Hanya uku da Trump ka iya kawo jan ƙafa a tuhumar ɓoye sirrin ƙasa

Asalin hoton, EPA
Tsoho shugaban Amurka Donald Trump ya musanta zargin da ake masa na aikata ba daidai ba inda ake tuhumarsa da laifin boye wasu muhimman bayanai bayan da ya bar fadar gwamnatin White House.
Ana tuhumarsa da laifuka 37, da suka hada da kawo cikas a kokarin gwamnati na neman bankado bayanan da ake zarginsa da boyewa.
Masu gabatar da kara sun yi kokarin a gaggauta gabatar da shara'ar kasancewar mista Trump ya bayyana a gaban kotun.
Sai dai kwararrun masana shara'a sun ce mai yiwuwa ne tsohon shugaban yayi kokarin harfar da jinkiri a shara'ar da ake masa.
"Yana da dukkan dabaru na kawo jinkiri," a cewar Carl Tobias, wani farfesa a fannin shara'a dake jami'ar Richmond a Virginia, ya kara da cewa mista Trump yana yakin neman zaben shugabancin kasa a jam'iyyar Refablikan domin sake dawowa fadar White House a 2024.
A ranar Talata ne aka tsare mista Trump a Miami inda yayi zama dirshan don sauraron shara'a. An tsayar dashi da kuma yi masa gwajin kwayoyin halitta na DNA gabanin shiga kotun.
An bashi damar ficewa daga kotun ba tare da gindaya wasu sharrudan daba beli ba, kasanewar sashen kula da al'amurran tsaro ya bashi kariya.
Mataki na gaba shine neman kariyar tsaro domin wanke lauyan mista Trump, kasancewar shara'a ce da ta shafi muhimman bayanai. "Wannan zai dauki lokaci," a cewar Kevin McMunigal, tsohon babban mai gabatar da kara a kotun tarayya kuma farfesa a fannin shara'a a jami'ar Western Reserve dake Ohio.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Gabanin faruwar hakan, Mr Trump zai kimtsa tawagar lauyoyinsa a Florida.
Biyu daga cikin lauyoyin nasa, James Trusty da John Rowley, sun yi murabus daga aiki a ranar Juma'a, kwana guda bayan tabbatar da zargin da ake masa a hukumance.
Tsohon shugaban na Amurka ya samu wakilcin Todd Blanche a lokacin gudanar da shara'ar a ranar Talata, sai dai masana sun ce mai yiwuwa ne zai sake gayyato wasu lauyoyin don bashi kariya a shara'ar.
A hannu guda, kotun zata yi gaban kanta wajen zabo alkalan da zasu jagoranci shara'ar.
Farfesa McMunigal yace kotun tarayyar zata gaggauta shara'ar inda ake sa ran gudanar da shara'ar ga wadanda zasu kare kansu cikin kwanaki 90 bayan tsaresu. Sai dai shara'ar mista Trump ta sha banban, mai yiwuwa ne saboda kasancewarsa a matsayin wani babban kusa wanda za a bukaci bashi kariyar tsaro.
Tawagar kwararrun lauyoyi sun ce zarge-zargen da ake yiwa tsohon shugaban kasar sna da matukar karfi kuma duk wani yunkurin neman yiwa shara'ar kafar-ungulu ba lallai ne yayi tasiri ba.
Ga wasu hanyoyi uku da ake zaton zasu yi amfani dasu wajen shashantar da shara'ar.
1. Ikirarin rashin aikata laifi
Mista Trump ya sha nanata cewa yana da 'yancin daukar bayanan daga fadar White House karkashin kudirin dokar fadar shugaban kasa, kuma an riga an amince da cewar bayanan ba na sirri bane gabanin shugaban ya sauka daga kan karagar mulki.
Lauyoyinsa zasu yi kokarin gabatar da batun a gaban kotu, koda yake farfesa Tobias yace mai yiwuwa ne ba za a yi musu adalci a shara'ar ba.
"Ban gamsu cewa ya kamata ya nade hannu ya zura ido musu ido ba don kawai ya sauka daga shugabancin kasa," inji farfesa Tobias. "Dokar bayanan a fili take, kuma bana tsammanin akwai abun cece-kuce game da hakan."
2. Zargin rashin yi masa adalci
Lauyoyinsa za kuma su iya cewa mai yiwuwa ne Trumph ana yi masa shara'a ne saboda an rena masa kura, bisa yadda ake nuna masa rashin adalci duba da yadda wasu 'yan siyasa irinsu su Hillary Clinton, Mike Pence da shugaba Joe Biden, ba a taba tuhumarsu da laifuka game da yadda suka tafiyar da takardun ba.
Sai dai Farfesa Tobias yace shara'ar tsohon shugaban kasar ta sha banban ta hanyoyi da dama. Babu koda mutum guda cikin 'yan siyasar da aka taba nema ya dawo da wasu bayanan da yake dasu, yayin da shedu suka tabbatar da cewa mista Trump ne kadai ya fuskancin wannan tuhuma.
"Tuhume-tuhumen na cike da batutuwa marasa kan gado da ake zargin mista Trump da aikatawa," inji shi.
3. Yunkurin watsi da manyan hujjoji
Hanya ta gaba da mista Trump da tawagar lauyoyinsa zasu iya yunkurin haifar da jinkiri a shara'ar shine ta hanyar neman yin watsi da hujjojin da aka gabatar a gaban mai shara'a, musamman shaidu daga wajen lauyan Trump M Evan Corcoran.
"Wannan wani batu ne na gabanin gabatar da shara'a wanda zai iya kawo jinkiri a shara'ar," inji farfesa McMunigal.
Sai dai ya kara da cewa, alkalin dake kula d shara'ar a Washington DC ya riga ya amince cewa za a iya sanya hujjojin tuhume-tuhumen da ake yiwa tsohon shugaban kasar karkashin zargin manyan laifuka.
Kwararru sun ce koda yake ba lallai bane wadannan batutuwa su iya lalata shara'ar, sai dai zasu iya haifar da jinkiri a shara'ar, kasancewar kot zata auna dukkan batutuwan da lauyoyin mista Trump suka gabatar.











