Me ya sa ake taƙaddama tsakanin gwamnan Bauchi da Ministan harkokin wajen Najeriya?

Lokacin karatu: Minti 4

Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar ya mayar wa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed martani bisa wasu kalamai da gwamnan ya yi a kan shi.

Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan BBC ta sanya tattaunawar da ta yi da gwamnan na jihar Bauchi, inda ya kare manufofinsa tare da mayar da martani kan sukar da ministan ya yi wa gwamnatin jihar.

Ƴan siyasan biyu dukkaninsu sun fito ne daga jiha ɗaya - Bauchi - da ke arewa maso gabashin Najeriya, kuma sun daɗe suna jan zarensu a harkar siyasa.

A wata tattaunawa da ta gabata, Tuggar ya ce "jihar Bauchi ta samu kuɗi sama naira biliyan 8.8 a watan Oktoba da kuma naira biliyan 9 a watan Nuwamba, amma babu wani abu da aka gani a ƙasa a jihar".

Haka nan ministan ya soki lamirin shirin gwamnatin Bauchi na raba filayen noma, inda ya ce gwamnan na "amfani da kuɗin da jihar ke samu wajen sayen kadarori da kuma filaye daga hannun talakawa".

Lokacin da aka tambaye shi kan zargin rashin gudanar da ayyuka da kuɗaɗen da jihar ke samu, gwamna Bala Mohammed ya ɗora wani ɓangare na laifin a kan faɗuwar darajar naira idan aka kwatanta da dala.

Sannan ya ƙalubalanci ministan da cewa zai iya duba irin ayyukan da gwamnatin jihar Bauchi ke yi kasancewar ana wallafawa a ƙasidu.

Sai dai ya yi zargin cewa ministan na ƙoƙarin kare shugaban ƙasar Najeriya, Bola Tinubu ne bayan sukar da gwamnan ya yi masa a kwanakin baya.

Ya ce "Wataƙila yana yi ne domin kare shugaban ƙasa saboda mun faɗi abin da ya kamata a gyara, shi ya sa shi kuma yake suka."

A makonnin da suka gabata an ji yadda gwamnan na Bauchi ya soki shugaban Najeriya, Bola Tinubu a lokacin da ya karɓi baƙuncin wani sanannen malamin addinin Musulunci na ƙasar, wanda ake wa kallon ɗaya daga cikin magoya bayan shugaban ƙasar.

'Abin kunya ne gare mu'

Sai dai bayan martanin da ya mayar, gwamnan ya zarce da bayani, inda ya riƙa sukar lamirin yadda ministan ke tafiyar da ayyukansa.

Ya ce: "Gara ya fara gyara nasa aikin kafin ya fara ganin na wani...Yanzu idan ka duba sha'anin jakadanci a Najeriya, abin kunya ne mu ce wannan ɗanmu ne".

Ya bayar da misali da gazawar Najeriya wajen naɗa jakadu a ƙasashen ƙetare da kuma yadda gwamnatin Najeriya ta tunkari matsalar juyin mulki a wasu ƙasashen yammacin Afirka.

Martanin Tuggar

Sai dai kwana ɗaya bayan hirar da aka yi da gwamnan, Yusuf Tuggar ya mayar da martani, inda ya yi zargin gwamnan da raba filaye ga "abokansa da na kusa shi da kuma iyalansa".

Sannan ministan ya musanta zargin rashin yin abin da ya kamata a harkar diflomasiyya na Najeriya, musamman batun juyin mulki a wasu ƙasashen Afirka ta yamma.

"Na farko, shugaban ƙasa bai riga ya hau mulki ba lokacin da aka yi 'ku' (juyin mulki) a ƙasar Mali a 2021, ba na nan, shugaban ƙasa ba ya nan aka yi 'ku' a Burkina Faso, sannan a watan Juli, kwana na 26 a 2023 aka yi 'ku' a Nijar, ban zama minista ba sai watan Agusta."

"Saboda haka nan ka ce ka ɗora wannan laifi a kaina... ni ne na sa aka yi 'ku'?" in ji Tuggar.

A ranar 21 ga watan Agustan 2023 ne shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya naɗa Yusuf Tuggar a matsayin ministan harkokin waje na Najeriya.

Haka na zuwa ne bayan ya zama jakadan Najeriya a Jamus a daga shekarar 2017 zuwa 2023.

Tuggar ya zama minista ne a daidai lokacin da Najeriya ke ƙoƙarin samar da maslaha ga juyin mulkin da aka yi a wasu ƙasashen Afirka, musamman Jamhuriyar, kasancewar shugaba Bola Tinubu ne shugaban ƙungiyar haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka.

Sai dai duk da ƙoƙarin Najeriya da sauran ƙasashen yankin, ƙasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun dage kai da fata kan juyin mulkin, kuma har yanzu babu wani takamaiman lokaci da shugabannin suka bayar na lokacin da suke sa ran mayar da mulki ga farar hula.