Real Madrid na son Ibrahima Konate, Man City za ta nemi John Stones

Ibrahima Konate

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ibrahima Konate
Lokacin karatu: Minti 2

Real Madrid na sa ido kan halin da kwantaragin dan wasan bayan Liverpool da Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 26 ke ciki, da nufin dauko shi a bazara a kyauta idan zamansa a Madird din ya kare. (ESPN)

Dan wasan bayan Ingila John Stones, mai shekara 31, na shirin tattaunawa da Manchester City don tsawaita kwantiraginsa da zai kare a bazara. (Mirror)

Aston Villa na tunanin neman dan wasan Sunderland dan kasar Faransa Wilson Isidor mai shekaru 25 a watan Janairu. (Football Insider)

Crystal Palace na sa ran Liverpool za ta dawo da tayin dan wasan bayan Ingila Marc Guehi, mai shekara 25, a watan Janairu, bayan da dan wasan bayan Italiya Giovanni Leoni, mai shekara 18, ya yi jinyar shekara guda. (TBR Football)

Liverpool kuma tana zawarcin dan wasan bayan Uruguay da Barcelona Ronald Araujo, mai shekara 26, a matsayin mai tsaron baya. (Cought Offside)

Chelsea na duba zabin mai tsaron ragarta yayin da suke shirin sayar da dan wasan kasar Sipaniya Robert Sanchez, mai shekara 27, a karshen kakar wasa ta bana. (Fichajes)

Dan wasan tsakiya na Ingila Morgan Rogers, mai shekara 23, ya fara tattaunawa da Aston Villa kan sabunta kwantaraginsa, yayin da kungiyoyi da dama na Premier ke nemansa. (Football Insider)

Nottingham Forest ta sanar da Manchester United, da Tottenham, da Newcastle da Liverpool cewa dan wasan tsakiyarta na Ingila Elliot Anderson mai shekara 22 ba na sayarwa bane. (TBR Football)