Southgate na iya maye gurbin Amorim, Bernardo Silva zai koma Saudiyya

Manchester United na sha'awar sayen dan wasan Juventus dan kasar Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 25, a kasuwar musayar 'yan wasa ta Janairu. (Gazetta)
Dan wasan Manchester City dan kasar Portugal, Bernardo Silva, mai shekara 31, yana tunanin komawa Saudiyya idan kwantiraginsa ya kare a bazara mai zuwa. (Talksport)
Dan wasan tsakiya na Portugal Joao Neves, mai shekara 21, shi ne babban burin Manchester City, amma ana sa ran Paris St-Germain za ta yi watsi da batun. (Football Insider)
Real Madrid na zawarcin 'yan wasan tsakiya biyu na Chelsea, Enzo Fernandez dan kasar Argentina mai shekara 24 da kuma dan kasar Ecuador Moises Caicedo mai shekaru 23. (TBR Football)
Tsohon kocin Ingila Gareth Southgate na cikin jerin mutane uku da za su iya maye gurbin kocin Manchester United Ruben Amorim idan an kore shi. (Talksport)
AC Milan ta fara tattaunawa da dan wasan bayan Ingila Fikayo Tomori, mai shekara 27, kan sabon kwantiragi, sakamakon zawarcin da kungiyoyin Premier ke masa. (Fabrizio Romano)
Leeds United tana sa ido kan dan wasan tsakiya dan kasar Brazil mai shekara 20 Gustavo Prado, yayin da bayanai ke cewa a shirye Internacional take ta biya kusan fan miliyan 17 kan dan wasan (SportWitness)







