Yadda manyan ƙasashe za su fafata a kwata-fainal na Gasar Kofin Afirka

Mane, Osimhen, Diaz, Amad

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Ahmad Bawage
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

An kammala wasannin zagayen ƴan 16 a gasar cin kofin Afirka da ake yi a Moroko.

Tawagogin ƙasashe sun yi fafatawa mai zafi, an nuna bajinta da kuma ƙwarewa.

Yanzu dai daga cikin ƴan 16, ƙasashe takwas sun fice daga gasar yayin da takwas suka tsallaka zuwa zagayen kwata-fainal.

Za a fara gwabzawa a zagayen na kwata-fainal ne ranar Juma'a, 9 ga watan Janairun 2026.

Mun yi duba kan ƙasashe da za su fafata da kuma abin da ake sa ran gani.

Mali da Senegal

Kofin Afirka

Asalin hoton, Getty Images

Tawagar ƙasar Mali za ta fafata ne da ƙasar Senegal wanda kuma wasa ne da ake hasashen za a kai ruwa rana, ganin irin ƙoƙari da duka ƙasashen suka yi kafin zuwa zagayen kwata-fainal.

Ƙasar Senegal dai dama tana cikin ƙasashe da ake ganin suna da damar lashe wannan gasa tun da farko.

Ƙasar tana da zaƙakuran ƴan wasa da duniya ta san da su kamar Sadio Mane da Kalidou Koulibaly da Idrissa Gueye da Nicolas Jackson da sauransu.

Ta samu damar zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Amurka, sannan tana matsayi na 18 a jadawalin Fifa na ƙasashen da suka iya taka leda.

A ɗaya gefe, Mali ma ba kanwar lasa ba ce ganin cewa ita ta fitar da Tunisiya daga gasar har ta samu damar zuwa kwata-fainal.

Tana da ƴan wasa masu hazaƙa irin su Sangaré da Bissouma da sauransu, sai dai ba ta samu damar zuwa gasar cin kofin duniya ba.

Kamaru da Moroko

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wannan ne wasan da ake ganin zai fi zafi a zagayen kwata-fainal saboda irin ƙwararrun ƴan wasa da ƙasashen biyu ke da su.

Moroko dai ita ce mai masaukin baƙi ta kuma je zagayen kwata-fainal ne bayan doke Tanzaniya da ci 1-0, kuma tana cikin ƙasashe biyar da aka yi hasashen za su iya lashe gasar ta bana.

Moroko ce ke kan gaba a jerin ƙasashen Afirka a jadawalin FIFA, ta taka rawar gani a fagen ƙwallon ƙafa a duniya a shekarar 2022, inda ta zama tawagar Afirka ta farko da ta buga wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya - kuma ta samu damar zuwa gasar da za a yi Amurka a watan Yuni.

Atlas Lions na ganin cewa wannan ne lokacin da ya fi dacewa ta sake lashe gasar ganin cewa a gida take wasa.

Tana da shahararrun ƴan wasa irinsu Brahim Diaz wanda shi ne ya fi zura ƙwallo a gasar da ake yi, Achraf Hakimi, Yousuf En-Nesri, Yassine Bounou da Mazraoui.

A ɗaya gefe, Kamaru wadda ta lashe gasar a 2021 a ƙasarta na fatan sake samun nasara.

Tana da shahararrun ƴan wasa irinsu Bryan Mbeumo da kuma Calos Beleba da sauransu.

Duk da kwazon ƙasar, ba ta samu damar zuwa gasar cin kofin duniya ba.

Abin da ya sa ake ganin wannan wasa zai ƙara yin zafi shi ne Kamaru ce ta fitar da Afirka ta Kudu daga gasar.

Algeria da Najeriya

Tun da farko dama Najeriya tana cikin jerin ƙasashe biyar da aka yi hasashen za su lashe gasar da ake yi a Moroko. Ta lashe dukkanin wasanninta a gasar har zuwa zagayen kwata-fainal.

Najeriya ta haskaka matuƙa tun fara gasar Afcon saboda irin salon wasa mai ƙayatarwa da take bugawa. Ta doke Mozambique 4-0 a zagayen ƴan 16.

Tawagar Super Eagles dai na da shahararrun ƴan wasa kamar su Victor Osimhen, Ademola Lookman, Alex Iwobi, Chukwueze, Bassey da kuma Ndidi.

Najeriya na matsayi na 38 a jerin jadawalin Fifa, sai dai ba ta samu damar zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi ba.

Aljeriya kuwa na son buɗe wani sabon tarihi na ƙoƙarin sake samun nasara. Ta yi ta nuna bajinta tun fara gasar saboda irin jajircewa da suke nunawa a wasannin da suka fafata.

Sun samu nasarar zuwa kwata-fainal ne sakamakon ƙoƙarin ƴan wasansu irin su Riyadh Mahrez wanda ya zura ƙwallo uku, tana kuma da matasan ƴan wasa kamar Chaïbi da Houssem Aouar da Rayan Aït Nouri, da Badredine Bouanani.

Ƙasar ta samu damar zuwa gasar kofin duniya kuma tana rukini ɗaya da Argentina a rukunin J.

Masu sharhi kan ƙwallon ƙafa na ganin za a kai ruwa rana a wannan wasa saboda kowace tawaga za ta jajirce don ganin ta kai zagayen daf da ƙarshe.

Masar da Ivory Coast

Wannan fafatawa ce da kowane masoyin ƙwallon ƙafa zai ƙagu don kallon yadda za ta kaya.

Idan aka kira sunan Masar da Ivory Coast dai kowa ya san irin tarihin da suke da shi a fagen ƙwallon ƙafa a nahiyar Afrika.

Tun da farko ma an yi hasashen ɗaya daga cikinsu na iya lashe gasar - Masar na neman lashe gasar karo na takwas a tarihi bayan kasancewarta wadda ta fi fice a ƙwallon ƙafar Afirka yayin da Ivory Coast kuma za ta yi fatan lashe Afcon karo na huɗu bayan lashe gasar a 2024 lokacin da ta karɓi baƙuncin gasar.

Ana ganin wannan ne dama ta ƙarshe da tauraron tawagar ƙasar Masar Mohamed Salah ke da shi na fatan lashe gasar karon farko - akwai kuma shahararrun ƴan wasa irin su Omar Marmoush da Mostafa Mohamed.

Ivory Coast ma na da shahararrun ƴan wasa irinsu Ahmad Diallo, Kessie da kuma Guessand.

Duka ƙasashen biyu sun samu damar zuwa gasar kofin duniya da za a yi a Amurka - Masar na matsayi na 35 a jadawalin Fifa yayin da Ivory Coast kuwa ke matsayi na 42.