Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin ko akwai ƙabilanci a korar ma'aikatan CBN fiye da 100?
"Gaskiya babu maganar kabilanci ko addinanci ko ma bangaranci. Duk wanda aka kora ko dan arewa ko kudanci, Musulmi ko Kirista to yana da laifi. Ka san an tafka kurakurai a babban bankin Najeriya. Mu dai a yanzu ba mu ga alamar haka ba. Abin da muke gani shi ne shirin kawo gyara a babban bankin" In ji wani ma'aikacin bankin da ba ya son BBC ta ambaci sunansa.
Tun bayan da bayanai suka fito daga babban bankin Najeriya cewa ya kori ma'aikata 117, masu manyan matsayi, 'yan Najeriya musamman a kafafen sada zumunta suke ta tofa albarkacin bakinsu.
Yayin da wasu ke alakanta abin da kabilanci ko bangaranci da dama na nuna cewa addinanci ne ya yi tasiri.
Hakan ne ya sa BBC ta tambayi wasu ma'aikatan babban bankin wadanda 'yan arewacin kasar ne da ake ganin an dauki matakin domin su.
Binciken BBC Hausa
BBC ta gano cewa CBN na gudanar da bincike ne ta ƙarƙashin ƙasa tare da ɗaukar mataki kan dukkan waɗanda aka kama da hannu kan zargin da ake musu na aikata ba daidai ba.
Ba dai lokaci guda bankin ya kori ma'aikatan nasa ba da a yanzu suka haura 100.
Amma da korar mutum 50 da ya yi na baya-bayan nan, adadin kamar yadda bayanai ke cewa ya kai 117.
Mutanen da BBC ta tattauna da su daga CBN din sun bayyana mata cewa korar ta shafi wasu manyan sassa uku ne na bankin da suka hada da ɓangaren ba da tallafi wanda a turance ake cewa (Intervention) da mai kula da kwantaragi ko kuma procurement a turance da kuma mai kula da harkar lafiya wato medical department.
Majiyoyin BBC sun tabbatar da cewa "an tafka badakala a babban banki a shekarun da suka gabata."
A ƙarƙashin sashen bayar da tallafi ne dai CBN ya gudanar da shirye-shirye irin na ba da rance ga manoma na Anchor Borrowers da bayar da rance na Korona dai sauransu da aka gudanar lokacin gwamnatin Buhari.
A baya-bayan nan ne babban bankin ya sanar da cewa har yanzu kudade fiye da biliyan 500 sun makale a hannun jama'a ba su koma wa bankin ba.
Waɗanne ma'aikatan aka kora?
CBN ya yi wannan kora ne cikin kwanakin da ba su gaza 20 ba.
Ma'aikatan na CBN da BBC ta tattauna da su sun shaida mata cewa "adanda abin ya shafa ya zuwa yanzu sun hada da daraktoci da mataimakansu da manyan manajoji da kuma masu biye musu da wasu daga cikin ƙananan ma’aikata".
Majiyar ta kara da cewa "gaskiya yadda ake yin abin ya cancanci yabo kasancewar bankin ya kudiri aniyar yin bincike domin tono duk wata badakala da aka yi musamman mai alaka da ma'aikata.
An hada kai da ma'aikata an yi abubuwa marasa dadin ji. Saboda haka bisa tsarin da'ar ma'aikata, dole ne a hukunta su. Kuma haka bankin yake yi ba tare da nuna banbancin kabila ko addini ko kuma bangaranci ba." In ji majiyar BBC.
Dangane kuma da yadda binciken ke shafar wadanda ba su ji ba ba su gani ba, majiyar ta ce " e lallai akwai 'yan tsiraru wadanda abin ya shafe su ba tare da su suka aikata laifin ba illa dai wani ya aikata ko dai da sunansu ko kuma a karkashinsu. Muna sa ran nan gaba bankin zai tsananta bincike wajen tantance wadanda kashin kaji aka shafa musu". In ji ma'aikacin CBN.
Ya kara da cewa "misali akwai mutanen da aka kora saboda samun su da laifin sayar da sabbin takardun kudi a nan Abuja lokacin da kudin kasar suka yi karanci sakamakon tsarin sauyin kudin kasar."
Ma'aikatan CBN na zaman zulumi
Matakin na babban bankin Najeriya na korar ma'aikata dai ya jefa ma’aikatan CBN din cikin zaman zulumi da ɗarɗar saboda rashin tabbas da sanin abin da zai iya faruwa gobe.
Da yawan ma'aikatan CBN sun shiga rudani, musamman wadanda a baya suka tabbatar sun taɓa shiga wata hada-hadar da ta saba ƙa'idar bankin.
Wata majiya ta shaida wa BBC cewa nan gaba bincike zai iya kaiwa ga bangaren masu lura da hada-hadar kuɗaɗen ƙetare da kuma wadanda suka tafiyar da shirin sauya fasalin naira da gwamnatin Buhari ta yi.
"Ai yanzu aka fara wannan al'amari. Ko rabi ma ba a yi ba kuma hakan ne ya jefa ma'aikatan bankin cikin zaman zulimi da rashin tabbas musamman dai wanda ya san yana da kashi a gindinsa. Kai har kowa da kowa ma tunda wani zai iya shafa maka kashin kaji. To amma dai muna fatan a nan gaba bankin zai yi bincike a tsanake." In ji majiyar ta BBC.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefele ke fuskantar shari'a bisa tuhume-tuhumen rashawa da cin hanci.
Shugaban na CBN, Dr Olayemi Cardoso ya lashi takobin tabbatar da an kawo sauye-sauye ga babban bankin na Najeriya da suka sha banban da na tsohon shugaban bankin, Chief Godwin Emefele.
Masana dai da masu sharhi kan al'amura sun karkata hankalinsu kan banban bankin domin ganin al'amura ke wakana.