Liverpool da United za su fafata kan Branthwaite, Mourinho na zawarcin Benzema

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool da Manchester United za su fafata wajen siyan dan wasan bayan Everton Jarrad Branthwaite, mai shekara 23 (Mirror)
Manchester United na shirin zawarcin dan wasan Atletico Madrid dan kasar Ingila Conor Gallagher mai shekaru 25 a duniya. (Express)
Atletico Madrid na zawarcin dan wasan gaban Marseille dan kasar Ingila Mason Greenwood, mai shekara 23, wanda kungiyar ta Faransa ta yi wa farashi a kan fan miliyan 65. (Fichajes)
AC Milan na zawarcin dan wasan bayan Liverpool dan kasar Ingila Joe Gomez mai shekaru 28, kuma suna tunanin daukarsa a watan Janairu. (Calciomercato)
Chelsea na fatan doke Real Madrid wajen siyan dan wasan Como dan kasar Argentina Nico Paz mai shekaru 21. (Cought Offside)
Liverpool na zawarcin dan wasan baya na Bayern Munich dan kasar Faransa Dayot Upamecano mai shekaru 26 a duniya a karshen kakar wasa mai zuwa. (Kirista Falk)
Kocin Benfica Jose Mourinho yana sha'awar sayen dan wasan Al-Ittihad, mai shekara 37, kuma tsohon dan wasan Faransa Karim Benzema. (Marca)
Tottenham za ta iya kiran dan wasan Ingila Mikey Moore mai shekaru 18 daga aron da yaje Rangers a watan Janairu. (Football Insider)
Chelsea na shirin dauko dan wasan Juventus dan kasar Italiya Manuel Locatelli, mai shekara 27, amma tana fuskantar hamayya daga Newcastle, da Aston Villa, da West Ham da Bayer Leverkusen. (Cought Offside)
Manchester United na duba yiwuwar daukar Graham Potter bayan sallamarsa da West Ham ta yi, don maye gurbin Ruben Amorim. (Fichajes)
Sunderland za ta yi tunanin sayar da dan wasan bayan Ingila Dennis Cirkin mai shekaru 23 a watan Janairu. Kwantiraginsa zai kare ne a bazara mai zuwa. (TBR Football)










