Barca ta ce wa Depay ya nemi wata kungiyar, Chelsea za ta rasa Kounde

Asalin hoton, Getty Images
Mai horas da ‘yan wasan Barcelona Xavi ya fada wa dan wasan gaba na Netherlands Memphis Depay cewa ya san na yi bayan da kungiyar ta dauko Robert Lewandowski daga Munich, da kuma dan wasan Brazil dinnan Raphinha, mai shekara 25. (AS - in Spanish)
Sai dai ana cewa Ronaldo zai shaida wa Manchester United din cewar zai bar kungiyar, kuma ba zai karbi tayin da za su masa ba. (Sun)
Aniyar kungiyar Chelsea ta daukar dan wasan baya na Sevilla Jules Kounde na cikin hadarin rushewa ganin cewar Barcelona na kara kaimin ganin ta dauki dan wasan na Faransa mai shekara 23. (Guardian)
Idan har Chelsea ba ta samu nasarar dauko Kounde ba, to za ta fara tunanin sayo dan wasan Villarreal Pau Torres mai shekara 25, ko Milan Skriniar na Inter Milan da kuma matashin dan wasannan dan asalin Croatia Josko Gvardiol wanda yanzu ke wasa a RB Leipzig. (90 Min)
Chelsea ta yi tayin bayar da dan wasanta Timo Werner, ga RB Leipzig a kokarinta na shan gaban Paris St-Germain wajen sayen dan wasan baya na Faransa Nordi Mukiele mai shekaru 24, daga kungiyar, mai buga gasar Bundesliga. (Foot Mercato, via Metro)

Asalin hoton, Reuters
Dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo zai tafi Ingila domin tattaunawa da Manchester United kan makomarsa a kungiyar. (Athletic)
West Ham ta kammala cimma yarjejeniya da dan wasan gaba na Italiya Gianluca Scamacca, kuma ana sa ran za a duba lafiyarsa a yau Talata gabanin kammala dauko shi daga kungiyar Sassuolo. (Guardian)
AC Milan na tunanin kara kudi kan tayin da suka yi na sayen dan wasan tsakiya na Club Bruges Charles de Ketelaere, wanda ake alakantawa da kungiyar Leeds United, domin ganin ko cinikin nata zai fada. (Calciomercato - in Italian)
AC Milan kuwa na shinshinar dan wasan gefe na kungiyar Chelsea Hakim Ziyech kuma dan wasan mai shekara 29 dan asalin kasar Morocco na son komawa kungiyar wadda ke taka leda a gasar Serie A. (Calciomercato - in Italian)
Lyon ta ce a shirye take ta saurari tayin da za a yi wa dan wasanta mai shekara 24 dan asalin kasar Brazil Lucas Paqueta, wanda ake alakantawa da kungiyar Arsenal. (Metro)
Dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen, ya ce duk wani batu na sauya shekarsa jita-jita ce kawai domin kuwa shi yana jin dadin zamansa a Napoli. (Corriere dello Sport - in Italian)










