Yadda ficewar Nijar da ƙawayenta daga Ecowas za ta shafi kasuwanci da tafiye-tafiye a yammacin Afirka

Sojojin da ke mulkin ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso sun kara tabbatar da yanke hulɗa da ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma wato Ecowas.

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne ƙasashen uku suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya ƙarƙashin sabuwar ƙungiyar ƙawancen ƙasashen yankin Sahel (AES), tare da jaddada shawararsu ta ficewa daga ƙungiyar tarayyar ƙasashen yankin.

Mali ta kasance a ƙarkashin mulkin soja tun shekara ta 2020, ita kuma Nijar tun 2023, abin da ya tunzura ƙungiyar ta Ecowas ta ƙaƙaba wa ƙasashen takunkumai da zimmar tursasa musu komawa kan turbar dimokraɗiyya.

Da suka tashi mayar da martani, sai ƙasashen uku suka yanke shawarar ficewa daga ƙungiyar.

Cikin fiye da shekara 40, yarjejeniyar Ecowas ta tabbatar da ƴancin zirga-zirgar jama'a da kayayyaki a yankin, wanda ya bai wa ƙasashe mambobin ƙungiyar damar cin gajiyar rangwame kan biyan haraji yayin jigilar kayayyaki. An yi hakan ne don haɓaka kasuwancin yanki da kuma inganta haɗin kai.

Amma da wannan ficewar, wace asara ƙasashen Sahel suka yi, kuma wace irirn asara sauran ƙasashen yammacin Afirka za su yi?

Yadda lamarin zai shafi sauran ƙasashen Afrika ta Yamma

Daga nama zuwa albasa, farashin wasu kayayyakin abinci na iya tashin gwauron zabi.

Ƙasashen yankin Sahel sun yi suna wurin kiwon dabbobi da noman kayan lambu, wadanda suke samarwa ga sauran ƙasashen yammacin Afirka. Safarar abinci daga waɗannan ƙasashe, dole ne ta jawo ƙarin farashi idan ƙasashen uku ba su iya samun rangwamen haraji da suaran ƙasashen Ecowas ke samu ba.

Hakan na nufin ƴan Najeriya da Ghana da Senegal da sauran ƙasashen yammacin Afrika za su biya kuɗi fiye da yadda suka saba kan waɗannan kayayyakin abincin da ƙasashen na yankin sahel ke samarwa.

Safarar kayan ma zai ƙara tsada saboda sabbin abubuwan da ke tarnaki ga harkar kasuwanci duk da cewa akwai hanyoyin kasuwanci na yau da kullum na bayan fage tsakanin ƙasashen.

Shi ma bututun iskar gas na Trans-Saharan gas (TSGP) wani babban aiki ne da ke iya fuskantar barazana. Ana sa ran zai fara aiki a shekarar 2030.

TSGP aiki ne na haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Nijar, da Aljeriya. An tsara bututun mai tsawon kilomita 4,000 don jigilar iskar gas da ya kai yawan cubic biliyan 30 a shekara daga Najeriya ta hanyar Nijar zuwa Aljeriya, inda zai haɗe da sauran bututun da ake da su zuwa Turai.

Yana da nufin cike giɓin makamashi a nahiyar Afirka da kuma bunƙasa kasuwar iskar gas a nahiyar da duniya baki ɗaya, amma a halin yanzu aikin na fuskantar barazana sakamakon lalacewar dangantakar da ke tsakanin Nijar da Najeriya wanda zai janyo babbar asara.

Ƙasaitattun tashoshin jiragen ruwa na Togo da Ivory Coast ma za su shiga tsaka mai wuya.

An bayyana Togo a matsayin babbar cibiyar zirga-zirgar ababen hawa a yammacin Afirka saboda ingantaccen tsarinta na tashar jiragen ruwa da kayan aiki da ke taimakawa wurin hanzarta jigilar kaya.

Yayin da tashar jiragen ruwa ta Abidjan, wadda ake wa laƙabi da babbar tashar jiragen ruwa ta yammacin Afirka, ita ma babbar hanya ce ta jigilar kayayyaki zuwa yammaci da tsakiyar Afirka saboda ingantaccen tsarin layin dogo a ƙasar.

Waɗannan tashoshin jiragen ruwan biyu sun bunƙasa saboda ƙasashen Sahel da ba su da gaɓar teku sun dogara kansu wajen fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.

Ana iya watsi da sharuɗɗan kasuwanci da a yanzu ke kawo sauki idan ƙasashen na Sahel suka daina samun damar da zamansu a ƙungiyar Ecowas ke ba su.

Duk da yake hakan na iya nufin Togo da Ivory Coast za su rasa kasuwancin da ke tsakaninsu da waɗannan ƙasashen, ɓangarorin biyu za su yi asara idan ƙasashen na Sahel ma ba za su iya fitar da kaya zuwa ƙasashen waje ba.

Yadda zai shafi tafiye-tafiye

Ana iya samun cikas ta fannin ƴan Afirka ta Yamma da ke ziyartar ƙasashen na yankin Sahel. An ƙaddamar da fasfo ɗin Ecowas a watan Disamban 2000, wanda ke bai wa ƙasashen ƙungiyar su 15 damar tafiya ba tare da biza ba a cikin yankin, yana kuma aiki a matsayin takardun balaguro na ƙasa da ƙasa.

Ƴan ƙasashen mambobin Ecowas na da ƴancin zama a cikin wata ƙasa da ke mamba ta ƙungiyar har na tsawon wata uku, amma wannan na iya sauyawa ga waɗanda ke ziyartar ƙasashen da ba sa cikin ƙungiyar yankin.

Har ila yau, auratayya da aka saba yi musamman a yankunan kan iyaka, misali tsakanin Najeriya da Nijar da Ghana da Burkina Faso, da dai sauransu, wasu ƴan'uwa da ke da niyyar ziyartar ƴanuwa a ƙasashen Sahel na iya neman biza don shiga da kuma akasin haka.

Hakan na iya ƙara kawo cikas ga haɗewar yankin, da sauƙin gudanar da kasuwanci, da bunƙasar tattalin arziki, da kuma inganta yarjejeniyar ciniki cikin ƴanci ta nahiyar.

Asarar da Mali da Burkina faso da Nijar za su iya yi

Ƙasashen uku ba su da hanyar shiga teku, lamarin da ya sa suka dogara kan makwabtansu da ke kan gabar teku da suka haɗa da Togo da Benin da Ghana da kuma Najeriya wajen gudanar da kasuwancin ƙasa da ƙasa.

A cewar matattarar bayanan kasuwanci ta Ecowas (ECOTIS), a cikin 2022 kayayyakin da Mali ta fitar sun kai dala biliyan 3.91, ta kuma shigo da kayan da suka kai dala biliyan 6.45. Yayin da Burkina Faso ta fitar da kayan da suka kai dala biliyan 4.55, kuma ta shigo da waɗanda darajarsu ta kai dala biliyan 5.63. Nijar ta samu dalar Amurka miliyan 446.14 wajen fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen ƙetare, inda dala biliyan 3.79 suka shigo daga ƙasashen waje.

Don samun ci gaba da gudanar harkar kasuwanci, ƙasashen na Sahel za su buƙaci samun damar shiga tashoshin jiragen ruwa na wasu ƙasashen yammacin Afirka, wandanda za su nemi a biya su maƙudan kuɗade da sunan haraji - idan har suka daina kasancewa mambobin Ecowas.

A halin yanzu, ƙasar Benin ta toshe hanyar amfani da bututun mai da ya taso daga yankin Agadez da ke arewacin Nijar zuwa tashar jiragen ruwa ta Seme a Benin, lamarin da ya hana bututun mai tsawon kilomita 2,000 da ke samun goyon bayan China daga fitar da mai.

Amma duk da haka, Nijar na buƙatar ta yi amfani da ɗanyen man da take fitarwa zuwa ƙasashen waje domin biyan bashin dala miliyan 400 da ta karɓo daga China. Takun saƙa tsakanin Nijar da Benin ya biyo bayan matakin da Nijar ɗin ta ɗauka na ƙin sake buɗe iyakokinta bayan ɗage takunkumin da ƙungiyar Ecowas ta ƙaƙaba mata wanda ya sanya maƙwabtanta suka rufe kan iyakokinsu na sama da watanni shida.

A ranar Lahadin da ta gabata, shugaban hukumar ƙungiyar ta Ecowas, Omar Touray, ya yi gargadin cewa ficewa daga ƙungiyar na iya janyo wa ƙasashen na Sahel asarar kuɗaden da suka kai sama da dalar Amurka miliyan 500, wanda za su iya amfani da su wurin gudanar da ayyukan bunƙasa tattalin arziki wanda a halin yanzu za a iya dakatar da su ko kuma a rasa su baki ɗaya.

Shugabannin Ecowas sun kuma bayyana fargabar wargajewar yankin da kuma taɓarɓarewar tsaro. Yankin Sahel dai ya sha fama da hare-hare daga ƙungiyoyin masu da’awar jihadi wanda shugabannin yankin ke fargabar za su iya yaɗuwa ta kan iyakokin Sahel zuwa ƙasashen da ke maƙwabtaka da su tare da yin tasiri ga tsaron yankin.

An bayyana yankin Sahel a matsayin gida ga ƙungiyoyin ta'addanci saboda yawan alƙaluman ayyukan ta'addanci a duniya na shekarar 2022.

An bayyana yankin a matsayin sabuwar cibiyar ta'addanci, waɗanda aka ce "sun ƙara muni sakamakon yawan al'umma da rashin isasshen ruwa da abinci da sauyin yanayi da kuma gwamnatoci masu rauni".