina za ka shiga lokacin da mutuwa ke zuwa daga sama?"
Nadiya sauran mutanen da BBC ta zanta da su, sun shaida cewa illar da harin ya yi wa Gaza ya wuce hankali.
'Babu wurin tsira a Gaza'

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A gefe guda kusa da makwabta a Rimal, wata matashiya mai shekara 39 ta fice daga gidansu tare da iyayenta da wasu ƴan'uwanta da ke wajen wani lambu.
Unguwar yanki ne da babu hayaniya kuma ba shi da nisa da cikin gari.
A yammaci Litinin ne, ƴan gidansu suka fara jin karar makamai masu linzami a makwabta.
"Mun zaci abin ba zai zo kanmu ba, kwatsam sai muka ji ƙarar taga ta fashe, kofofi sun karye suna tashi sama," in ji Dina "wani ɓangare na rufin gidan ya sakko daidai kanmu."
Abin kaɗuwa ne, sun maƙale a cikin ruguzajjen gidan, saboda wasu makamai shida da suka ƙara durowa yankin.
Abin yana ƙara munana sai Dina da ƴan'uwanta suka tsere daga inda suke rayuwa, suka bar duk wani mallakinsu.
Sun garzaya asibiti domin karɓar magani ga raunukan da suka ji, Dina ta ce sun yi sa'a nasu raunin bai yi tsanani ba.
Lokacin da suka koma gida domin duba abin da suka mallaka, sai suka tarar sai kufai.
Yanzu suna zaune ne a wani gida na makwabta, har yanzu Dina na tuna wannan masifa "mun yi asarar gidanmu da kayanmu da inda muka saba da shi".
Ta ƙara da cewa "Babu wani wuri da ke da aminci a Gaza."
Asibitoci na fama wajen ceto rayuka

A asibitin Al-Shifaa, wanda shi ne babban asibiti a yankin mai cike da jama'a, shugaban asibitin Dr Mohamed Abo Sulaiman ya ce yanayin ya ƙazanta.
"Aƙalla mutum 850 sun mutu, 4,000 kuma sun jikkata," in ji shi.
Asibitin ya dogara ne kan wutar lantarki, yanzu kuma da aka yanke wutar, suna da ta kwana uku ne kacal da za ta yi musu saura.
Yayin da Isra'ila ta sanar da yi wa Gaza ƙawanya baki ɗaya, yanzu babu ruwan da aka tace da ake samu daga teku a asibitin.
Dr Abo Sulaiman ya ce yanzu sun dogara ne kawai da ruwa mai kyau "domin ceto rayuka" kuma yanzu sun rufe wasu sassan asibitin domin mayar da hankali kan ceto rayukan mutane.

Likitan na cikin fargaba kan tsirar waɗanda yake jinya, kazalika da ma'aikatansa - ya ce ana harar motocin ɗaukar marasa lafiya a harin da ake kai wa garin haka kuma har an kashe wani likita guda ɗaya.
A cewar Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Falasɗinu ta MDD cikin kwana guda an samu ƙaruwar mutanen da suka ɓata sama da 187,000 da waɗanda suka tsere suna neman mafaka.
Hukumar ta samar da tantuna 137,000 ga waɗanda ke neman mafaka sai dai ci gaba da hare-haren da ake samu ya haifar da fargabar tantunan za su cika maƙil nan ba da daɗewa ba.
Babu kowa a shaguna
Ishaq mai shekara 27 da haihuwa na zaune ne da mahaifiyarsa da mahaifinsa da surukarsa mai ƴaƴa biyar da ke zaune a Shujaiyya.
Bayan Firaiministan Isra'ila Netanyahu ya shaida wa ƙasarsa za su shiga yaƙin nan gadan-gadan bayan harin da Hamas ta kai a ranar Asabar, Ishaq da iyalansa sun yi hasashen abubuwa marasa kyau za su iya faruwa.
Sun ɗauki duka abubuwan da suka mallaka masu muhimmanci kowa cikin su ya ɗauki jaka guda suka kuma nemi tanti a tsakiyar gari.
A hanyarsu ta fita sun nemi kantin zamani domin sayan abubuwan da za su ɗan rika tabawa sai dai sun ce duka shagunan a rufe suke biyo bayan abubuwan da suke faruwa.
"Mun zauna a can kusan kwana biyu babu wuta babu ruwan sha," in ji Ishaq.
Da yammacin Litinin suka samu sanarwar daga sojojin Isra'ila su fice daga yankin, abin da ya tsiratar da su ke nan daga hare-haren sama.
"Babu abin da muke gani a ko ina sai rusassun gine-gine."














