Ko ECOWAS za ta iya jure wa ƙalubalen da ke gabanta?

    • Marubuci, Chris Ewokor
  • Lokacin karatu: Minti 6

Yayin da take cika shekara 50 da kafuwa, ana iya cewa ECOWAS ta fuskanci faɗi-tashi da dama da kuma jerin nasarori da ƙalubale tamkar dai wani mutum da shekarunsa suka fara nisa.

"Sau tari ba mu godiya kan nasarorin da muka samu," Inji ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Tuggar.

An fara tunanin kafa ƙungiyar ta ƙasashen yammacin Afirka ne bayan shugabannin yankin sun fara hangen yadda za su dunƙule waje guda domin ƙarfafa haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki.

A ranar 28 ga watan Mayun 1975, aka kafa ƙungiyar bunkasa tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) lokacin da shugabannin ƙasashen yankin suka sanya hannu kan yarjejeniyar kafa ta a Lagos.

Ƙudirin su kakkyawar fata ce- inganta alaƙar kasuwanci da bunƙasa hada-hadar jama'a da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Jama'ar yankin dai sun fuskanci abubuwa da dama masu kamanceceniya da suka haɗa da cinikin bayi da yanka kan iyakoki da Turawan mulkin mallaka suka yi da kuma rashin ci gaba, waɗanda sa nan da nan suka yi amanna da tunanin kafa ƙungiyar.

Sai dai kuma yayin da ECOWAS ke cika shekara 50 da kafuwa, dambarwar siyasa da ta ke fama da ita na nuni da tangaɗin da makomar ta ke yi.

Tabbatar da zaman lafiya da gida ƙasa

A farkon kafuwarta, ECOWAS ta samu yabo da jinjina saboda matakan gaggawa da ta ke ɗauka a kan zaman lafiya da tsaro.

Ta amfani da tawagarta ta ECOMOG, ƙungiyar ta shiga tsakani wajen kawo ƙarshen yaƙin basasa da wanzar da zaman lafiya a ƙasashen Liberia da kuma Sierra Leone.

Daga baya kuma ta shiga tsakani a rikicin da aka yi a Côte d'Ivoire da Guinea-Bissau da kuma Gambia.

A hirar sa da BBC, shugaban hukumar gudanarwar ECOWAS, Alieu Omar Touray, ya ce waɗanda suka kafa ƙungiyar sun yi hakan ne da fatan cewa za ta zamo hanyar kawo haɗin kai da ci gaban yankin da ma faɗaɗa shirin zuwa nahiyar Afirka baki ɗaya.

Ya ce "Tun da farko an mayar da hankali ne kan yadda za a zamo tsintsiya maɗauri ɗaya tsakanin jama'ar yankin da kuma bayar da damar gudanar da harkokin kasuwanci babu shamaki a tsakanin su.''

"Fatan ita ce ta hanyar kasuwanci a tsakanin mutnen yankin za a bunkasa alaƙa a tsakanin su da kuma taimakawa wajen fitar da jama'a daga talauci da kuma tabbatar da haɗi kai tsakanin jama'a da shugabannin yankin.''

Mr Touray ya ce ECOWAS ta ci gaba da zama babbar abin koyi wajen bunƙasa harkokin kasuwanci babu shamaki kuma babu haraji a yankin.

"Da katin shaida na ECOWAS, za ka iya tashi daga Lagos zuwa Dakar ba tare da neman visa ba. Ga irin mu da muke tafiye tafiye a nahiyarmu, mun sani cewa wannan ba ƙaramin ci gaba bane.'' Inji Mr Touray.

Ya bayar da misali da wani babban ɗan kasuwar Afirka da ya yi iƙirarin cewa yana buƙatar visa 39 domin tafiya ƙasashen sauran nahiya, amma a Afirka babu mai buƙatar visa kafin ya shiga ƙasashe.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ya ce baya ga inganta yadda ake zirga-zirga tsakanin jama'ar yankin, ƙungiyar ta kuma zamo mai tallafawa ƙasashen manbobin ta.

Ya ce "Ka ɗauki misalin nasarar da aka samu a ƙarƙashin hukumar lafiya ta ƙasashen yammacin Afirka, West African Health Organization (WAHO). Ba a cika magana a kan nasarar wannan tsari ba.''

"Muna ganin manyan ayyukan ci gaba kamar na jan bututun gas da tashi daga Najeriya zuwa kƙasashen yammacin Afirka da kuma Marocco, wanda ake sa ran zai shiga har Turai.''

Amma wani ƙudirin ƙungiyar da ya gagara shi ne samar da kuɗin bai ɗaya da ƙasashen yankin za su yi amfani da su.

Tun ƙumgiyar tana da shekara 20 wannan buri ke yawo kuma har yanzu ya ci gaba da zama buri, duk da cewa shugabannin yanki na cewa har yanzu da sauran fatan tabbatuwar sa.

A watan Afirelun bana shugabannin manyan bankunan ƙasashen yammacin Afirka sun yi wani taro da ministocin kuɗi na ƙasashen domin tattauna yadda za a samar da kuɗin bai ɗaya a yankin kafin 2027.

Shugabannin sun ce a shirye suke su aiwatar da shirin amma akwai ƙasashen da ba su kai ga cika ƙa'ida ba tukun.

Matsalar diflomasiyya a yankin Sahel

Duk da nasarorin da ta samu, makomar ECOWAS na cikin halin rashin tabbas.

A yanzu ƙungiyar tana fama da manyan ƙalubale da suka haɗa da rikicin siyasa a tsakanin mutanen da a baya suke mata kallon abin koyi.

A cikin shekaru huɗu da suka wuce ƙungiyar ta tsinta kanta a wani yanayi na zaman doya da manja tsakani ta da matasan sojojin da suka ƙwace mulki a yanki Sahel.

Daga 2020, an kifar da gwamnatoci a Mali da Guinea da Burkina Faso da kuma Nijar.

Babban ba zatan ECOWAS ya faru ne a cikin watan Yulin 2023, lokacin da sojojin da ke gadin shugaban Nijar, Mohamed Bazoum, suka hamɓarar da gwamnatin sa, suka kuma tsare shi.

A yunƙurin su na ganin juyin mulkin bai yi nasara ba, shugabannin ECOWAS sun bayar da wa'adi ga sojojin domin su janye matakin nasu, kum daga baya suna ƙaƙaba masu takunkumin tattalin arziki da ma barazanar ɗaukar matakin soji a kansu. Amma duk babu bazaranar da ta yi nasara a ciki.

Wanna ya sa an samu taɓarɓarewa alaƙa tsakanin ECOWAS da ƙasashen Nijar da Burkina Faso da kuma Mali. Daga baya ƙasashen uku suka fice daga ƙungiyar.

Manazarta dai sun riƙa tambayar ko ECOWAS ta zamo irin karen nan mai haushi amma baya cizo ne, saboda ficewar ƙasashen uku.

Shugaban hukumar gudanarwar ECOWAS Alieu Omar Touray ba za a ɗora masa laifi ba saboda bari ƙasashen uku na yankin Sahel su fice daga ƙungiyar.

Ya ce shiga ƙungyar ba tilas bane kuma ƙasashen da ke ciki suna mutumta matakin duk wata ƙasa da ta zaɓ fita.

Rashin nagarta

Ba ficewar ƙasashe ne kaɗai ke barazana ga ECOWAS ba, akwai kuma mutanen yankin da ke bayyana ra'ayoyi mabanbanta a kan tasirin ta.

Wasu sun ce sun yaba da ƙoƙarin ECOWAS amma suna cikin ruɗani game da aiwatar da shirin ta na tabbatar da walwala babu shamaki tsakanin jama'ar yankin.

Sun jajirce cewa wasu daga cikin nasarorin da ƙungiyar ta samu a baya sun bi iska saboda rashin yarda da ke yawaita a tsakanin jama'a.

''Mutane da dama ba su iya yin tafiya zuwa wasu ƙasashe cikin kwanciyar hankali saboda ana tare su a kan iyakokin ƙasashe.'' In ji Nana Adjei daga Ghana.

Ya yi iƙirarin cewa ana cin mutumcin matafiya tare da karɓar kuɗi a hannun su a kan iyakokin ƙasashen yankin.

Shi ma Marvis Sejuro daga Ghana ya yarda cewa tsarin tafiya babu shamaki na ƙungiyar ECOWAS ba ya aiki.

Ya ce "Akwai matsala a tsarin tafiye-tafiyen mu daga ƙasa zuwa ƙasa,''

"Kwanan nan na yi tafiya daga Accra zuwa Lome kuma akwai matsala. Ana neman ka bayar da cin hanci ko da kuwa kana da cikakkun takardun ka.''

Yayin da ya rage sauran ƙasashen 12 a ƙungiyar, ana ci gaba da kiran a gudanar da sauye-sauye a ECOWAS, kuma wasu na tambayar ko za ta iya ci gaba da gudana.

Amma shugaban hukumar gudanarwar ECOWAS, Omar Alieu Touray ya ce akwai abubuwa da dama da suka sanya a gaba.

Ya ce "Ina sane cewa mafi rinjayen mutanen yammacin Afirka sun fi son ECOWAS ta ci gaba da zama mai haɗa kan ƙasashen.''

"Akwai ƙalubale babu shakka, amma hakan baya nufin ba za mu iya shawo kansu. Cikin sasanci da laluma za mu iya magance wasu daga cikin matsalolin da suka janyo mana rashin fahimta.''