Kasuwar ƴan ƙwallo: Kante, Mane, Pogba, Lewandowski, Dembele, Calvert-Lewin

k

Asalin hoton, Getty Images

Sabon kocin Manchester United Erik ten Hag na farautar ɗan wasan Faransa da Chelsea mai buga tsakiya N'Golo Kante, ɗan shekara 31, yayin da yake shirin aiwatar da garambawul a Old Trafford. (Mirror)

Ɗan wasanLiverpool Sadio Mane, mai shekara 30, ya kasance mutumin da Bayern Munich ke hange idan ɗan wasanta Robert Lewandowski ya yi bankwana da ita a wannan kaka. (Bild - in German)

Lewandowski, mai shekara 33, ya amince ya koma Barcelona kan yarjejeniyar shekara uku. (Times - subscription required)

Dan wasan Barcelona mai buga gaba a Faransa Ousmane Dembele mai shekara 24 na cikin jerin mutanen da Bayern Munich ke hari. (Sky Sports)

Juventus ta shirya saye ɗan wasan Manchester United mai buga tsakiya Paul Pogba, dan shekara 29. A ƙarshen wannan kakar kwantiraginsa ke karewa. (Goal)

Newcastle ta yi tattaunawar wucin gadi da ɗan wasan Everton Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 25, sai dai ɗan wasan na Ingila ya fi son ya je Arsenal. (Football Insider)

Arsenal ta amince ta kashe kusan euro miliyan 25 (£21.2m) wajen siyo ɗan wasan Bologna Aaron Hickey. (Calciomercato - in Italian)

Gunners na gaba da cimma yarjejeniyar euro miliyan 3.5 (£3m) da ɗan wasan Barzil mai shekara 19 Marquinhos daga Sao Paulo. (ESPN)

Arsenal ta kuma shirya sayo ɗan wasan Manchester City Gabriel Jesus, mai shekara 25. City na neman tsakanin euro miliyan 50 zuwa 60m (£42.4m and £50.0m) kan ɗan wasan na Brazil. (Fabrizio Romano)

Manchester City za ta yi kokarin sake sayen wasu yan wasa, bayan ɗan wasan Borussia Dortmund da Norway da ta saye wato Erling Haaland. (Mail)

Aston Villa ta fara cinikin ɗan wasan tsakiyar Najeriya Joe Aribo mai shekara 25, wanda ke taka leda a tsohuwar kungiyar kocinsa Steven Gerrard wato Rangers. (Sun)

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya tabbatar da ci gaba da zaman ɗan wasan gaban Belgium Eden Hazard mai shekara 31 a kungiyar a sabuwar kaka. (Goal)

Fulham ta gamsu da yarjejeniyar dindindin kan ɗan wasan Wales Neco Williams, wanda ya je zaman aro a ƙungiyar daga Liverpool a watan Janairu. (Football Insider)