Wasu ƴan Kannywood da suka ƙware a fannonin masana'antar daban-daban

Lokacin karatu: Minti 5

Kannywood babbar masana'anta ce mai faɗin gaske da ke ɗauke da ɓangarori daban-daban da suka shafi ayyukan masana'antar.

Akwai ma'aikatan masana'antar da suka ƙware a fannonin da suke aiki, kama daga ɗaukar hoto da waƙa da shirya film da ma fitowa a matsayin jarumai.

To amma duk da irin faɗin da masana'antar shirya fina-finan ta arewacin Najeriya ke da shi akwai wasu ƴan Kannywood ɗin da suka yi fice ko zarra ɓangarori daban-daban.

Su waɗannan jarumai ba fanni ɗaya kawai suka ƙware ba, sun yi zarra a fannoni daban-daban na masana'antar.

Cikin wannan mukala mun duba biyar daga cikin ƴan Kannywood da Allah ya bai wa basirar yin fice a fannonin masana'antar daban-daban.

Ali Nuhu

Da alama laƙabin sarki da ake yi wa Ali Nuhu a Kannywood ya yi tasiri a wajensa na kasancewa jigo da ya yi fice a fannonin masana'antar daban-daban.

Ali Nuhu - wanda ya kasance cikin mutanen farko-farko a masana'antar - ya samu ƙwarewa a fannonin masana'antar daban-daban.

Shugaban hukumar tace fina-finai ta Najeriya ya fara ne a matsayin jarumi, inda ya fito a manyan tsoffin fina-finai kamar su Sangaya da Mujadala da Fil'azal da Gambiza da sauransu.

A zamanin yanzu kuma jarumin ya fito a manyan fina-finai masu dogon zango da zjuka haɗa da alaƙa da Gidan Sarauta da Izzar So da sauransu.

Bayan ya jima yana fitowa a matsayin jarumi, Ali Nuhu ya koma bayar da umarni, wato Darakta, inda ya jagoranci bayar da umarnin manyan fina-finai a masana'antar da suka haɗa da Gambiza da Dijangala da Sai Wata Rana da kuma yanzu da yake jagorantar film ɗin Alaƙa mai dogon zango da ma Gidan Sarauta.

Yakubu Mohammed

Yakubu Mohammed ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ƴan Kannywood da suka ƙware a fannonin masana'antar daban-daban.

Tun da fari Yakubu ya fara ne da waƙoƙi a masana'antar, Inda ya zama ɗaya daga cikin fitattun mawakan masana'antar a shekarun 2000.

Waƙoƙinsa da suka yi fice a lokacin sun haɗa da Waƙar Jarumai da Hanta Da Jini da Adamsy Yaro da Zubar Gado da Gara da Jarida da sauransu.

Yana tsaka da waƙa a masana'antar sai kuma ya koma bayar da umarni, inda nan ma sai da ya yi zarra tsakanin takwarorinsa masu bayar da umarni a masana'antar.

Fina-finan da ya bayar da umarni sun haɗa da Adamsy da Hawayena da Haƙƙin Miji da Ƙawayen Amarya da kuma na irinsu Allura Cikin Ruwa da Gidan Danja.

Haka kuma akubu Mohammed bai tsaya nan ba, sai kuma kwatsam ya koma fitowa a matsayin jarumin film, inda a yanzu yake jan zarensa a masana'antar.

Yanzu haka jarumin na fitowa a cikin manyan fina-finan masu dogon zango da suka haɗa da Allura Cikin Ruwa da Manyan Mata da Garwashi da Gidan Sarauta da sauransu.

Sani Danja

Sani Danja ya kasance aboki kuma makusanci ga Yakubu Mohammed, inda ake yi musu kallon tagwaye a masana'antar.

Kamar dai abokin nasa shi ma Danja ya kasnace cikin ƴan Kannywood da ba a fanni ɗaya kawai suka ƙware ba.

Da fari ya fara ne a matsayin jarumi, inda ya fito a manyan fina-finai da suka haɗa da Daham da Adamsy da Jarumai da sauransu, a yanzu kuma Allura Cikin Ruwa da Gidan Danja da sauransu.

Bayan shafe tsawon lokaci Danja na fitowa a matsayin jarumin Film, sai kawai aka ji shi tsundum a fagen waƙa duk dai a masana'antar.

Waƙoƙin da ya rera suka yi fice sun hala da Jamila ta Iya Ɗaura Zani, da Mai babbar Riga da Adamsy da sauransu.

Baya ga waƙoƙi Sani Danja ya kuma shiga fagen shirya fina-finai , wato furodusa, inda ya shirya fina-finai masu yawa kamar Allura Cikin Ruwa da Gidan Danja da sauransu.

Adam Zango

Adam A Zango da ake yi wa laƙabi da Adamu Usher na daga cikin jarumai masu basira da fasahar ƙwarewa a fannonin masana'antar daban-daban.

Da fari ya fara a matsyin jarumi a masana'atar iunda ya ja manyan fina-finan da suka yi fice a masana'antar, da suka haɗa da Raga da Sai Wata Rana da Ga Duhu Ga Haske da Walijam da Ɗan Almajiri da sauransu.

Daga nan jarumin sai ya koma fagen waƙa duk dai a masana'antar inda ya samu karɓuwa a nan ma, ya kuma rera waƙoƙin da suka yi fice kamar su Sawa da Maigari da Baba ya bani Zainab, da mai Atamfa da sauransu.

Baya ga waƙoƙi Adam Zango ya kasance ɗaya daga cikin masu shirya fina-finai, wato furodusa a masana'antar.

Fina-finan da jarumin ya shirya sun haɗa da Basaja da Gwaska da sauransu.

Rahma Sadau

Rahma Sadau ta kasance ɗaya daga cikin mata da ke taka mabambantan rawa a masana'antar Kannywood.

Kamar wasu da dama cikin jerin nan Rahma ta fara ne a matsayin jaruma, inda ta fito a manyan fina-finai da suka haɗa da Nadiya da Almajiri da Aljannar Duniya da Ba Tabbas da sauransu.

Baya da fina-fginan Hausa jaruman ta fito a wasu fina-fainan kudancin ƙasar da ma na Indiya saboda ƙwarewarta.

Baya ga kasancewarta jaruma, Rahma Sadau ta kasance cikin masu shirya fina-finan Hausa.

Ta samu nasarar shirya fina-finai kamar Rariya da ya samu karɓuwa tsakanin masu kallo.

Haka ma ita ce ta shirya fina-finan Matar Aure da Amaryar Lalle masu dogon zango a baya-bayan nan.

Hannatu Bashir

Ta kasance ɗaya daga cikin jaruman da ake yi wa kallon kallabi tsakanin rawuna a masana'antar.

Domin kuwa ita ma bayan kasancewarta jaruma ta kasance cikin jerin masu shirya fina-finai a masana'antar, inda ta jagoranci shirya manyan fian-finai.

Kamar dai sauran ta fara ne a matsayin jaruma, inda ya fito a fina-finai kamar Kotun Ibro da Sarauniya da Shahida da Mutum da Aljan da Kukan Kurciya da sauransu.

Bayan jimawa tana fitowa a fina-finai jarumar ta koma fagen masu shirya fina-finai, wato Furodusa inda ta samu nasarar shirya manyan fina-finai da suka haɗa da Shaheeda da Ashe Za mu ga Juna da sauransu.