Amurka za ta tura baƙin haure Uganda da Honduras

Bakin haure na sauka daga jirgin sama

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Amurka ta cimma yarjejeniyar fitar da bakin haure tsakaninta da gwamnatocin Uganda da Honduras a matakin da take dauka na magance matsalar shigar bakin haure kasarta.

Takardun bayanan hakan da kafar yada labarai ta CBS ta samu sun nuna cewa matakin wani bangare ne na gwamnatin Shugaba Trump na fadada neman wasu kasashen waje da a shirye suke su karbi bakin haure da ba 'yan kasarsu ba.

A gagarumin matakin da ta dauka na korar bakin haure wanda ba a taba ganin irinsa ba a kasar gwamnatin Shugaba Donald Trump na ta neman cimma yarjejeniya da wasu kasashe a nahiyoyi da dama – domin kasashen su karbi bakin hauren da Amurkar ke fitarwa daga cikinta.

Zuwa yanzu wajen kasashe goma sha biyu (12) ne suka yarda su karbi bakin haure 'yan wasu kasashe, wadanda Amurkar ta fitar daga cikinta.

Wasu daga cikin irin wadannan kasashen da suka cimma yarjejeniyar karbar da Amurka – kamar Uganda ana ganin suna da lam'a ko sun yi kaurin suna a kan zargin take hakkin dan'Adam.

Ita dai Uganda da ke yankin gabashin Afirka ta amince ta karbi daruruwan bakin hauren 'yan kasashen Afirka da kuma 'yan Asiya, wadanda suka nemi mafaka a kan iyakar Amurkar da Mexico.

Haka kuma takardun da kafar yada labarai ta CBS ta samu na yarjejeniyar sun nuna cewa kasar Honduras da ke Latin Amurka, ta amince ta karbi bakin hauren da Amurkar ta fitar 'yan kasashen da su ma masu amfani da harshen Sifaniyanci ne.

Masu rajin kare hakkin dan'Adam na suka sosai ga manufar gwamnatin Trump ta tura bakin hauren zuwa wasu kasashe, da cewa hakan na jefa mutanen cikin hadarin tura kasashen da za a iya cutar da su.

Ita kuwa gwamnatin na cewa wannan yarjejeniya na da muhimmanci ga gagarumin shirinta na fitar da bakin haure, kasancewar akwai bakin da ba za a iya mayar da su kasashensu ba cikin sauki saboda rashin kyakkyawar dangantaka tsakanin Amurkar da kasashen ko kuma wasu dalilai.