Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jirgi maras matuƙi ya kashe sojin Isra'ila huɗu mutum 60 sun ji raunuka
An hallaka soja huɗu kuma ƙarin wasu mutane kimanin 60 sun ji raunuka a wani harin jirgi maras matuƙi da aka kai wa wani sansanin sojoji da ke arewacin Isra'ila, kamar yadda Rundunar Dakarun Tsaron Isra'ila ta bayyana.
Rundunar IDF ta ƙara da cewa sojoji guda bakwai sun ji munanan raunuka a harin wanda aka kai kan wani sansani da ke "kusa da Binyamina" - wani gari mai nisan mil 20 a kudu da Haifa.
Ƙungiyar Hezbollah ta ce ita ce ta kai harin, wanda ta ce ta ƙaddamar da shi ne a kan wani sansanin horar da sojojin Rundunar Golani ta Dakarun Tsaron Isra'ila a yankin, wadda aka girke a tsakanin Tel Aviv da Haifa.
Ofishin yaɗa labaran ƙungiyar mai gwagwarmaya da makamai ya ce harin martani ne ga farmakin da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon da kuma Beirut ranar Alhamis.
Ƙungiyar ta ce ta kai harin ne kan sansanin wanda ke kudancin Isra'ila ta hanyar amfani da wani "cincirindon jirage marasa matuƙa".
Hukumar kula da motocin ɗaukar marasa lafiya ta Isra'ila, Magen David Adom (MDA), ta ce mutum 61 ne suka ji raunuka a harin - uku daga cikinsu ƙazamin rauni. Ta ƙara da cewa an kai 37 a cikinsu zuwa asibitocin yankin takwas ta hanyar amfani da motoci da jiragen helikwafta.
A cikin wata sanarwa kafin rundunar sojojin Isra'ila ta tabbatar da mace-macen, hukumar MDA ta ce ban da uku da ke cikin yanayi mai tsanani, akwai wasu 18 da suka ji matsakaitan raunuka, sai 31 da suka ji ƙananan raunuka da kuma mutum tara da suke "cikin kaɗuwa".
Babu masaniya ƙarara kan dalilin da ya janyo saɓani a alƙaluman mutanen da suka ji raunuka masu tsanani a tsakanin hukumar MDA da kuma rundunar sojojin Isra'ila.
Dokokin tace labarai a Isra'ila da farko sun hana kafofin yaɗa labarai ba da rahotanni na a ina ne ko kuma abin da aka kai wa harin, kafin rundunar sojin Isra'ila ta IDF ta tabbatar da cewa sansanin Binyamina ne.
Wasu kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ba da rahoton cewa sansanin ya fuskanci hari ne daga wani jirgi maras matuƙi ƙirar ƴan dagaji da aka harba daga Lebanon - wato makami ne da ba a ƙera da ingantacciyar ƙwarewa ba, lamarin da ya sa ga alama bai fargar da jiniyar gargaɗi da wurwuri ba.
A duk tsawon yammacin Lahadi, labaran talbijin da bayanan shafukan sada zumunta da rahotannin kafofin intanet sun yi ta nuna ababen hawan ɗaukar marasa lafiya ciki har da jiragen helikwafta lokacin da suke kwasar mutanen da suka jikkata zuwa asibitocin da ke faɗin arewacin Isra'ila.
Da yawan waɗanda suka jikkata an kai su Asibitin Hillel Yaffe Medical Centre a Hadera - yayin da wasu kuma aka garzaya da su zuwa asibitocin da ke Tel Hashomer da Haifa da Afula da kuma Netanya.
Har yanzu akwai ƙarancin bayanai amma ga alama mutane da yawan da suka ji raunuka sun taru ne a wani kanti a lokacin, kuma harin ya shammaci kowa.
Hotunan da ake ta yaɗawa a shafukan sada zumunta ga alama na nuna wani zauren taro babu kowa a ciki da kuma ɓurmammen rufin sama.