Arsenal, Man United da City na rububin Konate, Bayern na iya tsawaita zaman Jackson

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool na fatan sayen dan wasan Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 26, lokacin da kwantiraginsa zai kare a bazara, sai dai itama Real Madrid na sha'awar sayen dan wasan bayan na Bayern Munich. (Bild)
Tottenham na son rike dan wasan bayan Portugal Joao Palhinha, mai shekara 30, a matsayin dindindin bayan nasarar da ya samu a zaman aro daga Bayern Munich. (Talksport)
Manchester United ta amince da yarjejeniya da Fortaleza don siyan dan wasan tsakiyar Colombia Cristian Orozco mai shekaru 17 da zarar ya cika shekara 18 a watan Yuli. (Athletic)
Har ila yau United na neman kammala cinikin golan Derby na Ingila mai shekaru 16, Charlie Hardy. (Sun)
Bayern Munich na shirin bayar da kwantiragi na dogon lokaci ga dan wasan gaban Senegal Nicolas Jackson, mai shekara 24, wanda a halin yanzu yake zaman aro daga Chelsea. (Bild)
An bayyana dan wasan tsakiya na Barcelona da Netherlands Frenkie de Jong, mai shekara 28, a matsayin wanda Manchester United ke nema. (Football Insider)
Liverpool na fatan kulla yarjejeniya da dan wasan bayan Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 26, a yayin da Arsenal, da Chelsea da Manchester City ke zawarcinsa. (TBR Football)
Arsenal na fatan kulla yarjejeniya biyu da Real Sociedad kan kudi Yuro miliyan 75 (£65.6m) kan dan wasan Japan Takefusa Kubo, mai shekara 24, da kuma dan wasan bayan Faransa Lucien Agoume mai shekaru 23. (Fichajes)
Newcastle na cikin kungiyoyin da ke sa ido kan halin da dan wasan tsakiyar Faransa Eduardo Camavinga, mai shekara 22 ke cikin,yayin da yake tunanin barin Real Madrid. (Football Insider)











