Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saƙon da gwamnan Bauchi ya bai wa Jingir zuwa Tinubu ya ɗauki hankali
Kalaman da gwamnan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya, Sanata Bala Mohammad, ya yi wa fitaccen malamin addini Sheikh Yahaya Jingir game da mawuyacin halin da ake ciki a Najeriya na ci gaba da jan hankalin jama'a musamman a shafukan sada zumunci.
Cikin wani bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga Gwamnan Bala Mohammed,na jawabi ga Sheikh Jingir a fadar gwamnatin Bauchi lokacin da shehin malamin ya kai masa ziyarar ta'aziyar rashin matar mahaifinsa.
An jiyo gwamnan na shaida wa Sheikh Jingir cewa ya kamata ya faɗa wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu halin da ƙasar ke ciki sakamakon wasu manufofin gwamnatinsa.
''Kai ka bambanta kwarai da sauran malamai da ke goyon bayan gwamnatin Muslim-Muslim, saboda kai kowa naka ne, kuma Allah ya sa har yanzu kana da rai, kuma kana faɗa ana ji," in ji gwamnan.
''Watakila ka ji wasu maganganu tsakaninmu da Tinubu, to da gaske ba mu shiri da shi."
Gwamnan ya zargi Tinubu da ma gwamnoni da jefa 'yan Najeriya cikin mawuyacin halin matsin tattalin raziki.
A cewarsa: ''Sakamakon abubuwan da ya kawo wanda ba shi sauraron mutane, ba shi ji ba shi gani, abin kamar zai halaka mu mu al'ummar arewacin Najeriya''.
Bala Mohammed ya bayar da misali da batun ƙudirin haraji da Shugaba Tinubu ya gabatar wa majalisar dokokin ƙasar, wanda ke buƙatar aiwatar da wasu sauye-sauye kan yadda ake karɓa da kasafta harajin.
Gwamnan ya ce da kuɗin haraji ne gwamnatocin jihohi ke samun kuɗaɗen aiwatar da ayyukansu.
Gwamnan da ake yi wa laƙabi da Kauran Bauchi, na daga cikin gwamnonin arewacin ƙasar da suka fito fili ƙarara suka yi adawa da sabon ƙudirin harajin da ake son sauya wa fasali.
Bala Mohammed ya ce dama yana da niyyar zuwa har gidan Sheikh Jingir domin sanar da shi matsayarsa kan matakin na shugaban ƙasa.
''Watakila kana cikin mutaten da suke yi wa shugaban ƙasa magana kuma ya saurare su... muna so a faɗa wa shugaban ƙasa cewa ƙudurorin da yake gudanarwa ba su aiki'', a cewar gwamnan na jihar Bauchi.
Tun da farko a jawabinsa, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce jagoranci na buƙatar jajircewa.
Ya ce a lokacin da Allah ya aiko Annabi Nuhu sai da ya shekara 950 yana wa'azi amma bai samu mabiya da suka kai 100 ba. Amma duk da haka Annabin bai yi ƙasa a gwiwa ba.
''Shi ya sa ni ma nake wahala da Muslim-Muslim [gwamnatin Tinubu da Shettima], saboda kafin abin ya shiga ƙwaƙwalwar mutane da wahala," in ji malamin.
Sheikh Jingir na cikin manyan malaman Musulunci da ke goyon bayan gwamnatin Tinubu ta ''Muslim-Muslim'' - wato shugaban ƙasa da mataimakinsa duka mabiya addinin Musulunci.
An sha jin malamin na kare manufofin gwamnatin Tinubu a wuraren wa'azi a lokuta da dama, abin da ya janyo masa suka daga wasu 'yan ƙasar da ke ganin baiken gwamnatin Tinubun.
Me mutane ke cewa ?
Kalaman dai sun je hankulan 'yan ƙasar da dama, musamman masu amfani da shafukan sada zumunta.
Inda suka riƙa wallafa bidiyon da yin tsokaci game da shi.
Ga kuma wasu daga cikin abubuwan da masu amfani da shafukan ke cewa.
Comrade Abiyos Roni mai amfani da shafin X, cewa ya yi ''Gwamna Ƙaura ya yi wa Sheikh Jingir Wa'azi da nasiha''.
Haka kuma wani mai amfani da shafin X, mai suna Asad_Mukty yaba wa gwamnan na jihar Bauchi ya yi bisa kalaman nasa.
''Lallai Ƙaura jarumi ne, kuma siyasar Najeriya tana buƙatar irinsu'', in ji shi.
Shi kuwa fitaccen ɗan jaridar nan, Ja'afar Ja'afar a shafinsa na Facebook cewa ya yi ''Sheikh Jingir yana ɗaukar darasu irin na siyasa wajen Mallam mai ƁAROTA''.
Shi ma wani mai amfani da shafin Facebook, mai suna Ahmad Mu'azu Misau, ya ce gwamnan Bauchi ya sa jikin Sheikh Jingir ya yi sanyi.
Sannan ya yi fatan canzawar huɗubar malamin ta ranar Juma'a.