Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa Hisbah ke kama masu 'sheƙe-aya' a Kano - Daurawa
Muhawara da cacar baki sun kaure a ciki da wajen Kano, kan abin da wasu ke cewa gagarumin kame ne kan masu yawon ta-zubar da jami'an Hizbah suka ƙaddamar.
Hotuna da bidiyo sun cika shafukan sada zumunta na 'yan hizba cikin duhun maryace, suna daƙume 'yan mata, da ma samari a wuraren yawon dare.
Ba sabon abu ba ne kamen mutane a wuraren da ake zargi ana aikata karuwanci ga hukumar Hizbah ta Kano, sai dai ga alama, wannan ya kama hanyar shiga jerin ayyukan hizbah da suka fi tayar da ƙura da janyo ka-ce-na-ce.
Wasu dai na kallon samamen a matsayin wani muhimmin aikin da aka kafa Hukumar domin aiwatar da shi, wato hana aikata baɗala, kamar yawon dare da masha'a da sheƙe aya, kai har ma da karuwanci a birnin Kano.
Wasu kuwa na ganin duk da yake, 'yan hizbar 'aikin Allah' suke yi, amma zakewa da kokawa ko ruƙunƙumar 'yan matan da ake ƙoƙarin kamawa da karya ƙofar gida ko ɗaki, abubuwa ne da suka wuce gona da iri.
Yayin da wasu ma ke fitowa gaba-gaɗi suna zargin Hizba da keta haƙƙin ɗan'adam.
Sai dai masu kare dirar mikiyar Hizbah na cewa kushe hukumar a kan wannan sabon yunƙuri, tamkar nuna goyon baya ne da kuma rufe ido ga iskance-iskance da lalacewar da ke ƙaruwa a kan tituna.
Samamen kama 'yan kwalta - Hizba
Tun daga ranar Talata da hukumar ta kaddamar da samame, rahotanni sun ce jami'an Hizba sun kama gomman 'yan mata da maza a unguwannin Kabuga da Dambare da Ahmadu Bello Way da titin Murtala Muhammad da kuma Nassarawa.
A yayin zantawa da gidan rediyon Freedom game da wannan samame da suke yi, Mujaheed Aminuddeen Abubakar, kwamandan ayyuka na hukumar hizba ya ce sun kaddamar da abin da ya kira operation kau da badala ne don magance matsalar masu sheke ayar da ake kira 'yan kwalta a Kano.
Ya kara da cewa: "Ka je kana inda bai kamata ka je ba. Lokacin da bai kamata ka je ba. Ta inda bai kamata ka je ba, sai mu dauko ka a hizbance. Mu tantance ka. Mu mika wa mai girma mai shari'a ya yi maka nasiha wacce ta dace da kai".
Ya ce burinsu shi ne masu yawon ta-zubar da ya ce suke kamowa su dawo kan hanya.
Sai dai wasu cikin 'yan matan da hizba ta kama kamar yadda Freedom Radio ta ruwaito sun yi zargin cewa 'yan hizba sun kama su ne a wani wuri daban da inda ake zargin gidajen yawon sheke aya ne.
Wasu ma sun ce suna tsaka da tafiya ne kawai aka kama su.
Wani bidiyo da ya karade Facebook ranar Alhamis, an jiyo muryar wata matashiya tana ihun neman a kai mata dauki, lokacin da wasu ke kokarin balle kofar da take ciki.
An kuma ji tankiya ta barke bayan shigowar masu kokawa da kofar. Tun farko ta yi zargin cewa 'yan hizba ne suka je don kama su.
Me hukumar Hisbah ta ce?
A nata ɓangaren hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce nan gaba za ta gurfanar da mutanen da aka kama a lokacin samamen nata.
Shugaban hukumar, Sheikh Aminu Daurawa ya ce maƙasudin yin kamen shi ne jihar Kano na daga cikin jihohin da aka ƙaddamar da aiki da shari'ar musulunci, kuma an haramta wanzuwar gidajen barasa da na mata masu zaman kansu.
Dalilai uku na samamen Hisbah
- Kwararowar mata masu zaman kansu daga jihar Borno bayan umurnin gwamna Babagana Umara Zulum na rufe gidajen karuwai.
- Kwararowar masu aikata baɗala daga jihar Gombe bayan da gwamnatin jihar ta bayar da umurnin rufe gidajen Gala da na mata masu zaman banza.
- Shigar ƴammata cikin harkokin baɗala sanadiyyar talauci.
Sheikh Aminu Daurawa ya ce sun fara kai samamen ne bayan ƙorafe-ƙorafe daga mutane masu maƙwaftaka da otal-otal da kuma wasu gidajen masha'a.
Ya ce ƙorafin da suka samu shi ne akan riƙa yin zirga-zirga da ƴanmata a irin waɗannan gine-gine tsawon dare.
Matakan da muke bi wajen kai samame - Daurawa
Shugaban hukumar ta Hisbah ya ce akwai matakai uku da jami'anta ke bi kafin kai samame.
- Na ɗaya shi ne samun ƙorafi daga al'umma
- Tura masu bincike na ƙarƙashin ƙasa
- Sanar da rundunar ƴan sanda lokacin kai samame
Shugaban na Hisbah a jihar Kano ya kuma ce dalilin da ya sa suke kai samamen a cikin dare shi ne domin kama masu laifin a lokacin da suke aikata laifi.
Me mutane ke cewa kan kamen?
Mutane da dama kamar Rabi'u Ahmed Kofar Mazugal a shafin sada zumunta na Facebook sun yabawa aikin Hizba. Yana cewa "Ina amfani da wannan damar wajen yaba wa hukumar Hisba ta Kano a kan matakin da ta dauka na kawar da harkar karuwanci da zaman Otel ba bisa ƙa'ida ba".
"Wannan aiki da suke yi kamata ya yi duk wani Musulmi ya goya musu baya domin suna hana ɓarna ne", in ji shi.
"Mu daina sanya siyasa ko son zuciya a komai, ni da kai, dukkanmu ba za mu so a ce yau ga 'ya'yanmu ko kannenmu suna karuwanci ba.......", in ji Rabiu.
Shi kuma Ayuba Abudllahi Majidadi ya ma yi zargin cewa watakila masu ganin baiken hukumar hizbah akwai wani nau'in laifi da suke aikatawa, don haka ba sa farin ciki da kawar da ayyukan rashin tarbiyya.
A yayin da wasu ke yaba wa hukumar Hisbar bisa wannan kame, wasu a gefe guda kuma na ganin rashin dacewar sigar kamen.
Mafi yawan masu sukar hukumar na cewa yadda jami'an hizba suke bin mata da kokawa a wasu lokutan domin kama su bai dace ba sam.
Activist-Isma'eel S Jauro cewa ya yi abin da hukumar ta yi ya saɓa wa dokar Musulunci da kuma dokar 'yancin ɗan'adam.
A cewarsa wasu da aka kama sun ce har cikin ɗakunan gidajensu aka bi su aka kama, wasu kuma a kan hanyarsu ta zuwa sayen magani.
"Wasu kawai suna cikin tafiya ma aka tsayar da su aka kama su, wata tsohuwa ta ce tana kwance ma cikin gidanta, a ɗakinta aka banko ƙofar ɗaki aka ce ta tashi a tafi da ita, in ba haka ba za a lakaɗa mata duka", kamar yadda ya rubuta.
"Wata kuma tana tafiya za ta je kantin magani, don yi mata allura suka kama ta, wallahi kana ganin ta, ka ga maras lafiya", in ji shi.
"Wannan cin zarafi da take haƙƙi, abin damuwa ne wallahi. Kuma ƙarin cin zarafin ma, sai su yi baja-kolinsu ga ƴan jarida su yi ta watsa bidiyonsu".
"Ba ma a dokar kare haƙƙin ɗan'adam ba, ko a Musuluncin da Hisba ke iƙirarin yi wa aiki, babu inda aka ce idan kana zargin mutum da aikata laifi, ba ka zurfafa bincike don gano laifinsa ba, kuma ka zo ka baza a duniya cewar ya aikata laifin".
"Ko mutum ya aikata laifin Musulunci bai ce a baza a duniya ba balle ma zargi ake ba a tabbatar ba", in ji Activist-Isma'eel S Jauro.
Shi ma Ali Jamilu cewa ya yi holin da Hisba ke yi wa mutanen da ta kama, ya keta dokar Musulunci, kuma dokar da ta kafa Hisba ma, ba ta ce a yi haka ba.
Ya ce "samamen da Hisba ta yi, da kame da bulala har da holin mutanen ga ƴan jarida dai, tozarta ɗan'adam ne wanda hakan ya saɓa wa Musulunci da karantarwar Annabi (SAWS).
Kuma babu inda dokar da ta ƙirƙiri hukumar ta ba su damar yin hakan".
"Bai kamata malamin da ya yi shuhura wajen ba da fatawa da tarbiyya irin Sheikh Aminu Daurawa ya bari, ko ya ba da umarnin cin zarafi da keta mutunci da tozarta ɗan'adam da sunan kawo gyara ba".
Ya ce "kamata ya yi kwamishinan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin jihar Kano ya ja hankalin hukumar Hisbar, don su san matsayinsu a dokar da ta ƙirƙiri hukumar".
"Muna ba da shawara a riƙa aiki da lura da bin doka da oda, ba wuce gona da iri ba, wanda hakan ya saɓa dokokin musuluncin da ake iƙirarin ana yi don shi, haka nan ya saɓawa dokokin ƙasa da kundin tsarin mulkin Najeriya", in ji Ali Jamilu.
Wasu kuwa shawara suka bai wa hukumar kan hanyar da ya kamata su riƙa bidon kama masu laifin, amma ba wannan salo na kama mutanen da ake zargi da aikata laifi da kokawa ba.
Hauwa Farouk Ibrahim shawara ta bai wa Hisba cea idan za ta kai samame irin wannan to ta riƙa tafiya da jami'an mata, domin dai ƙwarya ta bi ƙwarya.
Ta ce "shawarata ga Hisba, idan za a je irin wannan samame, a dinga tafiya da mata don Allah, don na ga ani ɗan hisba yana daga ata ƙatuwa, yana wullawa a mota, wannan ba daidai ba ne gaskiya".
Shi kuwa Abdulhamid Nasir cewa ya yi batun kamen da Hisba ta yi, ya yi matuƙar razana shi.
Musamman yadda iyaye ke sakaci wajen sanya idanu a kan 'ya'yansu.
"Maganar gaskiya na saurari hirar da aka yi da yaran da hukumar hisba ta kama a samamensu na jiya"
“Wato gaskiya na ƙara tsorata da lamarin tura ‘ya’ya mata karatu wasu jihohin ba tare da sanya musu masu saka ido a kansu ba musamman kwanan hostel da wasu iyayen suke kai ‘ya’yansu karatu wasu jihohin", in ji shi.