Buhari ya shure masu nuna damuwar cewa ba a ganin sa a kamfe ɗin Tinubu

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce a shirye yake ya taya ƴan takarar jam'iyyarsa ta APC yaƙin neman zaɓe da cikakken ƙarfi da zuciyarsa gabanin babban zaɓen ƙasar na 2023.

Shugaban ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Mallam Garba Shehu ya fitar don musanta raɗe-raɗin da wasu ke yaɗawa cewa ba ya halartar gangamin da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Ahmed Tinubu yake yi a jihohin ƙasar.

Tun bayan yaƙin neman zaɓen da Tinubu ya ƙaddamar ne a Jos, babban birnin Filato cikin watan Nuwamba, ba a sake ganin ƙeyar Shugaba Buhari a sauran gangamin da APC ta yi ba.

Ɗan takarar shugaba ƙasar ya ziyarci jihohi da dama a kamar Kaduna da Imo da Delta da Kuros Riba da kuma Neja, a yaƙin neman zaɓe da yake ci gaba da yi.

Zuwa yanzu, ba a taɓa jin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya yi ƙorafi a bainar jama'a game da rashin halartar Shugaba Buhari tarukansa na yaƙin neman zaɓe ba.

Amma batun ya janyo ce-ce-ku-ce da gutsuri tsoma inda ɓangaren 'yan adawa da wasu ƴan ƙasar ke zargin ko Shugaba Buhari a yanzu ya raba gari da Tinubu.

Idan za a iya tunawa a bikin ƙaddamar da manufofin Tinubu ne Shugaba Buhari ya bayyana cewa zai kasance kan gaba a yaƙin neman zaɓensa.

Sai dai a sanarwar ta baya-bayan nan, Shugaba Buhari ya ce yin ƙarin haske kan dalilan da suka sa ba ya halartar tarukan ya zama wajibi domin kawo ƙarshen jita-jitar da ake ta yaɗawa.

Bayanai na nuna cewa a lokacin da jam'iyyar ke gudanar da gangaminta a sassan ƙasar, Shugaba Buhari yana halartar taruka a ciki da wajen Najeriya ne.

Kwanan ne ma Buhari ya dawo daga Amurka bayan ya halarci wani babban taro a Amurka wanda Shugaba Joe Biden ya gayyaci shugabannin Afirka.

"Da yake yi wa ƴan Najeriya da ke Washington jawabi a ziyarar da ya kai Amurka kwanan nan, Shugaba Buhari ya jaddada abin da ya sha faɗa cewa a shirye yake ya taya jam'iyyarsa kamfe domin ta yi nasara a babban zaɓen ƙasar na baɗi," in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa "Yaƙin neman zaɓen da APC ke yi zuwa yanzu shi ne ya fi tara jama'a da karsashi inda ake yin gangami babu kama hannun yaro saɓanin na jam'iyyun adawa da suke faman faɗi-tashi,"

Shugaba Buhari dai ya bayyana kyakkyawan fatan cewa APC za ta lashe zaɓe a dukkan matakai cikin adalci da gaskiya a 2023.